Magajin Garin Sakkwato Alhaji Hassan Ahmad Danbaba ya rasu a yau Assabar yana da shekara 54 a duniya bayan gajeruwar rashin lafiya ta kwana daya.
Margayin yabar matan aure uku da diya shida mata 5 namiji daya.
Hassan Muhammad Binanchi daya daga cikin makusantan Magajin Gari ne ya tabbatar da rasuwar ya ce Magaji ya rasu ne a jihar Kaduna bayan gajeruwar rashin lafiya data same shi a jiya ta sanadiyar tuntube da ya yi a kafarsa.
Ya ce margayin ya rasu a yau da safe, 'anan take muka samu wannan labarin da ya ya matukar girgiza mu, an yi rashin sadauki mai taimakon al'umma da tausaya musu'.
Magajin Gari Sakkwato babbar sarauta ce a fadar sarkin Musulmi dake mataki na uku a tsarin fadar Sarkin musulmi daga Sarki sai Waziri sai Magajjin Gari.
Alhaji Hassan Dan baba sanannen mutum ne a Nijeriya wanda yake jika ne a wurin Margayi Sardaunan Sakkwato Ahmadu Bello, a watannin baya ne mahaifiyarsa da take diya ga Sardauna ta rasu, yanzu kuma shi ya bi ta.
Za a yi janazarsa a jihar Sakkwato, bayan da aka kawo gawarsa, kamar yadda makusantan suka fada.