Mahara sun kashe mutum 6 tare da sace da dama a Sakkwato
Luguden wutar da sojoji ke wa miyagun a Jihar Zamfara da ke iyaka da yankin Tureta ne ya tilasta musu tserewa, amma suka rika bin kauyuka suna kashe mutane suna garkuwa da wasu, suna harbin wasu
'Yan bindiga dauke da makamai sun kashe mutum shidda bayan sun sace wasu da dama a karamar hukumar Tureta a jihar Sakkwato.
Maharan sun yaudari mutanen garin da yi masu kiran sallar Asubahi suka fito ana takesuka far musu.
Luguden wutar da sojoji ke wa miyagun a Jihar Zamfara da ke iyaka da yankin Tureta ne ya tilasta musu tserewa, amma suka rika bin kauyuka suna kashe mutane suna garkuwa da wasu, suna harbin wasu.
“Bayan mutane sun fara fitowa, sun dauka lokacin sallah ne ya yi, sai kawai maharan suka rika bude musu wuta, suka kashe mutum shida, suka kuma yi awon gaba da wasu.
“Mun kadu kwarai da gaske, wasunmu ma sun fara kaura zuwa wasu wurare,” inji majiyarmu.
Aminiya ta gano cewa akwai mutane da dama kuma da ’yan bindigar suka harba da ke karbar magani a asibitin Tureta.
Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato, Maniru Dan’iya, ya ziyarci yankin domin yi musu ta’aziyya a ranar Alhamis, inda ya jaddada aniyar gwamanin jihar ta ganin bayan ayyukan ’yan bindiga a Jihar Sakkwato.
managarciya