LISSAFIN ƘADDARA: Fita Ta 11&12
sannu Manu ya gajiyar hanya" Mahaifinsa ya faɗa cike da kulawa "Alhamdulillah Baba""ai nayi tunanin ka koma bacci ne,kai da ka dawo daga tafiya ai hutu ya kamata ka samu"cewar Mama da take shan kayan marmari,matsawa yayi ya ɗauki ayaba ya ɓare ya miƙawa Mama dan yasan akwaita da son ayaba karɓa tayi tan murmushi gami da sanya masa albarka "ameen Mamana tafi ta kowa,wai kinsan abun mamakin da na gani kuwa Mama?"ba shiri ta gyara zama dan tasan Manu baya zance shiririta "eh lallai Manu iya shegan naka da son kan da kake nunamin da waren da ake nunamin har a gabana ai da na zata sai a waya,zakayi waya kullum da ita ni kuwa baifi sau daya ba muke a wata"Baba ya ƙarasa maganarsa cikin sigar wasa "haba Baba ai in ana dara fidda uwa ake ai kai na musamman ne haka nake jinka anan

LISSAFIN ƘADDARA
*ZAINAB SULAIMAN*
(Autar Baba)
*DEDICATED TO SHAMSIYYA MANGA*
Not edited
P 11&12
yana barin gidan tayi daɓas a qasa tana kukan fili da na zuciya ita dai bata taɓa yiwa ubangiji laifi mai tsanani ba sannan tana iya ƙoƙarinta wajen kare haƙƙin Allah a da tayi tunanin sai kayi laifi mummuna wa ubangiji sannan yake haɗaka da mummunan ƙaddara,duk da tasan bijirewa mahaifinta da tayi shine babban kuskurenta a rayuwa,to amma ai ta tuba kuma mai yasa ƙaddararta zata shafi yaranta tabbas bazata bari wani abu ya sami Ameenatuh ba dan bazata yafewa kanta ba,yarinyar da tun tana ƙarama ta sadaukar da farin cikinta domin ganin walwalar Mahaifiyarta da ƴar uwarta,yarinyar da take ɓoye damuwarta dan kar su shiga damuwa,yarinyar da tunda aka haifeta batasan wani waishi farin ciki ba kuma duk hakan tafaru ne sanadiyarta da a ce ta yarda da zaɓin mahaifinta da duk hakan bata kasance dasu ba,to amma ita Ameenatuh ya makomarta zata kasance in taƙi yarda da haɗin mahaifinta,bataso Ameenatuh tayi irin rayuwar da tayi dan haka ta tashi tana mai goge hawayen da suka gama wanke mata fuska ta wuce ciki,
a can part ɗin Hajiya Mama kuwa Abban Hammad ne ya shiga da sallama a falo ya sami Mahaifinsa tare da Mama suna hira cike da soyayya shima ya samu guri ya zauna ƙasan carpet yana mai ƙara gaisuwa a gare su,
"sannu Manu ya gajiyar hanya" Mahaifinsa ya faɗa cike da kulawa "Alhamdulillah Baba""ai nayi tunanin ka koma bacci ne,kai da ka dawo daga tafiya ai hutu ya kamata ka samu"cewar Mama da take shan kayan marmari,matsawa yayi ya ɗauki ayaba ya ɓare ya miƙawa Mama dan yasan akwaita da son ayaba karɓa tayi tan murmushi gami da sanya masa albarka "ameen Mamana tafi ta kowa,wai kinsan abun mamakin da na gani kuwa Mama?"ba shiri ta gyara zama dan tasan Manu baya zance shiririta "eh lallai Manu iya shegan naka da son kan da kake nunamin da waren da ake nunamin har a gabana ai da na zata sai a waya,zakayi waya kullum da ita ni kuwa baifi sau daya ba muke a wata"Baba ya ƙarasa maganarsa cikin sigar wasa "haba Baba ai in ana dara fidda uwa ake ai kai na musamman ne haka nake jinka anan" Abban Hammad ya ƙarasa maganar da nuna saitin zuciyarsa kafun ya daidaita fuskarsa ta dawo ba wasa a tattare da ita yace "Mama yau naga abunda ya shayar da ni mamaki har na gaza ɓoyewa,yau naga mai kam da ke sak wallahi Mama har maganarku iri ɗaya ce kuma kinsan mai Mama?"cike dason jin ƙarashen labarin tace"a'a ai sai ka faɗa" "hmm Mama sunansu iri ɗaya da ƙanwata Maryama duk da ban taba ganinta ba amma ai ke na sha ganinki har a mafarkina" gaba ɗaya jikin Mama ya mutu tsigar jikinta ta tashi ji take akamar ana mata tafiya akanta kalar tafiyar tsutsa bashiri tace"Usumanu Allah yana halitta mabambanta kum bana cire tsammani ɗiyata Mairamu ka ga ni,to to a ina ma ka ganta Usumanu kai ni garet dan ko kowa zai manta kalar Mairamuta ai ni bazan manta"ai tun kan ta ƙarasa maganar tayi daki da sauri ta ɗauko mayafi ta lilliɓa tace"taso muje hanzarta""ina zakije"cewar Baba da ya harɗe a saman kujera "ko kallonsa batayi ba ta ƙara bawa Abban Hammad umarni akan ya tashi suje ganin mai sunan Mairamu sai dai taji dirar kalaman Baba cikin ɓacin rai da bada umarni yace"ina daɗa jaddada miki Maijidda ki fita idona in rufe ba tun yau ba in kuma zaki tsallakewa umarnina ga hanya nan,kuma Maryama tana cikin gidan nan a matsayin ƴar aiki ita da tarkacen ƴaƴanta,ki kula ki kiyayi saɓawa maganata Maijidda"ya juya akalarsa ga Abban Hammad yace "Inaso ta tsaya matsayinta in kuma ba haka ba zan kaɗata ta bar gidan nan wawaye kawai" yadda Mama ta saki baki tana kallonsa kai kace doluwa ce,sai da ta tabbatar Manu ya bar sashin nasu jiki a mace sannan ta dubi Baba tace"kayi haku Baban Mairamu amma a wannan karon bazan taɓa gangancin barin Mairamu ta tafi inda bani da masaniya akai ni ma ina da haƙƙinta ba kai kaɗai ka haifamun ita ba,kullum da anyi magana kace ai ta saɓa maka ta bijire maka ake saɓawa Allah ma kuma ya yafe,shekaru sha bakwai kenan rabona da Mairamu tun da na aureka na kasance mai biyayya a gareka kawo yanzu baka taɓa aje kara na ƙetare ba,Babam Mairamu ina maka albishir da cewa a wannan karon zan iya barin kowa akan ƴata inasonta ba wai bansonta bane yasa nake maka shiru ba cikinta na dauƙa ana wata tara sai da nayi goma sha ɗaya akan Mairamu dan haka ba wanda zai nuna ya fini son Mairamu"tana kaiwa nan fuuu ta wuce bedroom tana sharɓar kukanta son ranta kuma tana aiyan tabbas rabuwarsu tazo da Baban Mairamu sai,
baki sake ta barshi a falo dan kuwa ta gama kasheshi da mamaki matar da tunda suke bai taɓa cewa A tace B ba sai in yace to itama haka zata maimaita sai gashi yau da kanta da bakinta take furta sai dai su rabu, tunanin mafita ya shigayi a fili yace "ko haka ta tsaya ai ta tabbar Annabi Musa ba ɗan Allah bane manzonsa ne,ni dama na jima da yafe miki Maryama na barki ne duniya ta faɗamiki gaskiya",
A yadda ta shigo ɗaki ne ya ƙara tabbar musu ba lafiya,da sauri suka tashi har suna rigerigen tarota,har bakin katifarsu suka zaunar da iya "Umma mai kuma yayi miki?"Khadija ta fada cikin sarƙewar muryar kuka Ameenatuh kuwa tama kasa magana sai shafa bayan Umma da takeyi,wata wawiyar a jiyar zuciya Umma ta sauke hawaye na gangarowa ta kuncinta tace"komai! yayi mun komai Khadija Abbanku yamun komai!!!"tunkan ta ƙarasa ta fashe da kuka tace"Khadija Abbanku yamun komai yanzu kuma rayuwata yakeso da ta Ameenatu,duk ƙalubalen rayuwar da muka shiga bai wadatar dashi ba yayi burus da lamuranmu yanzu kuma rayuwar mu yazo ɗauka"gaba ɗaya suka rungumeta suka fashe da kuka mai tsuma zuciya,kafaɗar Ameenatu ta girgiza tace "kece farin cikina a yanzu kece kuma duk wata damuwa Ameenatu tabbas na zaɓi dauwama a rayuwar rashin ƴanci akan akan na bada aurenki,ku haɗa kayanku yanzu zamu bar gidan zamuyi nesa da kowa zamuyi hijira dan gujewa mahaifinki"kuka take sosai tana magana gwanin ban tausayi"Umma ba in da zamu domin kinsan ba'a gujewa ƙaddara Umma mu tsaya mu fuskanci ƙaddararmu,kiyi mana bayanin abunda yace miki shin kuma da gaske mhaifinmu ne""kwarai mahaifinku ne kuma bazamu iya fuskantar ƙaddararmu ba a halin da muke ciki zuciyata ƙuna take zuciyata zata buga,kuma ya nemi na bashi ke ya aurawa abokinsa nan da juma'a"gaban Ameenatu ne ya faɗi dan ita ko a mafarki akayi mata maganar aure ai ta ƙaryata dududu shekarta sha shida ina ita ina batun wani aure,
"to Umma mai kika ce masa kuma?" Khadija ta jefawa Umma tambayar "haba Khadija ai abunda zance a bayyane yake ni ban amince ba""a'a Umma ki amince kawai idan da rabon munzo duniya ne dan faɗawa ƙaddarori haka bakisan mai gobe zata haifarba,wasu suna fara rayuwarsu da ƙaddara kuma su rufe da samun nasar cin jarabawar ubangiji wasu kuma su fara da ƙaddarar kuma su kasacin jarabawa wasu kuma zasu fara da ƙaddara su kuma gama rayuwarsu a ƙaddara ne Umma baki san tanadin da Ubangiji yayi mana ba dama ni nasan nazo duniya ne badan jindadi ba nazo ne dan karɓar abunda Allah ya tsaramun,....
ina godiya da addu'o'inku gareni nagode da sharhi sosai da sosai,
Za'a jini shiru gobe zuwa sunday mun shiga hidimar biki ne,.