KOTU TA DAURA AUREN WASU MASOYA A JIGAWA DUK DA MAHAIFIN AMARYA YAKI AMINCEWA
By Amina Abdullahi Girbo.
Daga Kotun Shari'ar musulunci dake zama a Garun Gabas, Dake ƙaramar hukumar Malam Madorin Jahar Jigawa, Karkashin Jagorancin Mai Shari'a Mallam Muhammadu Yaba Ibrahim, Kotun Ce Ta daura Auren wasu masoya.
Kotun Ta Daura Auren ne, bayan mahaifin amarya ya ki amincewa da auren a mintunan karshe, sakamakon bincike da ya bayyana cewa angon ba mabiyin mazahabar da ya aminta da ita bane.
Tun da fari dai mahaifin yarinya Mallam Muhammadu Sabiu Mallam Madori ya sanya ranar Asabar 16 ga watan Disamba domin daurin auren.
Wannan yasa ango ya saki jiki har ya aike da lefe tare da cika dukkan sharuda Na Al'ada, kwatsam sai sanarwar soke auren ta bujiro daga mahaifin Amarya.
Wannan mataki da Mallam Sabiu ya dauka ya taba zuciyar gidan Angon dama dangin mahaifiyar yarinyar.
Bayanan Dai sun nuna cewa Amaryar da ake wannan takaddama akanta ta taso ne a hannun dangin mahaifiyarta tun bayan rasuwar mahaifiyar tata.
Fatima sun kwashe kusan watanni 14 suna soyayya da Haruna Sani Garun Gabas.
Wannan yasa yar uwar mahaifiyar Fatima shigar da korafi a Gaban Kotun, Wanda bayan nazarta da saurarar dukkan Bangarorin, Alkalin Kotun Ustaz Muhammadu Yaba Ibrahim yayi tawassali da hujjoji daga Alqurani da shari'ar musulunci ya daura auren.
Kuma bayan daurin auren ne angon Haruna Sani ya tabbatarwa Da Cewa"Da Yardar Allah zai rike Amarya da amana dai-dai gwargwago, kuma wannan kaddarar ce zata iya faruwa da kowa".
Haka mahaifin Angon ya bayyana cewa zasu tabbatar wannan sabani bai zama silar taba zumuncin Fatima da mahaifinta ba.
managarciya