'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Biyu Sun Sace 13 A Sakkwato

 'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Biyu Sun Sace 13 A Sakkwato

 


'Yan bindiga dauke da manyan makamai sun kashe mutum biyu sun yi garkuwa da 13 a yankin Mammansuka a karamar hukumar Gwadabawa ta jihar Sakkwato. 

Maharan sun zo da yawan gaske a kauyen su ci karensu ba babbaka in da suka tafi mata 11 da namiji biyu a cikin harin ta'addaci da suka kawo a satin da yagabata.
Shugaban karamar hukumar Gwadabawa Alhaji Aminu Aya ya tabbatar da harin ya ce bayan mutanen da suka kashe suka yi garkuwa da 13 sun tafi da dabbobi da wayoyin hannu da dukiyoyin  mutanen yanki.
Shugaban ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa su kawo dauki ga mutanen karamar hukumarsa ganin aikin ta'addanci ya zama abin da ake yi kullum.
Ya ce akwai bukatar a yi kokari a kwato mutanen da aka yi garkuwa da su cikin koshin lafiya dsu dawo cikin iyalansu.