Ku ɗauki ƙaddara, tsautsayi ne, Gwamnan Sokoto ya faɗa wa mutanen garin da sojoji su ka jefa wa bam

Ku ɗauki ƙaddara, tsautsayi ne, Gwamnan Sokoto ya faɗa wa mutanen garin da sojoji su ka jefa wa bam

Gwamna Ahmad Aliyu na Sokoto ya bayyana harin bam din da sojoji suka yi cikin kuskure, wanda ya hallaka mutane sama da 10 a jihar a matsayin wani abu na ƙaddara.

Idan dai za a iya tunawa an kashe mutane sama da 10 tare da jikkata wasu da dama a kauyukan Rumtuwa da Gidan Sama da ke karamar hukumar Silame a harin da sojoji su ka kaiwa yan ta'adda a jihar.

Harin ya kuma yi sanadin kashe dabbobi 100 da suka hada da rakuma, shanu, da jakuna.

Amma da ya ke magana da sashen Hausa na BBC, Gwamna Aliyu, wanda ya halarci jana’izar wadanda aka kashe, ya bukace su da su ɗauki ƙaddara a matsayinsu na musulmi.

Ya kuma tabbatar wa al’umma cewa harin bam din kuskure ne.

“Shin kun ji labarin cewa wasu sun shigo kasar nan, kuma wannan ba shi ne karon farko da sojoji suka kai musu hari ba? To sun saba yi amma ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba kuma duk su na samun nasara.

"Saboda haka wannan tsautsayi ne kuma mu dauki ƙaddara a matsayin mu na Musulmai," in ji shi.