Gwamnatin Tarayya za ta kashe fiye da kudin ayyukan ci gaba wajen biyan bashi cikin shekaru uku

Gwamnatin Tarayya za ta kashe fiye da kudin ayyukan ci gaba wajen biyan bashi cikin shekaru uku

Gwamnatin Tarayya tana shirin ware babban kaso na kasafin kudinta don biyan bashin da ake bin ta maimakon ayyukan ci gaba tsakanin 2025 zuwa 2027.

Bayanin hakan ya fito ne daga sabuwar takardar Medium-Term Expenditure Framework and Fiscal Strategy Paper na 2025–2027 da aka amince da ita kwanan nan, wadda ta yi hasashen cewa za a kashe Naira tiriliyan 50.39 wajen biyan bashin cikin shekaru uku, wanda ya zarce Naira tiriliyan 48.93 da aka ware don ayyukan ci gaba.

Yawan kudin biyan bashin da ake sa ran zai karu da kashi 26.7% daga Naira tiriliyan 15.38 a shekarar 2025 zuwa Naira tiriliyan 19.49 a shekarar 2027, yana kara tayar da hankalin masu lura da yanayin kudin kasar.

Don bayar da ma'ana, a shekarar 2023, Gwamnatin Tarayya ta kashe Naira tiriliyan 8.56 wajen biyan bashin, wanda ke nuni da cewa adadin na 2027 ya karu da kashi 127.7% cikin shekaru hudu kacal.

A wannan lokacin, biyan bashin zai lashe kashi 34.06% na jimillar kudaden kashewa na shekara, yayin da bunkasar kudaden ayyukan ci gaba ke tafiyar hawainiya, inda za ta karu da kashi 0.18% daga Naira tiriliyan 16.48 a shekarar 2025 zuwa Naira tiriliyan 16.51 a shekarar 2027.

Bincike mai zurfi kan hasashen kudin ya nuna cewa a shekarar 2025, kudaden ayyukan ci gaba za su kai kashi 34.44% na jimillar kasafin kudin, kadan ne kawai ya fi kashi 32.11% da aka ware don biyan bashin.

Sai dai, zuwa shekarar 2027, ana hasashen cewa biyan bashin zai karu zuwa kashi 37.2% na jimillar kudaden kashewa, idan aka kwatanta da kashi 31.51% da aka ware don ayyukan ci gaba.