Bikin Easter: Buni ya bukaci Kirista suyi addu'ar samun nasarar mika mulki ga sabuwar gwamnati

Bikin Easter: Buni ya bukaci Kirista suyi addu'ar samun nasarar mika mulki ga sabuwar gwamnati

Daga Muhammad Maitela, Damaturu.

Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya bukaci mabiya addinin Kirista a Nijeriya suyi amfani da bikin Easter wajen yin addu'o'i na musamman domin samun nasarar mika mulki ga sabuwar gwamnati mai zuwa.

A sanarwar manema labaru mai dauke da sa hannun mai magana da yawun Gwamnan, Alhaji Mamman Mohammed ya ce Buni ya sanar da hakan ne a sakon sa na bikin Ranar Easter da ya aikewa mabiya addinin Kirista.

Ya kara da cewa, abu ne mai mahimmanci ayi amfani da wannan lokacin wajen nuna kauna da soyayya tare da sadaukarwa a matsayin sakon da yake kunshe a bikin Ranar Easter ga kasar mu Nijeriya.

"Kyakkyawan darasin da yake tattare da wannan rana shi ne kaunar juna da sadaukarwa, wanda suka dace a aiwatar dasu wajen bunkasa zaman lafiya da hadin kai don ci gaban Nijeriya da yan kasa baki daya." Ya nanata.

Har wala yau, Gwamna Buni ya shaidar da cewa, wannan lokaci ne mai albarka wanda mabiya addinin Kirista suke gudanar da harkokin ibada a cikin na Easter, kuma a daidai lokacin da al'ammar musulmi suke gudanar da azumin watan Ramadan.

"Wanda saboda haka, wannan babbar dama ce garemu a matsayin yan kasa, muyi amfani da wannan lokacin mu yi addu'o'i na musamman ga kasarmu." In ji Gwamna Buni. 

Gwamnan ya jaddada kira ga shugabanin addini da na al'amma, kowane lokaci su rinka yin wa'azuka da kira wajen samun dawamamen zaman lafiya da fahimtar juna.

"Matikar mun aiwatar da koyarwar addininmu, zamu samu ci gaba mai dorewa ta hanyar samun zaman lafiya."

"Saboda a yan shekaru kadan da suka gabata, ba zamu iya zuwa masallatan mu da coci cikin nutsuwa ba a jihar Yobe, sakamakon matsalolin tsaro da muka sha fama dasu, amma yanzu cikin taimakon Allah, zaman lafiya ya dawo kowa yana harkokin sa cikin limana."

"Bisa ga wannan, mu yaki son zuciya tare da yaki da shaidan don kaucewa abubuwan da zasu harzukamu zuwa aikata abin da zai kawo tashin-tashina a jiharmu ta Yobe da Nijeriya baki daya." In ji shi.