Jirgin ruwa ya sake kashe mutum shidda, uku sun ɓace a Sokoto
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da ta gabata wanna shi ne karo na biyu a sati daya da lamarin na faruwa cikin kwana shidda.
Aminiya ta gano cewa wadanda suka rasa ransu suna cikin daruruwan Mutanen da ke gudu a kauyukan don neman tseratar da rayuwarsu ga hannun 'yan bindiga.
A bayanin da wani dan garin ya bayar ya ce mutanen kauyukkan suna kwana a dajin da ke kusa da su don kaucewa hari sai su dawo gidajensu da safe.
"Tsoro da mutane ke ciki da yawansu ba su kwana gidajensu sai da safe suke dawowa a lokacin ne wannan jirgin ruwan na katako ya nutse," a cewarsa.
Wani dan garin ya ce an samu matsalar ne a lokacin da mutanen ke ganin 'yan bindigar sun tunkaro su, saurin da suka yi na su tsere ne suka tuntsure a ruwan.
Wasun a cikin gaggawa sun shiga jirgin wasun bai dauke su ba domin baya iya kwashe su gaba daya a kan hanyar dai kuma dai ya fadi.
Dan majalisar dokoki a Sakkwato dake wakiltar Sabon Birni ya tabbatar da faruwar lamarin.
Yana ganin matslar tsaron ta sanya da yawan mutane sun bar gidajensu.
"Wasu garuruwa da yawansu sun zama kufai, da yawan maza suna kwana a daji su dawo gidajensu bayan gari ya waye," a cewar Boza.
Ya ce har yanzu yankin na bukatar karin jami'an tsaro duk da wadanda ke nan suna kokari, a kwanan nan sun tarwatsa wani hari na 'yan bindiga suka kama mutum hudu daga cikin su.
Hukumr bayar da agajin gaggawa ta kasa reshen jiha NEMA ta tabbatar da faruwar lamarin.
Wani babban jami'i a hukumar ya ce sun tseratar da mutane 19 yayin da suke neman mutum uku da suka bace a ruwan
managarciya