Har yanzu ba mu fara tattauna batun Maja da PDP da NNPP ba -Obi

Gabanin zaɓen 2027, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP) a 2023, Peter Obi, ya ce har yanzu babu wata yarjejeniya ta haɗin gwiwa da jam'iyyar PDP, NNPP, ko wata jam’iyya.
Obi, wanda tsohon gwamnan jihar Anambra ne, ya bayyana hakan ne a safiyar yau Alhamis yayin da ya gudanar da taron manema labarai a Abuja kan halin da ƙasa ke ciki.
Ya ƙara da cewa ba a cimma wata yarjejeniya da sauran jam’iyyu ba tukuna, inda ya kuma yi kira ga duk masu kaunar Najeriya a cikin harkar siyasa da su haɗa kai a 2027 domin kayar da jam’iyyar APC, wacce ya zarga da rashin kyakkyawan sarrafa albarkatun ƙasar.