Illolin da tufafi matsattsu ke haifarwa ga jikin mata

Illolin da tufafi matsattsu ke haifarwa ga jikin mata

ILLOLIN  DA SUTURA MATSATTSA KE HAIFARWA GA JIKIN  MACE

 

Nafisa  Kabiru  Muhammad   

 

Yanayin Sanya suturar matan Hausawa na da bambanci da yanda mazan  ke sanya sutura.

Bincike ya nuna a zamanin da, mata sukan sanya sutura ne daidai da al’adunsu inda sukan sanya riga da zane da kuma mayafin zane domin suturta jiki, wanda hakan ke sanya duk inda matar Bahaushe ta shiga ba ta boyuwa kuma za’a iya ganeta sabanin tun asali da malam Bahaushe ke sanya warki da ganye kafin zuwan addinin musulunci.

Sai dai zamani abokin tafiya a halin yanzu yazo da irin nashi tsari na sanya sutura wanda a wannan zamani matan Hausawa kan sanya riga da fatari wato siket ko riga da zane mai yanka yanka ko kwaryaye wanda aka fi sani da pieces haka kuma zamani yazo da yadda ake dinka dogayen riguna daban-daban kamar play ko pieces da kuma fitted gown, wanda duk wadannan ba  ‘yan mata kadai ke sanyasu ba har ma da matan aure.

Ga kadan daga cikin amfanin sanya sutura, sutura tana kariya daga wasu cututtuka da kan iya shiga kai tsaye a fatar mutum, sutura na fitowa da kimar mace da kuma bambanta ta da jinsin namiji, sutura na kara fitowa da kyawun mace na asali sutura na karawa mace martaba da kima har kaga ana girmama ta.

 Ta bangaren masu dinki kuwa sun bayyana irin alfanun da suke samu sosai ga dinkunan mata, da yadda yake saurin kawo musu riba wanda ba wai ga maza masu dinki kadai ba, har da mata wadanda suka iya dinkin zamani kuma suke yinsa yadda ya kamata.

Sai dai kuma mun samu wasu rade radin cewa sanya matsattsun kaya da ‘yan matan yanzu  ke yi nada illa toh bamu tsaya ba, sai muka tuntubi kwararren likita na asibitin da ke cikin jami’ar Usmanu Dan Fodiyo dake nan Sakkwato wato Dakta Bala Gadanga inda yayi mana karin haske akan lamarin.

Ya bayyana mana cewar sanya matsattsun tufafi na taimakawa wajen takurewar magudanun jini har ya kai ga toshewa wanda hakan nada matukar illa ga lafiya da kuma rayuwar Al’umma.

‘Sanya matsattsun tufafi  nada illa domin yana kawo matsala ga sinadarin tissue na jikin dan adam.’ In Dakta.

Haka kuma ya ci gaba da cewa, matsattsun tufafi na taka rawa ainun wajen haifar da cutar nan ta sanyin mata wato infection saboda rashin samun wadatacciyar iskar da ya dace jiki ya samu tare da hana zufa fita yadda ya kamata daga jikin dan adam yayin da zufan mace ke komawa cikin jiki, wanda hakan sam ba shi da kyau ga lafiyar dan Adam kuma yana da illa ga rayuwa.

 Da wannan ne kuma Managarciya ke  cewa yakamata  mata su hankalta su rika sanya suturar da ta dace ko don samun kwanciyar hankali da kulawa da lafiya kasancewar sanya matsattsun tufafi na daya daga cikin dalilan da ke haifar da yawan matsalolin fyade ga ‘yan mata kuma yana taimakawa wajen tsagewar fata a cikin lokacin hunturu wato sanyi.