INEC  Ta Tsaida Ranar Rabawa Zababbun Gwamnoni Satifiket

INEC  Ta Tsaida Ranar Rabawa Zababbun Gwamnoni Satifiket

 

Hukumar INEC mai gudanar da zabe a Najeriya ta ce za ta raba takardun shaidar nasara ga duka wadanda suka lashe zaben Gwamnoni.

 A wata sanarwa da ta fitar a daren Lahadi, INEC ta ce za a mika satifiket ga zababbun gwamnoni da wadanda suka lashe zaben majalisar dokoki. 
Za a fara wannan aiki ne daga ranar 29 ga watan Maris har zuwa ranar 31 ga watan mai ci a 2023. 
Legit.ng Hausa ta fahimci wannan bayani ya fito ne a sanarwar da Festus Okoye ya fitar a matsayinsa na Kwamishinan yada labarai na INEC. 
The Cable ta rahoto Festus Okoye yana cewa za a raba satifiket din ga wadanda suka yi nasara ne a ofisohin hukumar INEC da ake da su a Jihohi. 
Sashe na 72 (1) ya wajabtawa hukumar kasar bada takardar shaida ga ‘yan takaran da suka yi nasara, za ayi hakan ne kafin a zarce kwanaki 14.
A dalilin haka, Okoye ya ce daga ranar Laraba zuwa Juma’a mai zuwa, zababbun Gwamnoni da ‘yan majalisun jiha za su karbi takardar nasararsu. 
Zuwa lokacin za a sanar da masu jiran gadon game da lokacin da za su karbi satifiket dinsu, bayani zai fito ne daga bakin Kwamishinonin zaben jihohi. 
Baya ga gwamnoni da ‘yan majalisun da za su shiga ofis nan da karshen Mayu, za a bada satifiket ga wadanda za su zama mataimakan Gwamnoni.