Majalisar kula da harhaɗa Magunguna ta Nigeriya ta yi wa 'yan magani bita a Kano
Daga Ibrahim Hamisu, Kano.
Majalisar masu kula da harkokin harhada magunguna ta Nigeriya wato Pharmacists Council of Nigeriya da Ma'aikatar lafiya ta jihar Kano da hadin gwiwa da Kanawa Phamarcetiucal Pertners LTD, ta shirya taron karawa juna sani na kwana biyu ga masu saye da sayar da magani na jihar Kano, da ya gudana a dakin taro na NITEL, Kano.
Daya daga cikin ƴan kwamitin kasuwar dindin ta ƴan DanGwauro kuma uba a cikin kungiyar Dahiru Abdullahi Matazu ya ce bayyana cewa "Gwamnatin tarayya ta gayyato mana kwararru ne domin a karawa juna sani ta sanar da mutanen mu yadda wannan kasuwa ta Dan Gwauro za ta kasance, domin ganin an kawar da gurbattu magunguna da masu sa maye ta yadda za a kawo magani ingantace, domin marasa lafiya su sami magani ingantace"
Dahiru Matazu ya ƙara da cewa "yanzu haka an gina shaguna 679 kowane shago guda daya yana da fadin murabba'in faɗin 36 idan ka raba shi gida shida zai baka kusan rumfar Janbulo"
Sannan ya tabbatar da cewa nan bada jimawa gwamnatin Kano za ta buɗe mana wannan kasuwa ta Dangwauro ta yadda za mu ta shi daga sabon Gari mu koma can,
Kasuwar dai za ta gudana ne a karkashin kulawar Kanawa Phamarceteucal Pertners LTD bi sa kulawar Kasuwar CWC
Shi ma da ya ke na sa jawabin Manajan Daraktan Jaiz Bank Alhaji Hassan Usman ya bayyana cewa, bankin Jaiz ya shigo harkar masu saye da sayarda magani ne saboda sabon tsari da gwamnatin tarayya ta zo da shi a wannan kasuwa ta DanGwauro,
Don haka haka ya ce "Bankin Jaiz a shirye ta ke ta baiwa ƴan wannan ƙungiya kudi ko mallaka masu shaguna a wannan kasuwa, ta yadda mutum zai riƙa biya a hankali a hankali, daidaiku su ka zo ko a dunkule"
Taron dai ya samu halartar kwararru masu bita daga gwamnatin tarayya da kuma shugabannin da dimbin membobin ƴan magani na jihar Kano.
managarciya