Muhimman Bayanai  Game da Sabon Shugaban Jam’iyyar PDP Na Kasa

Muhimman Bayanai  Game da Sabon Shugaban Jam’iyyar PDP Na Kasa

 

Ba sabon labari ba ne cewa majalisar gudanarwa ta PDP ta nada Umar Iliya Damagum a matsayin sabon shugaban jam’iyya na riko. 

Daily Trust ta fitar da rahoto game da abin da aka sani a kan rayuwa da siyasar Ambasada Umar Iliya Damagum wanda zai rike jam’iyyar PDP. 
Wanene shugaban rikon kwaryar:
  A ranar 10 ga watan Agustan 1963 aka haifi Umar Iliya Damagum, hakan yana nufin a shekarar nan zai cika shekaru 60 a Duniya.
 An haifi Umar Ililya Damagum ne a garin Damagum wanda yanzu haka yana karkashin karamar hukumar Fune a jihar Yobe. 
 ‘Dan siyasar ya yi firamare akauyensa daga 1971 zuwa 1977, daga nan ya tafi Maiduguri a jihar Borno domin yin karatun sakandare.
 A shekarar 2003, Damagum ya sake komawa jami’ar da ke kusa da shi domin yin digirgir, a nan ya samu digirn M. BA na ilmin kasuwanci. 
 A lokacin Gwamnatin Olusegun Obasanjo, ‘dan siyasar ya zama Jakadan Najeriya zuwa Romaniya, ya rike kujerar daga 2004 zuwa 2007. 
 Damagum ya nemi zama Gwamnan jihar Yobe a karkashin PDP a 2019, amma Mai Mala Buni ya doke shi, ‘dan takaran bai je kotu ba. 
 Bayan ya sha kashi a zaben sabon Gwamna, Ambasada Damagum ya fito takarar mataimakin shugaban PDP na kasa, kuma ya yi nasara. 
 Kafin ya zama shugaban jam’iyya na rikon kwarya, Damagum shi ne babba a cikin mataimakan Iyorchi Ayu a NWC, yana wakiltar Arewa.