Gwamna Buni Ya Gina Cibiyoyin Kiwon Lafiya Matakin Farko 138 A Yobe

Gwamna Buni Ya Gina Cibiyoyin Kiwon Lafiya Matakin Farko 138 A Yobe

 

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

 

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, a ranar Talata ya kaddamar da sabbin cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko (PHCs) guda 138 waxanda gwamnatin jihar ta sake gyarawa a qananan hukumomi 17 a jihar.

 
A bikin buxe sabbin cibiyoyin, wanda ya gudana a Cibiyar kula da lafiya a matakin farko na unguwar Gwange da ke Damaturu, Gwamna Buni ya ce sake farfaxo da cibiyoyin kiwon lafiyar a matakin farko ya zama dole sakamakon yadda mayaqan Boko Haram suka lalata, al'amarin da ya haxa da gine-ginen jama'a, makarantu, turaku da cibiyoyin wutar lantarki, da makamantan su waxanda yan ta'addan suka varnata a jihar.
 
Gwamnan ya qara da cewa, gwamnatin sa ta quduri aniyar kawo sauyi mai ma'ana a fannin kiwon lafiya domin inganta sha'anin kiwon lafiya a faxin jihar.
 
A hannu guda kuma, Buni ya sanar da mahalarta taron cewa gwamnatinsa ta yi nasarar kammala gine-gine da gyara cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 138 a cikin cibiyoyi 178 waxanda ya xauki alqawarin samarwa a faxin jihar Yobe.
 
Da yake buxe cibiyoyin, Gwamna Buni ya ce, “Wanda domin hakan ne, mun zo nan a yau (Talata) don kaddamar da cibiyar kula da lafiya a matakin farko a unguwar Gwange.” in ji shi.
 
Gwamnan ya qara da cewa, ko shakka babu cibiyoyin za su taimaka wajen inganta harkokin kiwon lafiyar al'ummar jihar Yobe, musamman mata da qananan yara, tare da bunqasa ayyukan jinya.
 
Ya ce, "Akwai cibiyoyin kiwon lafiya guda 8 waxanda muka inganta su tare da xaga darajarsu zuwa manyan asibitoci, a garuruwan Bara, Buni- Gari, Babbangida, Yunusari, Yusufari, Jaji-Maji, Machina, da Asibitin Malam Baba da ke garin Nguru."
 
Har wala yau kuma, Gwamna Buni ya ce gwamnatinsa ta xaga darajar manyan asibitoci huxu zuwa Asibitocin qwararru a garuruwan Buni- Yadi, Gashua, Geidam, da Potiskum domin inganta harkokin kiwon lafiya zuwa matakin gaba a jihar.
 
Yayin da ya qara da cewa, "Ya na da mahimmanci a lura cewa xaya daga cikin manyan manufofin gwamnatinmu shi ne inganta harkokin kiwon lafiya don rage yawan mace-mace tare da daqile cututtuka masu yaxuwa, da kuma cimma muradun qarni wanda qasashen duniya suka sanya a gaba, wanda ya qunshi samar da ingantaciyar lafiya ga al'umma."
 
Gwamnan ya qara da cewa, gwamnatinsa za ta ci gaba da jajircewa wajen yunqurin cimma nasarar da qasashen duniya suka qudurta a fannin bunqasa kiwon lafiya (UHC) haxi da sauran manufofin ci gaban qarni mai xorewa. 
 
A gefe guda kuma, Gwamna Buni ya kaddamar da sabbin motocin xaukar majinyata (masu taya uku) 88 domin xaukar mata masu juna- biyu a faxin jihar.
 
Ya ce “Gwamnatinsa ta qaddamar da motocin domin yankunan karkara wanda hakan zai rage jinkirin kai wa ga cibiyoyi da asibitoci don ceton rai, wanda hakan yasa gwamnatin ta sayo tare da rarraba waxannan motocin xaukar majinyata 88 don su rinqa jigilar mata masu haihuwa da sauran maras lafiya."
 
A jawabin, Kwamishinan Kiwon Lafiya na jihar Yobe, Dokta Muhammad Lawan Gana, ya ce ayyukan gine-ginen da gyare-gyaren cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ko shakka babu zai zaburar da inganta aikin ma’aikatan lafiya da samun damar yin ayyukan qwararru a kowane lokaci.
 
A jawabin maraba wanda Sakataren Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko na jihar Yobe, Dakta Babagana Kundi Machina, ya ce waxannan ayyuka suna daga cikin muhimman alqawuran da Gwamna Mai Mala Buni ya xauka tun bayan rantsar dashi a matsayin Gwamna; na qarfafa hukumar kula da lafiya a matakin farko da kuma tabbatar da samar da aqalla cibiya xaya a kowace gunduma (PHCC) a gundumomi 178 a faxin jihar Yobe.
 
Machina ya ce wannan nasara abin a yaba ce, ya kara da cewa bisa ga wannan qudurin, gwamnati ta na samun goyon baya da haxin gwiwar qungiyoyi daban-daban kamar su Multi Sectoral Crises Recovery Projects (MCRP), United Nations Development Programme (UNDP), Plan International, NNPC/Cheron/Shell Petroleum a fannin inganta kiwon lafiya.