Mahara sun  sace ɗalibai 15 da kashe mutum 4 a Kwalejin Noma ta Bakura

Mahara sun  sace ɗalibai 15 da kashe mutum 4 a Kwalejin Noma ta Bakura

Mahara sun  sace ɗalibai 15 da kashe mutum 4 a Kwalejin Noma ta Bakura

Mahara dauke da mugan makamai  sun sace ɗalibai da malamai a Kwalejin Noma da lafiyar dabbobi dake garin Bakura a jihar Zamfara.

 

Mataimakin rijistara na kwalejin Malam Aliyu Bakura, ya tabbatar wa da BBC wannan labara na farmakin ‘yan bindigar da suka kawo.

Aliyu y ace maharani sun yi kashe mutum 4  ɗan sanda ɗaya da masu gadi uku don kawai zalunci.

 

Ya ce "a jiya Lahadi da daddare wajen ƙarfe 10 suka shiga suka yi ta harbe-harbe suka kwashe ɗalibai 15 da kuma wani malami da matarsa da ‘ya’yansa biyu," a cewarsa.

Malam Aliyu ya ce maharan suna da matuƙar yawa kuma sun haura katanga ne sannan sun fi awa biyu a cikin makarantar suna harbe-harbe.

A bayanin da aka samu kafin shiga Bakurar sun yi ta’adi a Maradun mahara suna cin karesu ba babbaka a gefen na Zamfara abin da ke kara tayar da hankalin mutane a yankin Arewa.