Sakataren jam'iyar APC a Sakkwato Alhaji Aminu Ganda ya ce ministan shari'a na Nijeriya Abubakar Malami kalamansa kan shugabancin APC a Sakkwato yana kan hanya ba in da ya ci karo da doka gaskiya ce ya bayyana wadda wasu mutanen basa so.
Aminu Ganda ɓangaren Shugaba Mainasara Abubakar Sani yake ya yi martani ga masu ganin cewa babban lauyan gwamnatin tarayya ya saba doka domin ya shiga gaban kotu kan maganar wane ne shugaban APC a Sakkwato kotu bata yi matsaya ba.
"Maganar Malami saman hanya take bisa doka, domin kotun tarayya ta yi hukunci cewa mu ne halastattun shugabannin jam'iyyar APC, wadanda ba su gamsu da hakan ba ne suka daukaka kara a kotu ta gaba, kan hukuncin baya Mainasara ne Shugaba har sai in wata kotu ta warware hukunci farko, a gefen doka ba wanda ta sani shugaban APC a Sakkwato sai mu," a cewar Ganda.
Ya kalubalnci Isah Sadik Achida ya bayyana takardun shedar da uwar jam'iya ta ba su na amincewa da dukkan zaben da suka gabatar, kamar yadda ya yi ikirarin suna hannusa.
Ganda ya ce kalmomin Malami ya yi murabus ko a cire shi kuma APC ta kore shi ba su dace ba, saboda kawai ya bayyana abin da suke son a rufe shi ga Sakkwatawa don suna raya su ne shugabanni duk da sun san doka bata san da su ba, "Malami ba zai yi murabus ba kuma ba za a cire shi ba da ikon Allah tun da yake kamanta gaskiya da adalci"
"Da abin da Malami ya fadi uwar jam'iya ta san ba daidai ba ne da ta ja hankalinsa ko barranta kanta da shi, amma ba a yi haka ba,"a cewarsa.