Idan Na Zama Shugaban Kasa Zan Cire Hannuna A Kan Sha’anin Matatun Mai, Zan Bar Farashin Komai A Hannun ‘Yan Kasuwa---Atiku

Idan Na Zama Shugaban Kasa Zan Cire Hannuna A Kan Sha’anin Matatun Mai, Zan Bar Farashin Komai A Hannun ‘Yan Kasuwa---Atiku

...Zan bar ‘yan kasuwa su dinga kula da jiragen kasa da kamfanin wutar lantarki ~ a cewar Atiku Abubakar

Daga Comr Abba Sani Pantami

Atiku Abubakar wanda shi ne zai yi wa jam’iyyar PDP takarar shugaban kasa a 2023 zai karfafa ‘yan kasuwa, ya ragewa gwamnati karfi.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Lahadi, 12 ga watan Yuni 2022 cewa Atiku Abubakar ya fitar da jerin manufofinsa na saida kadarorin gwamnati.

Idan ‘dan takarar ya yi nasarar zama shugaban Najeriya, ya ci burin saida matatun danyen man kasar nan a kasuwa domin a bunkasa harkar mai.

Haka zalika mulkin Atiku Abubakar zai kawo karshen mallakar TCN da gwamnatin tarayya ta ke yi, zai saida kamfanin lantarkin ne ga ‘yan kasuwa.

Rahoton yace ‘dan siyasar zai saida jiragen kasan Najeriya da wasu abubuwan more rayuwa ga ‘yan kasuwa domin gwamnati ta daina tafka asara.

Da yake dogon bayani a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, ‘dan takarar yace manufofin tattalin arzikinsa za su taimaka wajen bunkasa kasuwanci.