KANWATA: Fita Ta Ɗaya
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 1*
~Kauyene karami a yankin Adamawa anyi wasu 'yanmata guda biyu, su kad'aine iyayensu suka Haifa, suna zaune a unguwar ganye road, Babbar sunanta FADILA, karamar Sunanta AMRA, Fadila yarinyace me hakurin gaske ita kuma Amra batada hakuri ko kad'an, kyawawa ne sosai, Asalinsu fulanai ne, sunada gashi sosai saidai Amrah tafi Fadila tsayi dakuma hasken fata, Mahaifiyarsu ma kyakkyawace shima mahaifinsu ba baya ba wurin kyau, duk Inda kaga Fadila tofa zakaga Amra a wurin, Fadila tana matukar son kanwarta sosai, wasu lokutan idan Amra tayi laifi Fadila tana iya d'aukan laifin ayi mata hukunci, koda kitsone ita takeyiwa Amra, iyayensu suna matukar jin dad'in yanda suke zama cikin Aminci da kaunar juna, Abu d'ayane yake basu haushi shine yawan hakurin Fadila, Amra tana iya yi mata Laifi saidai tayi hakuri ta share hawayenta, daga baya takara Jan Amrah jiki ta bata hakuri, Fadila tanada saurayi KAMAL ita kuma AMRA tana secondary school sai next year zata gama.
"KAMAL yarone kyakkyawa fari dogo me class, shi kad'aine a wurin iyayenshi, mahaifinshi ya rasu sai mahaifiyarshi HAJIYA SARA, Hajiya Sarah tana matukar son KAMAL hakan yasa duk abinda yakeso tofa itama tanaso, KAMAL yanason Fadila sosai shiyasa Hajiya Sarah take sonta, saidai wani abunda yake had'ashi da mahaifiyarshi shine tad'au duniya da fad'in gaske, batada kunya ko kad'an, Tana harka da manya manyan masu kud'i, kasancewar Allah yayi mata kyau, hakan yasa take Jan hankalin maza, Kamal abin yana bashi haushi sosai, yayi mata fad'a takiji yayi fushi har yanzu bata dainaba, sai kawai ya hakura yanayi mata addu'a.
"yau ranar Talata 1/12/2020 daidai da ranar baikon Fadila da Kamal, Kamal ne zaune da Fadila suna hira a harabar gidansu Fadila, "Gaskiya zanyi farin ciki sosai idan na Aureki, sabida nasamu Mata me hankali da nitsuwa, uwa uba ga kyau ga hakuri"
Murmushi Fadila tayi tace "nima nayi farin cikin kasancewarka Wanda zan Aura, Ina Alfahari da kai, saidai wani abu guda d'aya danake tunawa yana tadamin hankali sosai, hakan yasa har ina ramewa"
Kamal cikin mamaki yace "menene wannan matsalar Fadila? Ki fad'amin idan har zan iya magance miki"
Idon Fadila ne ya cika da hawaye cikin muryanta me sanyi tace "banason Rabuwa da Amra, ina matukar sonta, itama nasan tana jin zafin zamu rabu b'oyemin kawai takeyi, naso ace rana d'aya zamuyi Aure da kanwata abun zaifi zuwa mana da sauki" share hawayenta tayi da gefen gyallenta tace "Amma ba komai haka Allah ya tsara mana, koda bamu rabu Dan Aure ba zamu rabu Dan Mutuwa"
"Ki daina maganar Mutuwa a wannan lokacin Fadila, kinsan cewa yau, za'ayi mana baiko ko?"
Gyad'a kanta tayi tace "nasani Kamal shiyasa kaga nace haka Allah ya kaddara mana"
Amra ce ta taso daga makaranta, cikin tafiyarta a hankali ta hango yayarta dakuma Wanda zata Aura, murmushi tayi ta karasa wurinsu, "Yaya Kamal sannu da zuwa, tin acan na hango Ku ai kuna murmushin soyayya, to Amma meya samu yayata naga kamar tayi kuka?"
Kamal ne yayi murmushi yace "kanwata ai kukan nan da kikaga tanayi, to kukan farin ciki ne, kinsan ai idan ana baiko Amarya kuka takeyi"
Dariya tayi tace "su Amarya manya"
Fadila ma dariya tayi tanajin son kanwar tata yana kara shiga zuciyarta, "kije ciki ki canja kayanki Amra, sai kizo muyi firan tare ko?"
Amra tace "to".
Bayan mintuna goma sha biyar saiga Amra cikin kaya irin na Fadila, tayi kyau sosai kamarsu takara fitowa, Murmushi ta sakar musu kamar yanda suma sukayi mata, zama tayi a gefen Fadila ta d'aura a hannunta akan cinyarta tace "Adda nayi kyau?" (Kasancewarsu Fulani shiyasa suke fad'awa yayunsu mata Adda, maza kuma Hamma) murmushi Fadila tayi tace "kinyi kyau sosai kanwata, haka nakeso kirika zama kyakkyawa a koda yaushe"
Kamal ne ya leko fuskarta yace "ji jambaki kamar me tallan Awara"
Turo baki Amra tayi tace "Yaya Kamal wallahi ka daina Neman tsokana ta, Dan kaga nafi matarka kyau shiyasa kake fad'an haka, to nima Wanda zan Aura yafika kyau da Aji da kuma iya gayu"
Tana fad'an haka ta mike tashiga cikin gida, Kamal sai dariya yake yana cewa "ke ai sai d'an kauye zaki Aura"
Fadila ce tahad'a rai alamar abun baiyi mata dad'iba, kallonta Kamal yayi yace "lafiya Amaryata?"
Dakewa tayi tace "eh"
Kamal dariya yayi yace.
"Lalle Fadila kinason Kanwarki sosai, sanin kanki ne nida Amra mun saba fad'an wasa, yanzu zamuyi fad'a kuma yanzu zamu shirya, meyasa Dan ranta ya b'aci na wasa zaki b'ata rai?"
Fadila turo baki tayi tace "to ai koda wasa banason ranta ya b'aci, kuma bayan Amra babu Wanda nakeso sai kai, Kamal ina sonka sosai, bazan iya rabuwa da kai ba, kayimin Alkawarin duk rintsi bazaka gujeni ba"
"Nayi miki Alkawari Amaryata, bazan tab'a rabuwa dake ba"
Murmushi tayi mishi me sanyi tace "bari nashiga gida na baiwa Amra hakuri ko?" Shiru yayi mata, ita kuma bata kulashi ba ta wuce cikin gida, tana zuwa ta tarar da Amra tana shan lemon kwalba hankalinta kwance suna hira da Mama, Murmushi ta sakar mata tace "Kanwata? Kin huce ne? Dama nashigone Dan in baki hakuri, sai kuma naga kin huce"
Amra cikin mamaki tace "Adda kema ai kinsan fad'anmu da Yaya Kamal, shine kuma zakizo kibani hakuri? Ni wallahi nama manta yanzu ina yake?"
Fadila tace "nabarshi a waje"
Amra tace "muje in nemi tsokanarshi"
Suna fita sukaga wayam yatafi Amra ranta ne yad'an b'aci ta juya wurin yayarta tace "baga irinshi ba, yanzu akan wani d'an kalilan na Abu kin jawo ranshi ya b'aci, ni gaskiya idan baki dena wannan abun ba raina zaina b'aci matuka" tana fad'an haka ta juya tayi tafiyarta,
Bin bayanta Fadila tafarayi tana cewa.
"Dan Allah kiyi hakuri Amra zan kirashi a waya in bashi hakuri, kuma nasan zai hakura"
Juyowa Amra tayi tace "kin tabbata zai hakura bazaiyi fishi dake ba?"
Dariya Fadila tayi ta sunkuyar da kanta tace "eh zaiyi kizoma in kirashi a gabanki kiji"
Zuwa Amra tayi suka zauna a gefe d'aya, Fadila ce takira Kamal, ringing kusan sau Uku kafin ya d'auka, shiru yayi, Fadila cikin sanyin muryanta me had'e da shagwab'a Wanda yariga yazama mata jiki tace "Dan Allah my fiancy kayi hakuri bansan ranka zai b'aci ba, am sorry"
Kamal Wanda yake kwance akan Sofa ya lumshe idonshi a hankali ya kuma bud'ewa da yayi niyan bazai hakura ba, Amma jin muryanta yasashi yaji yama hakura gaba d'aya, a hankali yace "ba komai na hakura my fiancy" (Fiancy yana nufin Wanda zaka Aura, misali anyi muku baiko ko makamancin haka).
"Amra ce ta mika mata hannu alamar su tafa, tafawa sukayi dukka sunajin dad'i, Amra tanajin dad'in Yayarta sun shirya da Masoyinta ita kuma Fadila tanajin dad'in Kanwarta ta saki fuska tana murna, Mama ce ta leko tace "ku shigo to kuyi wanke wanke naga bakuda Alamar shigowa"
Amrah ce ta mike cikin had'a rai tace "Mama yaufa naje Makaranta nagaji sosai bazan iya yin wanke wanke ba gaskiya"
Fitowa Mama tayi gaba d'aya tace "me naji kina fad'a Amrah? Bazakiyi wanke wanke ba?"
Amrah shiru tayi, Mama haushi tabata hakan yasa ta karaso wurinta zata zabga mata mari Fadila tayi saurin kai fuskarta, Tass kakeji Mari ya sauka akan fuskar Fadila, abin yabawa Mama haushi matuka, duk lokacin da Amrah tayi laifi idan zata daketa sai Fadila tayi sauri ta tare dukan abun yana kona mata rai, Janyo Fadila tayi tafara dukanta tana cewa "ke kikayi laifin ne da zaki tari Marin? To yau sai jikinki ya fad'a miki, gobe idan tayi laifi nazo zanyi mata hukunci to zaki kara karb'a mata, dukanta takeyi da iya karfinta domin ranta ya b'aci sosai,
Amrah ce ta iso wurin tana kokarin kwatan Yayarta, Mama janyo Amrah tayi ta had'asu dukka tana dukansu, Fadila ganin ana dukan Amrah saita fara kakkareta duk dukan daza ayi bata bari ya tab'a Amrah.
*Free book ne, kyauta ne kusha karatu lafiya amma ayi comment sosai da likes shi zaisa nasan kuna so*
_jiddah Ce...
managarciya