KIN TAƁA HAƊA ALALAN MASARA MAI DAƊIN GASKE

         KIN TAƁA HAƊA ALALAN MASARA MAI DAƊIN GASKE
BASAKKWACE'Z KITCHEN
          ALALAN MASARA 
Ingredients.
Masara ɗanya,wacce de bata bushe ba.
Manja da mangyaɗa.
Hanta
Ƙwai
Albasa,tattasai,tarugu
Spices.
Maggi&gishiri.
Gwango ko leda
METHOD
Da fari aunty na zaki wanke ɗanyen  masarar ki,ko wacce bata gama bushewa ba,ki jiƙa ta  ki zuba tattasai da tarugu da albasa ki kai niƙa,bayan an kawo nikar ki sa ruwa kaɗan,ki ɗauko gishiri da magi ki zuba,ki ɗauko dafaffiyar hantar ki ki zuba,ki ɗauko dafaffen kwan ki ki zuba,se zuba kayan kamshi ki jujjuya ,se ki zuba a leda ko gwango ki ɗaura a wuta,da ya dahu zaki ji ƙamshi na tashi se ki sauke se ci da miya ko da manja da yaji.
MRSBASAKKWACE.