Ba Wanda Za Mu Baiwa Hakuri Don Mun Gayyato Malami Daga Kasar Waje----Sarkin Musulmi

Ba Wanda Za Mu Baiwa Hakuri Don Mun Gayyato Malami Daga Kasar Waje----Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya ce Musulman Najeriya na da ’yancin gayyatar dan uwansu daga ko ina a fadin duniya domin ya yi wa’azi a kasar.

Basaraken na mayar da martani ne ga masu sukar lamirinsa kan gayyato fitaccen malamin addinin Musuluncin nan mai wa’azi dan asalin kasar Indiya, Sheikh Zakir Naik.

Malamin ya isa Sakkwato ne a farkon makon nan domin yi wa’azi a wasu Jihohin Najeriya, bisa gayyatar Sarkin Musulmin.

To sai dai da yake mayar da martani ga masu sukar lamirin nasa yayin rufe taron Makon Usmanu Danfodiyo da ya gudana a Sakkwato, Sarkin ya ce, “Shi Musulunci daya ne duk inda ka je.

“A matsayinmu na Musulmai, muna da damar gayyatar ’yan uwanmu Musulmai domin yin mu’amala da su. Na fara haduwa da Dokta Zakir Naik tun shekaru 11 da suka gabata.

“Sakkwato na farin cikin karbar bakuncinka. Mu muna alfahari da kasancewarmu Musulmai, kuma muna aiki ne domin ci gaban Musulunci, ba wai kowa ba.

“Mu Musulmai ne saboda haka Allah Ya ga dama, kuma babu wanda ya isa ya canza haka, muna gode wa Allah da ya yi mu a matsayin Musulmai,” kamar yadda ya bayyana yayin gangamin rufe taron a Cibiyar Taro ta Kasa da Kasa da ke Sakkwato.

Sarkin Musulmin ya ce malamin ya yi kokari matuka wajen ilimantar da Musulmai da ma wadanda ba Musulmai ba abin da Musulunci ya kunsa.Za