GOSHI: Fita Ta Biyu

GOSHI: Fita Ta Biyu

GOSHI
      


*_MALLAKAR_*
*_Umma Yakubu Imam(Maman Dr)_*


P-2


Baki a wangale malamar ta ce, "Iyeeee, wato ke rashin mutuncin naki har ya yi shurar da za ki hauro ta cikin wundo ba ma ki biyo ta ƙofa ba ki shigo aji ba ko? To zo nan don gwafar ubanki laifi biyu kika yi ga makara ga kuma haurowa ta cikin wundo, ko da yake bari in karɓo bulala abin da kika guda a bakin ƙofar makarantar dai shi kika zo kika tarar yanzu acikin ajin.
 Kafin yarinyar ta ƙaraso wajen malamar ta nufi ƙofar fita daga cikin ajin. Inda ta ja dunga ta tsaya daga bakin ƙofa haɗe da leƙawa waje. Umartar wani malami malamar ta yi da ya bata aron bulalar hanunsa yanzu za ta dawo mai da ita, ya ko bayar aka kawo wa malamar bulala ta juyo cikin aji sai dai ba ta yi ido huɗu da yarinyar ba dalilin da ya sa malamar ta ce.

"Kambala'i! Ina Hauwa Baffa take?

Malamar ta furta tana dube-dube ko za ta yi ido huɗe da yarinyar acikin ɗalibai wacce ta kira da sunan Hauwa Baffa. Ajin ne ya sake yin tsit tamkar ruwa ya shanye su, malamar ta kuma jero tabayar da ta musu a farko, wadda aka rasa wacce za ta buɗe baki a cikin ajin ta faɗi inda Hauwa Baffa take. Lura da yanayin ɗaliban ajin malamar ta sake buɗe baki ta ce,"

"Wai badaku nake magana ba? Ina Goshi idan kun ƙi amsa Hauwa Baffa ta shiga? 
Nan ma dai sammakal an aika bawa garinsu, ba wanda ya tankawa malamar, wani malami ya zo giftawa ta jikin ajin malamar ta yi saurin kwaɗa masa kira da cewa,"

"Malam Bukar... 

"Na'am! Malama Sadiya." Malamin ya amsa tare da faɗowa cikin ajin da bulala a hannu sai baɗa hanci yake tare da zare ido. Malama Sadiya na cigaba da cewa," Ka ga ɗalibanka wai ni za su nunawa haɗin kai, yarinyar nan Goshi ina tsaka da rubutu a allo ta hauro ta cikin wundo daga leƙawa karɓar bulala a hannun malam Shamsu ka ga ta yi ɓatan dabo acikin ajin nan kuma an rasa wanda zai faɗi inda ta ɓuya na san tana cikin ajin nan wallahi.

 "Abin nema ya samu malama Sadiya bar ni da su in dai ƴan ajin nan ne za su aikata abin da ya fi haka akan Hauwa Baffa tsoronta suke yi kamar uwar da ta tsuguna ta haifesu, to amma bari jikinsu ya fara gaya musu tukunna zaki ji zuwan da dawowar.
Faka-faka malam Bukar ya shiga jibgar ɗaliban ajin na gaba, malamar ma ta fara jibgar na gabanta ba a ɗauki dogon lokaci ba wata daga cikin ɗaliban ta ce,"

"Zan faɗa, zan faɗi inda ta shiga malam...

"Maza ki faɗa min inda Hauwa Baffa ta shiga? Malam Bukar ya jefawa yarinyar da ta yi magana tambaya, cikin sauri yarinyar ta ce

 "Tana cikin nan... Yarinyar ta nuna wani ɗan ƙaramin ɗaki da ke ƙarshen ajin ba kowa ke shiga ba saboda duhun masifar da ɗakin ke da shi acewar ɗaliban ajin wai ɗakin ƳAR MADOBO ne. Malam Bukar ya danna ciki kai-tsaye bayan ya kunna fitilar hannunsa da ke jikin wayarsa, ba tsoro Goshi ta fito daga cikin ɗakin jin dirfafowar malam Bukar ya danƙo hijabinta suka dawo gaban aji tare da ɗaga bulalar hannunsa zai zambaɗa mata ta ce,"

"Kar ka doke ni malam Bukar. 

"Idan na dake ki zaki rama ne?

"A'a, amma dai kar ka sake ka doke ni malama ki hana malam Bukar dukana...kafin ma Goshi ta ɓame baki tuni malam Bukar ya kawo mata duka, inda ta yi wata katantanwa sai ganota aka yi burum acikin zanin malama Sadiya ta shige ban da Allah ya sa malamar ta dafe allon bangon ajin da tuni ta kefe ƙasa ɗalibai suka tuntsire da dariya.
Tsawa me ƙarfi malam Bukar ya dokawa ɗaliban aji kowa ya tsuke bakinsa kafin ya dawo kan Goshi da ke cikin zanin malama Sadiya yana kai mata dukan da take kaucewa, ya yin da bulalar ke sauka ajikin ƙafar malama Sadiya da ta furta,
"A'aaa! Malam Bukar tsaya wallahi ni kake zumbuɗawa bulalar nan, ba yarinyar nan kake samu ba. Jin furucin malama Sadiya da malam Bukar ya yi, ya sa ya tsaya da kaiwa Goshi duka yana rantsuwa idan har ya zaro ta daga cikin zanin malama Sadiya na lahira sai ya fita jin daɗi don haka gwara ta fito ya jibgeta tun da wuri ta huta.
 Batun malam Bukar kamar ƙarawa goshi ƙaimin ruƙunƙume ƙafafuwan malam Sadiya tamau ya yi acikin zanin domin ko motsin kirki malama Sadiya ba ta iya yi gudun faɗuwa agaban ƴan aji sai ma hannu da ta saka ta tare cinyoyinta.
Abu kamar wasa, ƙaramar magana ta zama babba! Ajin ya cika da malamai mata da maza fal, juyin duniya goshi ta fito daga cikin zanin malama sadiya taƙi, malamai mata suka ce malamai maza su fita  har ɗaliban aka koro su waje aka rufe ajin daga malama sadiya sai sauran ƴan uwanta malamai mata sai kuma goshi da ke cikin zanin malama Sadiya. Malama sadiya ce ta zare mayafin jikinta a cewar malamai mata ta cire mayafi da zanin duk tsiyar Goshi sai ta zo hannu, tare da miƙawa malamai mata da suka zagayeta.
 Bayan ta zare mayafi ta fara ƙoƙarin kwance zanin jikinta a hankali har ta fara cirosh goshi na riƙe dashi gam malamai mata suka yi mata rufdugu suna janyeta wasu na janye zanin malama Sadiya wuf ta saki zanin malama Sadiya ya yin da ta faɗa cikin zumbulelen hijabin malama Ummi.

Dawa Allah ya haɗa malama Ummi ta fara kaiwa Goshi duka ta ko'ina, Goshi na kai mata yakushi da cizo acikin hijabin nata sauran malamai suka komo kan malama Ummi ya yin da malama Sadiya ta ɗaura zaninta a juye mayafi a hannu ta yo waje malamai maza na tambayar yanda aka haihu a ragaya.
Lamari ya yi zafi, inda aka cigaba da ɗauki ba dad'i da malamai mata da goshi acikin aji har Allah ya basu sa ar cakumota suka taso ƙeyarta gaba zuwa waje gaban malamai maza da mata, gaban ɗalibai don lokacin har an fito da su cin abincin biraik sun yi carko-carko ganin goshi a hannun malama Baraka. 

A gaban ɗalibai malam Bukar ya zane goshi ciki da bai, ya baiwa malama Sadiya bulala taƙi dukanta sai malama Baraka da malama Ummi ne suka ƙara mata akan dukan da malam Bukar ya yi mata. Wanda ko ƙwalla ba ta fitar ba ballantana ruwan hawaye dalilin da ya kuma saka malam Bukar sake tisa dukan goshi da ya yi a karo na biyu ya kuma ce sai ta tsince ledojin makarantar gabaɗaya. Goshi ba ta yi gardama ba ta bi tana tsince ledojin kamar yadda malam Bukar ya umarceta har aka koma a ji ita ma ta shiga ajin ya yi tsit kamar malamai na ciki. Wajen zamanta ta nufa, tare da cewa, "Wace mai gangancin ce ta faɗi inda na shiga?

"Ga ni nan, ni na faɗa don ba za ki ja mana duka muna zaman-zamanmu ba.

"Jan duka ko Bilkisa? Cewar Goshi, Bilkisa ta ce, "Bilkisu nake don haka kar ki sake ce mini Bilkisa wallahi zan je na faɗawa malam Bukar ya ƙara miki dukan da ya yi miki. "Idan kin fasa zuwa faɗa masa ba ki haifu ba Bilkisa ki ce ya kashe ni kar ya bar ni da rai kuma na fad'a Bilkisa, Bilkisa... Kan ka ce me Bilkisu ta yo waje da gudu ta nufi wajen malamai maza. Ƙorafi ta shigar na cewa, "Malam Bukar ka ga Goshi daga dawowarta aji ta fara zagina wai sai ta lakaɗa mini dukan tsiya, ta kuma kara da ce min Bilkisa a gaban ƴan aji salon su fara tsokanata da Bilkisa. Taso ƙeyar Bilkisu malam Bukar ya yi a gaba suka nufo aji kamar yadda ya saba yanzu ma sai da ya yi wa Goshi bulala goma a hannu biyar ƙafarta ma biyar idan ta ɗauke ta zube akan Bilkisu ya kuma shiga tsakaninsu ko kallon banza Goshi ta yi wa Bilkisu ta zo ta faɗa masa sai ya canjawa Goshi kamanni. Fitar malam Bukar ke da wuya ajin kowa ya ɗauko jakarsa ɗaya-bayan-ɗaya suka dinga kawowa Goshi abin da suka siya suka rage mata kasonta kamar kullum. In da Fati ƙawar Goshi ke cewa, 
"Kin san yau me amaryar babanmu ta dafa mana kuwa? "A'a, goshi ta ce, Fati ta cigaba da cewa, "Dankali da ƙwai, kin ga ma na rago miki naki da na yi biraik ba kya nan Goshi. Karɓa goshi ta yi, ta juya dankali da ƙwan da Fati ta bata a hannu tare da cewa, 

"Ni ma fa babanmu ya kusa yo mana amarya Fati ki taya ni murna har fati zan yi. "Da gaske kike Goshi? Cewar Fati cikin mamaki, goshi ta cigaba da cewa, "Wallahi kin san ma wace ce amaryar? "A'a sai kin faɗa mini goshi. "To uwani tifar yashi ce kafin na zo makarantar ma sai da na biya na gaishe da Innar ta har na kai mata silifas ɗan-madina da omo da goro kuma da zan fito na tsokaneta a guje ta biyoni da lukutayen cinyoyinta tana taɓar-taɓar kamar ɓaunar daji. Dariya su biyun suka kwashe gabaɗaya kamar ba a jibgi goshi a ranar ba ta cigaba da safgarta, duk lokacin da suka yi ido huɗu da Bilkisu sai ta sakarwa Bilkisu dariya, Bilkisu kuwa har wani nunawa ƙawayenta take wai Goshi tsoronta take ji yanzu har aka buga ƙararrawar tashi daga makaranta kowa ya nufi hanyar gidansu.

Cike da zumuɗin shiga kwanar gida Bilkisu ta taho daidai lokacin Goshi ta shawo gabanta hannayenta biyu a dunƙule, ya yin da ta turowa Biliksu su tana cewa,

"Ga ta tsiya, ga ta arziƙi idan kin isa ki ɓare ta tsiya ki sha bugun tsiya ƴar matsiyata! Tankaɗe hannuwan Goshi guda biyu Bikisu ta yi cikin fushi ganin ta zo gida babu abin da Goshi ta isa ta yi mata. Cikin ba za ta kuwa Goshi ta kaiwa Bilkisu wani daƙiƙin naushi abaki tare da hamɓareta ƙasa ta faɗa kan ruwan cikinta cikin zafin nama Goshi ta shiga kai mata mahanguruɓa, naushi, mari da su yakushi tamkar mage ta Yi arangama da ɓera. Tsabar kiɗimewa kasa kuka Bilkisu ta yi, ta kasa kare kanta bare ta rama, ita ko Goshi har ƙasa ta dumbuzo tare da murje bakin Bilkisu tamkar yadda ake murje masar tana mai cewa,

"Kin ga yanzu sai ki faɗawa ƙanin ubanki malam Bukar da hujja na yi miki dukan tsiyar da kika yi min sharri, shegiya Baƙar munafuka algunguma. 


@Real Maman Dr
(2025)