Sanata Wamakko ya samar da gurabun karatun digiri na biyu ga 'yan asalin Sakkwato 25 

Sanata Wamakko ya samar da gurabun karatun digiri na biyu ga 'yan asalin Sakkwato 25 
Sanata Wamakko ya samar da gurabun karatun digiri na biyu ga 'yan asalin Sakkwato 25 
Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya samar da gurbin karatu ga 'yan asalin jihar Sakkwato su 25 a ƙudirinsa na ganin ilmin jiha ya bunkasa a fannoni daban-daban ya sanya ya  tura mutanen don su yi karatun digiri na biyu dana uku a Makarantar tsaro dake Kaduna.
A lokacin da yake miƙa takardar amincewa ta soma karatu ga waɗanda suka samu gurabun  Sanata Wamakko ya ce an yi haka ne bisa ga cancanta.
Shugaban kwamitin zaɓo ɗalibban Farfesa Musa Garba Maitafsir wanda shi ne ya waƙilci Sanata Wamakko ya ce kafin a zaɓo ɗalibban sai da aka yi masu tantancewa ta ga da ga domin tabbatar da ƙwarewarsu ga abin da za su je su karanta.
Maitafsir ya ce mutane 80 ne suka nuna sha'awar a samo masu gurbin karatun da za a ɗauki nauyin karatun amma 25 ne suka yi nasara a tantancewar da aka yi. 
Ya yi kira ga ɗalibban su yi amfani da damar da suka samu wadda Sanata ya samar musu don haka su tabbatar kwalliya ta biya kuɗin sabulu.
Ya ƙara da cewar Sanata Wamakko soyayyarsa da ilmi ce ta sanya a koyaushe yake shirye ya kashe ko nawa ga harkar ilmi musamman a fannin kimiya da ƙere-ƙere.
Ya ƙalubalanci ɗalibban su mayar da hankali ga karatunsu a lokacin da suke makaranta.
Daraktan mulki a ofis ɗin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, Alhaji Almustapha Abubakar Alƙali ya ce Sanata Wamakko ya biya kuɗin makaranta da wurin kwanansu,  kawai abin da yake buƙata su mayar da hankali ga karatunsu.
Ya ce ɗalibban za su kwashe shekara biyu zuwa  uku a makarantar kafin su gama karatunsu, an kuma tura su ne su karanci fannonin domin Sakkwato nada buƙatar cike giɓin da take da shi a haujin.
Alƙali ya ce ɗalibban za su tafi Kaduna a wannan sati domin za a soma karatu a wani sati.