2027: Mun shirya yadda za mu kwace mulik a Sakkwato---Sanata Tambuwal

2027: Mun shirya yadda za mu kwace mulik a Sakkwato---Sanata Tambuwal
Tsohon Gwamnan Sakkwato Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya ba da tabbacin za su sake dawo da mulkin Sakkwato a bangarensu nan ba da jimawa ba.
Sanata Aminu Waziri Tambuwal a gaban magoya bayansa a lokacin da yake kaddamar da rabon shinkafar watan Azumi a ranar Litinin cikin gidansa dake birnin Sakkwato ya ce sun shirya tsaf domin ganin mulkin jihar Sakkwato ya dawo bangarensu ganin yadda gwamnati mai ci ta kasa ciyar da jihar a gaba.
"Da yardar Allah a shirin da muka yi za mu sake dawo da mulkin jihar Sakkwato domin cigaba da ciyar da jihar gaba, da ikon Allah abin da muka rasa zai dawo.
"A wannan shekara iyalai dubu 30 be za su amfana da wannan tallafin dana samar, wanda hakan zai taimaka ga rage radadin da ake fama da shi," a cewar Tambuwal
Sanata ya jinjinawa 'yan majalisar tarayya da jiha na jam'iyar PDP kan samar da wani tallafi da dukkan matasa a Sakkwato za su amfana ya ce wannan shi ne karon farko da aka samar da irin wannan tallafin a jiha.
"Dole a godewa matasan 'yan majalisar tarayya musamman su biyu da suka hade kansu don kawowa matasa cigaba abin a yaba ne da hakan kuma za mu kai ga nasara in da muka dosa."