Direba Ya Rasa Ransa A Cikin Tankar Man Fetur A Kano
Direban babbar mota Dahiru Aliyu Hotoro mai shekara 45 ya rasa ransa a cikn tankar Man fetur kamar yadda hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar.
Kakakin hukumar, Saminu Abdullahi, shi ne ya fitar da sanarwar faruwar lamarin a ranar Talata, amma lamarin ya faru ne a ranar litinin data gabata kamar yadda Aminiya ta ruwaito.
Hukumar ta ce ta samu kiran waya ne ta hannun wani Shu'aibu Muhammad da safiyar ranar, a take suka tafi in da abin ya faru da misalin karfe 10:59 suka tarar direnan ya bar duniya.
Ya kara da cewa, Aliyu ya shiga cikin tankin motar ne domin wanke man da ke ciki, amma aka yi rashin sa’a ya makale a ciki har ya mutu ya kasa fita sai bayan rasuwarsa aka fahimci yana ciki bai fito ba.
managarciya