Ran wani ɗan Nijeriya ya ɓaci bayan ya sayi sakwara da miyar agusi na dala 140 a Amurka

Ran wani ɗan Nijeriya ya ɓaci bayan ya sayi sakwara da miyar agusi na dala 140 a Amurka

Wani ɗan Nijeriya da ke zaune a Amurka ya nuna matuƙar ɓacin rai bayan da ya biya Dalar Amurka $140 ya sayi faranti biyu na miyar egusi da sakwara

Wannan al’amari, wanda aka dauka a wani bidiyo da Oyindamola ya wallafa a shafin X a jiya Talata, ya jawo hankalin jama’a kan yadda wasu gidajen abincin Afirka ke zabga tsada ga ’yan kasashen Afirka , musamman ’yan Najeriya.

A cikin bidiyon, mutumin ya bayyana fushinsa, yana korafin cewa masu sayar da abincin Afirka suna ƙara farashi da gangan, musamman ga kwastomomi ƴan Najeriya ne.

Ya bayyana cewa  da ya je wani gidan abincin Afirka, an ce ya biya $140 kan faranti biyu na miyar egusi da sakwara. 

A cewar sa, lokacin da ya nemi bayani kan yadda farashin ya yi tsada hala, sai aka shaida masa cewa farashin kowanne faranti dala $40 ne, sauran kudin kuma haraji ne.