Za a Ƙarfafa Guiwar Matasa A Ɓangaren Noma Da Sana'a a jihar Neja

Shugaban na jiha ya cigaba da cewar kungiyarsu a matakin jiha za ta tabbatar dukkanin yankunan kananan hukumomi sun samu shugabanci dan rage nauyi ga uwar kungiya ta jiha.

Za a Ƙarfafa Guiwar Matasa A Ɓangaren Noma Da Sana'a a jihar Neja
Za a Ƙarfafa Guiwar Matasa A Ɓangaren Noma Da Sana'a a jihar Neja
Za a Ƙarfafa Guiwar Matasa A Ɓangaren Noma Da Sana'a a jihar Neja
Daga Babangida Bisallah
Karamar hukumar Bosso dake jihar Naija, ta sha alwashin karfafa guiwar matasa a bangaren noma da sana'a. Sakararen karamar hukumar, Hon. Garba Jeoji ne ya bayyana hakan a lokacin rantsar da sabbin shugabannin kungiyar Gbegnu Bokun Yakwu reshen karamar hukumar a sakatariyar karamar hukumar da ke Maikunkele.
Jeoji yace kafa kungiyar yazo daidai da lokacin da ya dace, domin shugaban karamar hukumar mu,.Hon. Abubakar Gwamna ya zo da kudurce kudurcen da zasu taimakawa matasa musamman bangaren sana'a da noma dan kawar da rashin aikin yi ga matasa, Gbegnu Bokun sun zo da kudurce kudurcen da suka dace da na gwamnati, l ganin yadda matsalar tsaro ya zama ruwan dare a wannan lokacin, fatar mu hadin kan al'umma, samar da ayyuka ga matasa ta hanyar rungumar noma da sana'a ka-in da na'in wanda hakan zai taimaka wajen karya lagon bata gari masu anfani da matasa wajen tada zaune tsaye.
Kamar yadda maigirma shugaban karamar hukuma, Hon. Abubakar Gwamna ya bukaci in fada ma wannan taron, cewar gwamnatinsa a shirye take wajen hada hannu da duk masu son cigaban karamar hukumar Bosso. Za mu yi aiki tare da ku dan ganin kun cin ma muradun ku na samar da  kai da kuma baki mazauna karamar hukumar mu, da karfafa guiwar ku wajen yaki da bata gari, tare da karfafa guiwar ku wajen wayar da kan matasa muhimmancin dogaro da kai ta hanyar sana'a da noma da tarihi ya tabbatar da mu kabilar gwarawa akan sa.
Da yake jawabi ga sabbin shugabannin, Alhaji Bako Bawa Bosso, shugaban kungiyar ta jiha, ya jawo hankalin rantsattsun shugabannin da su dora a inda suka karba musamman samar da hadin kai tsakanin 'yan asalin Bosso da baki mazauna, musamman su tabbatar sun hada kai da gwamnati da sarakunan gargajiya wajen sanya ido akan bakin da ke shigowa dan samun malaba, wadanda dole a tantance su kar a baiwa baragurbi mafakar da zasu cutar da al'umma.
Shugaban na jiha ya cigaba da cewar kungiyarsu a matakin jiha za ta tabbatar dukkanin yankunan kananan hukumomi sun samu shugabanci dan rage nauyi ga uwar kungiya ta jiha.
Alhaji Ahmed Auta Maikunkele, shi ne zababben shugaban kungiyar na karamar hukumar Bosso, yace babban burin shi idan ya fara aiki, shi ne yadda zasu bullo da dubarun wayar da kan kabilar Gbagyi musamman a karamar hukumar Bosso, ta yadda za a samu zaman lafiya, da wayar da kan su illar kai kara ofishin 'yan sanda, muna da shugabanni ya kamata komi ya taso mu zauna da shugabannin mu da sarakunan mu wajen walwale shi, shi zai takaita yawaitan shari'o'i a kotuna, haka na ji karamar hukuma ta tabo inda ke min kaikayi na rashin aiki ga matasa, shirin karamar hukuma na tallafawa matasa na aikin hannu, muna maraba da shi kuma a shirye mu ke wajen bada goyon baya.
Muna kira da babban murya ga 'yan asalin karamar hukumar Bosso masu hannu da shuni da yan bokon mu da su dawo dan mu hada kai dan ciyar da karamar hukumar nan gaba. Wannan tafiyar ta kowa da kowa ce kuma muna da tattalin arzikin kasar da kowa zai anfana idan mun tattala shi kuma mun sarrafa shi yadda ya dace.
Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki yan kabilar gbagyi 'yan asalin karamar hukumar, wanda Hon. Garba Jeoji sakataren karamar hukumar ya wakilci shugaban qaramar hukumar, Hon. Abubakar Gwamna, da shugabancin kungiyar ta jiha bisa jagorancin Bako Bawa Bosso.