Boko Haram ta halaka manoma 40 a jihar Borno
Daga Shamsudeen Muhammad, Maiduguri
Majiya mai qarfi ta tabbatar da yadda mayaqan Boko Haram suka halaka fararen hula 40 a qaramar hukumar Kala Balge da ke jihar Borno.
Bayanan da wakilinmu a jihar ya tattara, sun nuna irin yadda ayarin mayaqan suka yi wa waxannan bayin Allah qawanya tare da yi musu yankan rago xaya bayan xaya, a ranar Lahadi da ta gabata.
Yayin da take mayar da martani dangane da wannan mummunan aika-aika, yar majalisar wakilai da take wakiltar yankin, Hon. Zainab Gimba, ta tabbatar wa da BBC Hausa aukuwar labarin.
Har wala yau, ita ma wata majiyar jami'an tsaro a yankin ta tabbatar wa da wakikinmu faruwar farmakin wanda ya jawo salwantar rayukan jama'a da dama, waxanda kuma tuni aka yi jana'izarsu kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
Mista Zagazola Makama, qwararre ne kan yaqi da matsalar tsaro kuma mai fashin baqi dangane da al'amurran Tafkin Chadi, ya bayyana cewa harin ya yi sanadin rayukan gwamman manoma, biyo bayan farmakin mayaqan.
Wanda ya qara da cewa, ana ci gaba da bincikar gawawakin mutanen da yan bindigar kan mashinan hawa suka aikata kan fafaren hula kuma manoma a garin Rann, shalkwatar qaramar hukumar Kala-Balge a jihar Borno.
Ya ce, “Sama da manoma 40 ne abin ya rutsa dasu, yayin da aka yi gunduwa-gunduwa da jikinsu, wasu kuma an xaure su tamau kan yan ta'addan su yanka su."
“Haka kuma, tuni an gudanar da jana'izar gawawakin da aka samu a ranar Litinin, wanda har yanzu ba a samu gawawakin wasu da dama a cikin su ba.” Ta bakin Zagazola.
managarciya