Tambuwal Ya Yi Alkawalin Fara Baiwa 'Yan Banga Alawus Na 20,000 Daga Watan Disamba

Tambuwal Ya Yi Alkawalin Fara Baiwa 'Yan Banga Alawus Na 20,000 Daga Watan Disamba

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya sanar da fara baiwa 'yan banga waton mambobin kungiyar sintiri ta jiha alawus na dubu 20 a kowane wata, biyan  zai soma daga watan Disamba domin karfafa su.

Tambuwal ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis lokacin da ya kai gaisuwar ta'aziyar mutane 23 da 'yan bindiga suka kone a Sabon Birni cikin motar da ta dauko mutum 32 a ranar litinin data gabata a wurin ne ya ba da sanarwa tallafinsa na kashin kansa dukkan iyalan mamatan zai ba su naira dubu 250, sannan gwamnati za ta biya kudin maganin wadanda ke kwance a asibiti saboda harin.

 

"Muna iyakar kokarinmu wurin tallafawa jami'an tsaro dake jihar nan, mun bayar da ababen hawa sama da 500, mun bayar da horo ga 'yan banga kusan 1000,"  
Tambuwal a bayaninsa ya ce mashin 500 da suka tallafawa 'yan banga  domin su iya gudanar da aiyukkansu ne a karkashin kulawar jami'an tsaron kasa.