Hukumar Zaɓe Ta Ƙasa Ta Fitar Da Sanarwar Ranakkun Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A 2023 

Hukumar Zaɓe Ta Ƙasa Ta Fitar Da Sanarwar Ranakkun Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A 2023 
Hukumar Zaɓe Ta Ƙasa Ta Fitar Da Sanarwar Ranakkun Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A 2023 
Daga Babangida Bisallah
Hukumar zaɓe ta ƙasa ta bayyana cewar babban zaɓen shekarar 2023 zai kasance ranar 18 ga watan Fabrairu ga shugaban kasa da mataimakinsa,  dana 'yan majalisar wakilai da dattijai waton sanatoci duk a rana ɗaya.
Sanarwar ta cigaba da cewar zaɓen gwamnoni da 'yan majalisar dokoki na jahohi zai kasance ranar 4 ga watan Maris na shekarar 2023.
Wadanda suka samu nasara kuma za a rantsar da su ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Siyasa 2023 ta fara tun yanzu in da kowane ɗan siyasa ke ƙoƙarin samun mafita.