Labari da rubutawa
*Hauwa'u Salisu (Haupha)*
Page 2
Gaje ga dukkan alama ita ma ta shiga tararrabin da nake ciki, domin na lura ta kasa magana sai kallon Binta kawai take idanuwa waje, zuwa can ta nisa tace, "Lallai Jiddah akwai matsala ban ji miji ba, mijinki bai da hali sam, Allah Ya shirya shi Yasa ya gane gaskiya." Daga haka ta miƙe tsaye ta kakkaɓe zaninta tace, "Ni na tafi Jiddah ki saka haƙuri a rayuwarki, shi aure ya gaji hakan watarana baƙi, watarana fari, to ke yau baƙin ce ta zo maki don haka ki danne zuciyarki ki natsu ki yi haƙuri komai ya wuce Jiddah, an san babu daɗi kam amma haƙuri ya zama dole gareki yanzu, sai ki san zaman da kike da Safiya yanzu, amma ban da fitina bata da amfani sam." Binta ta amshe maganar itama tace, "Ai mun ɗauka ta san abin da yake tuni ashe bata sani ba, amma don Allah maganar ta tsaya iyakar mu nan, kada ace na zama munafuka don Allah." Ni dai ban ce ƙala ba har Gaje ta fice daga gidan, Binta ta gyara zama tace, "Jiddah maganar gaskiya idan baki nan mijinki matan banza yake kawowa a cikin gidan nan, unguwar nan kowa yasan hakan faɗa ne dai ba a yi gabanki amma ana ta gulmar yadda kike tafiya yawo kina barin gidan yana kawo mata ciki, idan yana da laifi ke ma kina da shi, me yasa kike zuwa yawo bayan kina da aure me kike tsinta a yawon Jiddah?" Har zuwa yanzu ban da bakin yi mata magana domin baki ɗaya ta ƙara min nauyin zuciya da duhun kai tare da jefa min wani tunanin na daban a raina wanda lissafin yafi ƙarfin sauran natsuwa ta, don haka na ja jikina na kwanta idanuna a rufe hawaye na tsiyaya. Tabbas aure na cike da tashin hankali da ƙalubale kala-kala wanda zai iya kai mutum ga ajalinsa bai fargaba. Binta ganin ban da bakin magana ta tashi ta fice cike da sanyin jiki ko ban tambaya ba nasan tana jin tausayina ne na kasancewarta maƙwabciyar da nake kulawa fiye da sauran maƙwabtana.
Bayan fitar Binta na buɗe idona da ƙyar dake ta azabar zafi ga kaina na sarawa kamar zai tsare gida biyu, amma ƙoƙari nake na gano waye ke da matsala a cikin mu ukun nan? Nice ko ƙawata Safiya? Koko shi mijin nawa ne mai matsalar? ("Duk sadda baki nan yana kawo matan banza a cikin gidan nan.") Maganar Binta ke ta yawo a cikin kunnena, kenan ma ba ƙawata bace kawai yake kawowa ba gidan? Wace irin baƙar rayuwa ce wannan nake yi? Dama haka auren yake?" Kuka nake sosai tamkar an gayamin rasuwar mahaifiyata saboda tsabar baƙin ciki da nake ciki yasa na manta cikin jikina na tashi da sauri na sanya hijabi na fice ban tsaya ko'ina ba sai gidanmu, Mamarmu na ganina ta saka Salati tana tambayata ko ban lafiya. To ai dole tai min wannan tambayar yadda ta ga na koma lokaci guda dole ai zaton ban cikin hayyacina, sai dai lafiyata lau, lafiyar zuciya ce kawai ban da ita, sai uwa uba natsuwa itama tai min ban kwana tun bayan da idanuna suka sauka kan baƙin ganin da nayi a cikin gidana, cikin ɗakina tare da mijina da ƙawata. Shigewa ɗaki nayi na haye kan gado na kwanta hawayen har zuwa yanzu basu daina tsiyaya ba, haka na kasa daina ganin abin a cikin idanuna.
Sallamar Mamarmu naji ta shigo ɗakin amma ko ɗaga kaina ban yi ba, sai a lokacin nake jin nayi wautar zuwa gunta, to me zance mata? Ba zan taɓa iya gaya mata abin da ke damuna ba, domin hakan zai dameta kamar yadda ya dameni, zata riƙe abin a ranta ya hanata walwala kamar yadda ya hanani, idan na bari hakan ta faru na sake tsoma kaina ga tashin hankali, gwara na zauna a damuwa da mahaifiyata ta kasance cikin damuwa, don haka na yi ƙoƙarin share hawayena na rufe idanuna alamar barci nake. Ina ganinta ta jima tsaye kaina da alamar damuwa fal a fuskarta, amma ganin kamar barci nake yasa ta zauna ta tasani gaba da kallo tana ajiyar zuciya, ta daɗe a hakan zuwa can kuma ta tashi ta fice daga ɗakin, ta ɗan jima ta dawo duk ina kallon abin da take sam bata cikin natsuwa don har ɗan yin jim take irin na tunanin nan, sai tace "Allah Ya sawaƙe." Jin ƙamshin kunun kanwa yasa na fahimci shi ne ta dama min, da yake duk ranar da na zo yini gidan takan dama min shi sosai na yini sha. Duk yadda nake son kunun kanwa da uwar yunwar dana kwaso sai naji ban son shi, asalima babu yunwa a tare da ni. "Yayarsu tashi ki sha kunun kanwa da zafinsa kar ya huce." Nayi bulum ban motsa ba, haka ban ce komai ba, don har ga Allah babu inda zan saka kunu a cikin wannan mugun yanayin da nake ciki. Sai da ta taɓa ni sannan na buɗe idanuna, hawayen da nake ta ɓoyewa suka zubo min, ni da ita mu kai jim ba mai magana, zuwa can tace min, "Ina mijin naki?" Na fahimce ta so take ta ji ko faɗa mu kai da shi don haka nace cikin muryar kuka "Bai nan." Tai ajiyar zuciya tace, "Kin shigo cikin tashin hankali kin ƙi gayamin abin da ke damunki shin ya kike so inyi maki ne?" Kamar tace ci-gaba da kuka haka naji kawai na ci-gaba da raira kukana mai taɓa zuciya, ina jin yadda ɗan cikin cikina ke wutsilniya kamar zai fito waje, amma nayi kamar ban jin shi domin ba tashi nake yi ba ta matuƙar tashin hankalin da nake ciki wanda ubanshi ne ya ja zamin halin da nake ciki. Mamarmu ta zauna sosai kusa da Ni, "Ki gayamin gaskiyar abin da ke damunki domin kin saka ni cikin tashin hankali, sai kuka kike kin ƙi gayamin abin da ke faruwa ya kike so nayi maki ne? Idan faɗa ku kai ki gayamin abin da ya haɗa ku ina jinki." Na ɗago kaina ina kallon mahaifiyata ina jin a raina shin in gaya mata gaskiya koko in yi shiru?
Shin Jiddah zata gaya ma mahaifiyarta abin da ke faruwa koko?
Ina mijin Jiddah ya tafi bai dawo ba?
Da wasu amsoshin ma duk ku biyo Haupha dan jin yadda zata kasance.