Masallacin Jumu'a ya yi Sallar Jana'iza Ga Sarkin Gobir a Sakkwato 

Masallacin Jumu'a ya yi Sallar Jana'iza Ga Sarkin Gobir a Sakkwato 

             

Daga Mukhtar A Haliru Tambuwal Sokoto.

 Masallacin Jimua na Sahaba da ke a Sakkwato sun gabatar da Sallar Ga'ib bayan Kisan Gillar   da aka yi wa Uban kasar Sabon Birnin Gobir.

jinkadan da Kammala Sallar Jumu'a wadda Dakta Usman Riba Mataimakin Kwamandan Hisba na Jihar Sokoto ya jagoranta, ta samu halartar dimbin jama'a.

 Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto mni, Wanda shi ne Shugaban Cibiyar Da'awa ta Ahlil baiti da Sahaba ya bada Umurnin yin Sallah inda ya bayyana ya halatta a yi musamman Duba da yadda akayi Kisan.

Limamin ya yi kira ga Alummah Musulmi Hausawa da Fulani da su shiga taitaiyim su kar su yarda makiya suyi Nasarar cimma Burin su na hada fada tsakanin Musulmi Hausa da Fulani. Limamin yayi kira ga Gwamnati da Masarauta da sauran Alummah da a ƙara kokarin ganin anshawo kan matsalar tsaro.

Yayi Ta'aziyyar ga Alumma Musulmin kan Wannan Rashin da Addu'ar Allah ya karbi Shahadar shi.