Mun gaji ruɓaɓɓen babban layin wutar lantarki kuma dole ya riƙa yawan sauka - Gwamnatin Taraiya
Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce babban layin wutar lantarki na kasa zai ci gaba da sauka saboda "tsoho ne kuma ruɓaɓɓe ne".
Jaridar PUNCH ta ruwaito Adelabu ya bayyana haka ne a yayin wani zaman kare kasafin kudi da kwamitin majalisar dattawa akan wutar lantarki a jiya Litinin.
Ministan ya ce gwamnati na shan wahalar gyaran layin da ta gada daga gwamnatin da ta gabata, inda ya bayyana cewa babban layin ya sauka sau takwas a shekarar 2024 ba 12 ba kamar yadda ake yaɗawa.
“Mun yi kokari sosai don ganin mun gyara layin daga yadda mu ka gaje shi.
“Abin takaici, har yanzu ya tsufa sosai. Ya lalace. Kuma muna ta ƙoƙarin yadda za a shawo kan lamarin na dindindin,x in ji shi.
managarciya