LISSAFIN KADDARA: Fita Ta 7&8

LISSAFIN KADDARA
*LISSAFIN KADDARA*
*ZAINAB SULAIMAN*
(Autar Baba)
Not edited
DEDICATED TO SHAMSIYYA USMAN MANGA
Page: 7&8
Karan fasa gilashin da ya ziyarci kunnuwansu ne yasa kowa ya juya a hanzarce don baiwa idosa abinci, Alhaji sama'ila kuwa tuni ya rude domin sanadiyar wurgo da tabarya da yayi ne gilashin motar da tazo wucewa ya fashe,tuni kallo ya koma sama domin masu cewa Allah ya kara sunfi yawa akan masu Allah ya kiyaye shiru da kusan minti biyu ba'a fito a motar ba sai dai kowa attention dinsa naga motar da kuma son ganin hukuncin da mai motar zai dauka akan Alhaji Sama'ila ita dai Ameenatuh tana rike da Khadija suna sharbar kuka Umma kuwa tashi tayi ta samo yana tazo ta lika a goshin Khadija da jini yaki tsayawa,
A hankali aka bude motar,kafar macece ta fito daga bisani ta fito gaba daya fuskarta dauke da tabarau irin na likitocin nan kallon banza ta watsawa Alhaji Sama'ila a hankali cikin tafiyar kasaita da gayu ta zagayo har inda yake tana masa kallon up and down kafin cike da nutsuwa ta maida kallonta kansu Ameenatuh daidai lokacin kuma sukaji karar horn din mota a bayansu cire tabaran tayi ta fuskanci Alhaji Sama'ila ta watsa masa key din motar kafin cikin nutsuwa tace" bana daukar asara a gurin wanda baisan mutunci da darajar dan Adam ba dan haka ka tabbatar kafin nan da ƙarfe hudu ka biyani barnar da kayi mun"daga haka ta juya inda Ameenatuh ke durƙushe tare da Umma abun duniya ya ishe su tace"in kuna bukatar taimako zaku iya biyoni na fuskanci kuna cikin damuwa, kuzo muje gidana kafun dare muga abunda za'a yi"tana gama fada ta kama kafadar Khadija ta tasheta tsaye Umma da Ameenatuh suka rufa mata baya suka shiga motar ba tareda shayi ko dar ba dan a ganinsu ba daren da jemage bai gani ba,'yan unguwa kuwa ba karamin jin dadin hukuncin da akayiwa Alhaji Sama'ila sukayi ba sakamokon kowa yasan halinsa batason zaman lafiya shi kullum cikin tozarta masu zama a gidanjensa matsayin haya yake ba'a cikakken wata baiyi watsi da kayan wasu ba,
Motar bata tsaya ko ina ba sai get din wani makeken gida dake unguwar Rigiyar Zaki jahar Kanon dabo tun daga waje zaka gane gidan ya tsaru iya tsaru take gaban Umma ya tsananta faduwa bawai dan tana jin tsoro ba kawai dai haka ta tsinci kanta tunda suka shigo unguwar Ameenatuh kuwa baki ta bude alamu mamaki dan ita tunda take a zahiri bata taba ganin gida haka ba gida ne mai part biyu kuma akwai tazara sosai tsakaninsu kuma da alamun duk iri daya ne,basu gama shan mamaki ba sai da suka shiga part din farkon nan ido yasamu abincinsa dan tuni kallo ya koma sama, masauki tayi musu cikin hanzari matar ta barsu a falo ta shiga daki bayan ta dauki excuse bata wani jimaba ta fito hannun ta dauke da first aid box cike da kwarewa ta kamo Khadija tana yi mata sannu haka ta fara wanke mata ciwon goshinta har ta gama sannan ta haɗa kayan ta mayar ɗaki ta fito ta samesu inda ta barsu fuskarta dauke da fara'a tace"Sannunku kunzo bakon guri batare da cikakken bayani ba,karku damu Sunana Firdausi amma dai Nana ake cemun daga ni sai mai gidana anan, dayan part din kuma na iyayenmu ne wato mahaifan mai gidan nan da Ɗanmu daya, da ma kuma dalilin fita ta zanje ganin wasu ne da nake sa ran zasu faramun aiki to banaso sai ankawosu nace basumun ba saboda banason kazanta kuma a hanyata ta zuwa Allah yayi sanadin haduwata da ku,ya kukaga zaku mana aiki muna biyanku ko kuma taimako kawai kukeso"a jiyar zuciya Umma ta sauke dan ita dai tunda ta shigo gidan nan nutsuwarta ta bar jikinta haka kurum taji gabanta na faduwa a hankali ta kalli Nana tace"haba baiwar Allah wanne taimako zaki mana da ya wuce wannan,abunda mun dade muna nema bamu samu ba mun amince Ubangiji ya bamu ikon rike amana" ita dai Ameenatuh rungume take da Khadija tana faman shafa mata baya har bacci ya fara daukarta "to ameen ya Allah,amma dake part biyu ne sai daya ta koma wancan part din tana masu aikin sannan zamuna biyan ku every month in sha Allah,yanzu kuzo muje ku huta anjima sai in raka wacce zata nayiwa su Mama aiki"murmushi sukayi gaba daya suka tashi kamar yadda suka ga tayi Ameenatuh riƙe da kafaɗar Khadija dake mayen bacci,tayi gaba suna bin ta a baya tana dan jansu da hira har suka karasa masaukin da aka tanadarwa masu aiki,bayan ta gama nuna musu ta fito ta basu guri dan su huta kafin yamma,
Sai ƙarfe uku suka tashi a bacci su duka,alwala sukayi suka gabatar da sallah azhr suna idarwa Ameenatuh ta janyo ledar maganinta da duk bala'i baisa ta zubar da su ba ta ɓallawa Khadija ta bata tasha da ruwan pure water da suka samu a dakin,tana gama sha suka fita dan fara aiki,
A falo suka same ta tana zaune kafa daya kan daya tana waya dan haka daga nesa suka tsaya harta gama ta yafitosu da hannu suka ƙarasa tare da durƙusawa a kasan carpet,kallon Khadija tayi tace"ke kam ai aiki ba yanzu ba sai kin samu sauki"ta maida dubanta ga Ameenatuh tace"ke kuma ina ga ke zakije gurinsu Mama kamar sai kinfi sister ki kwari"kai kawai Ameenatuh da gyada kafun Nana tayi musu nuni da hannu zuwa wani dan lungu tace"ki shiga ki dauko muku abincinku a kitchen akwai tea flasks da tea a ciki ki dauko muku nasan zuwa yanzu dole kuji yunwa"tashi tayi tabi hanyar da ta nuna mata aranta tana cewa "yo ni na manta ma yau bamu ci abinci ba,Allah sarki nasan zamu samu munacin abinci kullum,ai mu ko ba'a bamu kudi ba zamu zauna ga muhalli mai kyau ga kuma abinci"ALHAMDULILLAH ta fura a fili lokacin da take karasawa kitchen din,.
Yau kimanin sati biyu sunayiwa Hajiya Nana aiki Umma da Khadija sune a bangarenta ita kuma Ameenatuh tana bangaren Mama kuma kullum sai taje sun gaisa da Umma da safe haka da dare saboda ba wani aiki ne mai yawa a bangaren Maman ba sai dai ko ina ita take gyarawa kuma tayi girki,tuni sukayi kyau suka murje a bangaren Khadija kuwa tuni Hajiya Nana ta dorata a kan magani sosai kuma take samun sauƙi dan da ɗan jima batayi ciwon cikin b wanda dama Ulcer ce ta da typoid duka taba mata kayan cikinta sai kuma tari da ta gamu da shi a company ƙaro,
kamar kullum yau ma suna zaune suna hira dan sun gama aikinsu Ammeenatuh takalli Mama tace "Umma dama inaso na tambaye wallahi kullum sai na sha'afa"gyara zama tayi cike da fara'a tace "yi tambayarki yau tunda Allah ya baki iko"itama murmushi tayi tace"wai Umma ba wanda kika sa ni a dangi Abbanmu?"sai da ta danyi jum kafin tace"na san tsiraru amma tun lokacin yana tare da mu suka barmu saboda sun ɗan samu saɓani da ɗan uwansu to shafinsa ne ya shafemu kuma ƙarshe m a bayan mun nemesa bamu samu bama muka tuntuɓesu,to dai ma ƙarshe abun ba daɗin ji"ta ƙarasa maganar tana kuka,cikin kiɗima Khadija ta dafa kafaɗar Umman yayin da Ameenatuh ma ta rikice "dan Allah Umma kiyi haƙuri bansan ranki zai ɓaci da tambayar ba""ba komai Ameenatuh ba ke nake yiwa kuka ba kawai ya dace nayi kuka na ƙara har sai kai na yayi ciwo,Ameenatuh bana muku fatan bin ruɗin zuciya,ban muku fatan samun miji mai makamanci halin mahaifinku,Ameenatuh da ace damuwa tana illatarwa da tuni ba zance akeba na zaɓi zabina nabar zaɓin Allah sai gashi Allah ya nunamin tun a duniya shifa ba'a mishi wayo"ga ɗaya suka rungumeta suna sa kuka mai cin rai,sun jima a haka hayaniyar da suka jiyo a farfajiyar gidance tasa suka fita gaba daya ganin mai gadin gidan da Ɗan su dake ɓangaren kakanninsa acan gefe kuma wani mutum ne da kallo daya zaka masa kayi tunanin mahaukaci ne sai hayaniya yake akan sai anbarshi ya shigo gidan,mai gidan ne ya fito shima wanda tunda suka zo gidan baya nan sai jiya da dare ya dawo"mai ya faru ne haka nake jin hayaniya,ganin ba abunda ya shafesu bane yasa suka juya da nufin komawa ciki aikuwa kunnuwansu ya jiyo musu cikin ƙaraji"Maryama!!" a firgice Umma ta juyo jiyo muryar da bazata taɓa mantawa da ita ba duk jimawar da tayi ba tare da tajita ba.,
Na gaji da typing ba tareda naje inda nakeson tsayawa ba,
In dai kunyi sharhi mai kyau zuwa gobe zan saki 9&10 saboda acan rikicin yake,
Kuna karanta lissafin kaddara amma bakwa son yimin comment basan dalili ba kuma sai kunji shiru ku biyoni private kuna neman ci gaba,
Zancen gaskiya in banga comment daga wannan page din zuwa na gaba ba zan daina posting sai ta pc, in na baki kema kimin sharhi a pc din.