Wahalar Man Fetur ta kunno kai a Nijeriya a lokacin da kungiyar 'yan kasuwa masu sayar da fetur ta kasa suka koka kan karin da masu rumbun ajiye fetur suka yi masu.
Mataimakin shugaban kungiyar Alhaji Abubakar Maigandi ya ce an yi masu kusan karin naira 9 ga kowace lita.
Maigandi ya ce masu rumbun mai da ake kira deport sun yi kari daga naira 148 zuwa 157 ga kowace litar mai hakan ya sanya 'yan kungiyarsu jikinsu ya mutu ga sayo man a wurin masu rumbu.
Kungiyar IPMAN ba ta son karin kudin mai tun sanda aka kara masu man suna saye kan 153 zuwa 155.
A jihar Sakkwato man fetur ya fara wuya domin a mafi yawan gidajen da suka bude suna sayar da man za ka samu dogon layi na abubuwan hawa.
Gidan Man A.A Rano a jihar shi ne mafi girma in har akwai mai a gidajensa za ka samu wuyar man tana da sauki amma in har ba a zuba mai a gidajensa ba za ka samu abin ya kara ta'azara.
A tun ranar Assabar data gabata ne aka fara samun wuyar man a jihar ta Sakkwato, abin yana kara ta'azara a kullum.
Har yanzu gwamnatin Nijeriya ba ta yi magana kan wuyar man da aka soma ba a kwanannan.