Kasan Wane ne Barista Bello Goronyo?

Barista Bello Goronyo sanan ne da ya fito a cikin tsatson wadanda da suka kafa Daular Usmaniya dake jihar Sakkwato.
An haife shi a garin Goronyo daya daga cikin kananan hukumomi dake jihar Sakkwato salsalarsa ba ta yanke ba har kan Shaikh Usman Danfodyo mujaddadin addini a Afirika ta yamma.
Bello Goronyo mutum ne dan baiwa, ya samu damar zuwa jami'aar Usman Danfodiyo in ya karanta fannin shari'a, waton shi yana da digiri kenan.
Samu ilmi da ya yi a fannin ya sanya ya amfanin mutane da ilminsa, wurin kokarin kare dokokin kasa da kare maras karfi a cikin al'umma hakan ya kara fito da martabarsa ganin yanda ya dauki al'umma da daraja.
Haka ma burin da yake da shi na taimakon al'ummar Nijeriya ta hanyar jagoranci a siyasa bai hana masa cigaba da aikin lauya ba.
Shigarsa harkokin siyasa ya fito da hangen nesansa da basirar da yake da ita, a matsayinsa na mamba a jam'iyar APC bai sha wahalar zama daya daga cikin jagororinta ba, in da ya zama sakataren yankin Arewa maso yamma mukamin da yake da ta cewa da hidima kansa wanda sai jajirtacce ake baiwa shi.
Goronyo gogewarsa a siyasa ta taimaka sosai wurin samar da nasara ga jam'iyarsa a yankin Arewa, jama'a nada yakinin shi nasu ne.
Kafin ya samu wannan mukamin na karamin minstan ruwa da tsaftar muhalli ya rike mukamai da dama a harkokin siyasa kamar shugaban masu rinjaye da mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Sakkwato, da kwamishina a gwamnatin jiha dukkansu ya taka rawar da ta taimaka wurin samun nasarar da yake saman ta a yau.
Nasarar da Bello Goronyo ya samu tabbaci ne ga irin gidan sarauta da ilmi da hangen nesa da ya fito.
Sadaukarwarsa ga tushensa da jama'arsa da kasarsa ya taimaka masa sosai ya cigaba da yi wa jama'a hidima, tarihi ba zai manta da rawar da ya taka a matsayinsa na lauya dan siyasa mai son cigaban Nijeriya.
A kasar Goronyo tarihi zai cigaba da tuna Barista Bello Goronyo a kokarinsa na gina matasa domin ganin sun cimma burinsu na rayuwa, da saudakarwar da yake da ita ganin dai gobensa ta yi kyau.