MAMAYA: Labarin Soyayyar Mutum Da Alajani, Fita 21
Page 21
Cikin kwanciyar hankali Bilkisu ke barcinta, wanda rabon da tayi irinsa tun kafin tai arba da karen da ta kora a islamiyyar su, a cikin barcin take mafarkin gata tayi aure tana matuƙar son mijin nata amma wai cikin daji suke rayuwa inda babu mutane ba dabbobi su kaɗaine ke rayuwa a cikin dajin cike da so da ƙaunar juna, sai dai kuma duk sanda take ma mijin nata kullum sai sun zauna sunyi kuka kamar basu dainawa, wani lokacinma har mijin nata na neman suƙewa yana kakkafewa, ta rasa abin da ke sasu kukan nan kuma, suna cikin hakan wata rana taga wani baƙin maciji gabanta zai haɗiye ta, lokacin mijin nata na kwance cikin ɗaki na sana'ar tasa wato kuka, bata san sanda ya fitoba ta dai ganshi tsaye yana huci jikinsa na fidda hayaƙi ya dubi macijin rai ɓace yace "Na rantse da Allah duk wanda ya sake bayyana gaban matata sai nayi ajalinsa! Wata mahaukaciyar dariya ta karaɗe gun kafin muryai mace ta amsa amo cikin faɗa da fusata "Kafi kowa sanin bana ragi bana ragowa bana barin takwana bana ragama ko mai ragamun, balle ita data shiga rayuwarmu kai tsaye ta rabamu, yau zan kasheta na shafe babin rayuwarta a doron duniyar baki ɗaya.
Wane tudu wane gangare kawai ganin mai gidan nata tayi ya koma katon maciji wanda ya ninka wanda yazo da farko girma da tsawo ga tartsatsi na tashi na wuta daga jikinsa. Cike da razana ta fara ja da baya tana rufe bakinta, da ƙyar tasamu ta fara karanto addu'ar neman tsari.
Cikin galabaitar gaske Inna Huraira ta buɗe idanunta waɗanda tsabar kuka yasa sun ƙanƙance kamar me, ta dubi Aljanar dake tsaye gabanta cikin muryai ban tausai tace "Ki taimaka min dan Allah ki rabu dani haka nan, kinfi sauran mugunta, haka kawai kiyi ta wanani kamar kin riƙe kan mota? Ke kam cikin tawagar mugayen kinci lamba guda, kai haba wannan mugunta har ina ni Huraira....bata rufe bakinba taji saukar mari kala daban- daban a kumatunta, ta kuwa dage da sauran ɗan karfin nata ta fara karanto addu'ar mugayen Aljanu kamar haka _"Walmugiratul kyale-kyale, rabbi sakamun da azamatul dundush, karmak nak wak muguwatul aljanatul dundush._
Haka Inna Huraira taita karanto addu'ar neman tsari daga muguwar Aljanar nan da dukkan karfinta tana tofe fuskar Aljanar da uban miyau.
Cikin mamakin jahilcin Hurairai Aljanar ke kallonta, duk da cewar tana daga cikin kidahuman da Yah Malam ke masga duk ƙarshen sati tafi wannan Hurairai sanin ilimin addini ma, akaf yarensu babu irin wannan maganar da take yi da sunan addu'a, da farko ta ɗauka Hurairai ta fara harka da ifiritai harta gyara shiri taga wanda zata kira mata su kwabsa sai ta kula da addu'a ce take yi, ta hanyar tofo uban miyan da take yi akai-akai tana ƙara ƙarfin muryanta.
Halshenta ta fiddo yayi tsawo kamar igiyar shanya, ya naɗe Huraira kamar yanda maciji ke naɗe mutum ga dukkan alama so take ta karya ƙasusuwan Huraira,ai sai Huraira ta ƙara ƙarfin addu'arta, sosai tana ihu, tana wayyo na bani ni Huraira ubanwa yasa na yarda nazo wajen nan?
Cikin matuƙar tsoro take kallon faɗan nasu wanda jikinta ba inda bai rawa addu'arce kawai take iya yi, wani wagegen baki ya bayyana ya jikin macijiyar da tazo kasheta ya fara haɗe mijin nata, aikuwa ta dage ta zabga kabbara mai karfi, wadda ta amsa ɗakin baki ɗaya.
A hankali ta buɗe idanunta ta sauke su kan rufin ɗakin, tana jin yanda zuciyarta ke bugawa da neman zaucewa. Aljanar najin kabbarar Huraira ta fara yamutsa fuska cikin abin da baifi daƙiƙa ba ta zare halshenta tabar ɗakin, kai tsaye gun Major Nasir ta nufa da sigar wata kyakykyawar budurwa mai shegen kyau, sanye cikin ƙananan kaya masu masifar kyau, sai ƙamshi take mai ratsa zuciya da sa nishaɗi.
Bilkisu ta dubi Inna cikin alamar ciwo da maida numfashi tace "Inna ruwa.
Cikin galabaitar dake damun Innar tace "Uban ruwa ba ruwa ba, nace uban ruwa ba ruwa ba kinji ?
Kuka ne ya tahoma Bilkisun tana ƙara gazgata maganar dake yawo a kasan ranta anya kuwa Innar itace ta haifeta ?
Wani munafikin ƙamshi ne ya surnana cikin hancinsa, yaji bai taɓa jin ƙamshin turare mai daɗin ƙamshi irinsa ba, sai ya samu kansa da ɗagowa ganin mai turaren, abin mamaki yanzu ake buga ƙofar alamar turaren ya riga mai shi zuwa inda yake.
Cike da isa yace "Yes come in. Ya maida kansa ƙasa ya lumshe idanunsa kamar mai barci.
Koya zata kaya kenan idan ya ganta ?
Inna Huraira ko itama sai taga likitan ?
Ya gaskiyar mafarkin Bilkisu ?
*Taku ce dai Haupha
managarciya