'Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Tagwayen Jarirai Kwana 4 da Haihuwarsu Tare da mutum 20 a Zamfara 

'Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Tagwayen Jarirai Kwana 4 da Haihuwarsu Tare da mutum 20 a Zamfara 

'Yan awowi kadan da suka wuce kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara Ibrahim Magaji Dosara ya sanar da cewa harkokin tsaro a jihar sun inganta, ana haka sai ga shi 'yan bindiga sun yi garkuwa da wasu tagwayen jarirai kwana hudu da haihuwarsu tare mutane akalla 20 a kauyen Dauran cikin karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara ranar Lahadi data gabata.

 Malam Haruna Dauran da yake a kauyen ya sanar da wakilinmu a waya cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 'yan bindigar sun shiga kauyensu ne da misalin karfe takwas da rabi na safe suka rika shiga gida-gida suna bincike har suka samu adadin mutanen da suke so suka tafi da su.
Malam Haruna ya ce maharan sun yi kokarin shiga masallaci amma wadan da ke ciki suka tsere kafin zuwansu. 
"maganar da nake yi da kai kashi 90 na wadanda suka tafi da su matan aure ne tare da tagwayen jarirai da aka yi kwana hudu da haihuwa da mahaifiyarsu da ke shayarwa. Haka ma sun kai hari a wani kauye da ake kira Baicin Dauran.
"a lokacin da suka shiga kauyen sun samu mutanen na kokarin tafiya makabarta wurin bizne wani dan uwa da 'yan bindiga suka kashe a haka suka tare mutanen suka caje dukan wadan da ke wurin suka tafi da duk abin suka samu na waya da kudi ba wanda zai gaya maka adadin abin suka sace daga mutanen," a cewarsa.
 
 
 Malam ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su kawo dauki su kuma dakatar da siyasantar da yanayin tsaro a jiha. 
"abin da ya sanya nace gwamnati na siyasantar da lamarin tsaro duba ka gani jiya(assabar) kwamishinan yada labarai ya ce harkar tsaro a Zamfara ta inganta bayan muna ta fama da hare-hare."
A lokacin da wakilinmu ya tuntubi jami'in hulda da jama'a na 'yan sanda SP Muhammad Shehu ya ce yana bukatar minti 30 zai sake kira a waya, har lokacin hada rahoton bai kira ba.