Farfesa Yusuf: Shaikh Gumi Ya Zargi Tinubu da Kama 'Yan Adawa da Manufar Siyasa 

Farfesa Yusuf: Shaikh Gumi Ya Zargi Tinubu da Kama 'Yan Adawa da Manufar Siyasa 


Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya yi gargadi ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan kama mutanen da ke sukar gwamnatinsa. 
Malamin ya yi zargin cewa kama tsohon shugaban hukumar NHIS, Farfesa Usman Yusuf, wani abu ne da ke nuna zalunci da kuma ramuwar gayya ta siyasa. 
Legit ta tattaro kalaman Sheikh Ahmad Gumi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a safiyar ranar Alhamis. 
Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa kama Farfesa Yusuf a irin wannan lokaci na matsin tattalin arziki da rudanin siyasa ba abu ne mai kyau ba. 
Malamin ya ce irin waɗannan matakai na iya shafar martabar gwamnatin Tinubu a idon 'yan Najeriya. 
A cewar Sheikh Gumi: "An cafke mutane bisa tuhuma da ke nuna ramuwar gayya ta siyasa, hakan ba abu ne mai kyau ba a irin wannan lokaci da Najeriya ke fama da matsaloli." 
Sheikh Gumi ya kara da cewa ya san Farfesa Yusuf sama da shekaru 49, kuma ya tabbatar da cewa mutumin kirki ne da ke adawa da duk wani nau'in zalunci tun zamanin su na jami’a. 
A kan haka malamin ya bukaci shugaba Tinubu da kada ya bari 'yan-miya-ta-yi-dadi su bata masa suna.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an EFCC sun dira gidan tsohon Shugaban NHIS, Farfesa Usman Yusuf, da ke Abuja da misalin karfe 4:30 na yamma a ranar Laraba, inda suka kama shi. 
Majiyoyi daga hukumar EFCC sun tabbatar da cewa Farfesa Yusuf yana hannun hukumar, kuma ana yi masa tambayoyi kan badakalar wasu makudan kudi. 
Premium Times ta rahoto cewa ana zargin ya tafka almundahana a fannin fasahar zamani, aka ce ya kara kasafin kudi daga N4.9bn zuwa N8.7bn ba tare da bin ka’ida ba.