Daga Ibrahim Hamisu.
A kokarin da ake na tabbatar da zaman lafiya da bin doka da Oda a fadin Jihar Kaduna,
Ƙungiyar nan ta Arewa Consultative Synergy Congress (ACSC), ta roki Gwamna Malam Nasiru El-Rufa’i da ya sake duba harkokin hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa na Jihar Kaduna wato (KASTLEA).
A wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar (ACSC) na kasa Engr. Dakta Harris (EI-Rasheed) Moh’d Jibril, ya fitar wa gaanema labarai a ranar Laraba da ta gabata a garin Kaduna, ya ce ana yawan samun jami’an hukumar KASTLEA da yin amfani da karfi fiye da kima, rashin da’a da rashin sanin ya kamata, yayin da suke gudanar da ayyukansu a kan manyan hanyoyi.
Ya kara da cewa, rashin da’a iri-iri da wasu daga cikin ma’aikatan ke nunawa a yayin da suke gudanar da ayyukansu na da matukar tayar da hankali wanda ya sa ya zama wajibi kungiyar ta rubuta masa damuwarta game da rashin da’a da Jami’an KASTLEA suke yi ga ‘yan Jihar Kaduna.
Dakta Jibrin Ya ce, “Tun da aka haife ni har na girma a garin Kaduna duk tsawon rayuwata, har da iyayena da suka gabace ni, ko shakka babu na shaida gagarumin aikin sabunta birane, da farfado da martabar Jiharmu ta Kaduna a karkashin gwamnatin malam Nasir don haka wannan aiki abin yabawa matuƙa.”
“Duk da haka KASTLEA wata hukuma ce da gwamnatin Jiha ta kirkira kuma an kafa ta a ƙarƙashin wata doka ko ƙa’idar aiki bisa kyakkyawar manufa, sai dai tabbas muna fama da jin jiki, cin zarafi ko zalunci da aiwatar da waɗannan dokokin muhalli guda 8 ba sa cikinsa.”
“Rundunar Sojoji da suke gudanar da ayyukansu a manyan tituna ba su da kwarewa sosai, rashin bin doka da oda kuma a matsayina na mai son ku kuma dan’uwanku fatana da sunan ku ya kasance jagora a dora masa laifin yin abin da ya dace fiye da laifin aikata ba daidai ba, ina so ku lura da wannan tashin hankalin da bai yiwa ’yan kasar da suka zabe ku dadi ba kuma kuka rantse sannan kuka yi alkawarin kare ku,
“Tabbas mun shaida irin yadda suke ta’ammali da aikinsu wanda gaba daya ba su da tausayi fiye da na “VIO” da kuka wargaza, muna tafiya nesa da kusa a ciki da wajen kasar nan, mun shaida yadda ake aiwatar da doka da aiwatar da ita cikin kwarewa da mutunci da ladabi.”
“Jami’an KASTLEA ba sa bin ainihin manyan laifukan da direbobin ‘yan kasuwa ke aikatawa, ko kuma wuraren ajiye motocin da ba daidai ba a kan manyan hanyoyinmu fiye da kima na mutane da kayayyaki, maimakon haka suna mayar da hankali kan abin hawa tare da ƙananan batutuwa kamar bayanan abubuwan hawa (takardu), mafi muni sai su gangaro wa iyaye mata da ba su ji ba ba su gani ba, wadanda garin kokarin gaggawar kai yaranmu Makaranta suka manta da lasisin tukinsu ko kuma jinkirta wani dan kasa mai kishin kasa wanda ya manta ya saka belet din kujerarsa garin sauri da safiya ko sabunta takaddun abin hawa ba tare da taka tsantsan ba.”
“A halin da ake ciki yanzu, Jami’an a wasu lokuta suna cutar da direbobin ta hanyar cire lambar su ko kuma cin zarafi ko fada, da dukan mota a kan hanya ko fasa madubin amadadin matsalolin da za a iya warware su cikin aminci da kwarewa.” A cewar sanarwar
A karshe, wannan ƙungiya ta ACSC ta jaddada cewa a yanzu muna cikin mulkin farar hula ne, don haka ya kamata ayyukanmu su zama na bin doka da oda ne, sannan ta godewa Gwamnan Jiha Malam Nasir El-Rufa’i bisa gagarumin ayyukan da ake aiwatarwa a Jihar Kaduna.