Kotun Koli Za Ta Saurari Bukatar  Mainasara Kan Rikicin Shugabancin APC a Sokoto

Kotun Koli Za Ta Saurari Bukatar  Mainasara Kan Rikicin Shugabancin APC a Sokoto

Kotun kolin Nijeriya za ta soma sauraren bukatar da Honarabul Mainasara Sani ya gabatar a gabanta na duba shari'arsa da ya jingine bayan daukaka kara daga kotun daukaka kara.
Mainasara yana kalubalantar shugabancin Isah Sadik Acida a matsayin shugaban jam'iyar APC a Sokoto.
Mainasara Sani yana ganin shi ne shugaban jam'iyar APC a jiha Wanda aka zaba rikicin da aka dade ana yi tun bayan kammala zaben shugabannin jam'iyar APC da aka yi a shekarar data gabata.
A gobe Litinin Kotun Koli za ta duba bukatar Mainasara Kan neman duba kararsa da ya daukaka bayan fita batun maganar Karar da ya yi.
Managarciya ta nemi jin ta bakin Mainasara Kan shariar  amma wayarsa bata shiga kan matsalar sadarwa.
Haka ma Isah Sadik Acida baya kusa ga waya an kira shi sau biyu bai daga ba har zuwa hada rahoton.
Wani lauya a Sokoto ya tabbatarwa Managarciya zaman Karar da za a yi gobe, har lauyoyin APC bangaren Isah Sadik sun Isa Abuja a lokacin da yake magana.