ANA BARIN HALAL....: Fita Ta 32

ANA BARIN HALAL....: Fita Ta 32

ANA BARIN HALAL....: Fita Ta 32

*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE* 

*®️GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_(Gaskiya Dokin Ƙarfe.Burin Mu Faɗakar Da Al’umma Domin Ribatar Duniya Da Lahira.)_

*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*

Idan kana/kina sha’awar:

_**Updates akan tallafin gwamnati (Grant & Loan)._

_**Hanyoyin samun kuɗi ta kasuwanci na online._

_**Sana’ar hannu da za ki iya yi daga gida._

_**Dabarun amfani da waya wajen samun kuɗi._

_To wannan group ɗin na Business/Grant/Loan naku ne! Zaku samu labarai kai tsaye + shawarwari masu amfani in sha Allah._
Join yanzu don kada ku rasa sabbin damarmaki*
https://chat.whatsapp.com/C64wC3IDhW6FtwjSpWWDiL?mode=ac_t

*INA UWARGIDAYEN SUKE? NACE INA UWARGIDAYE MASU CAPACITY SUKE, IDAN BAKI YI MATSA GA MASU* *AUTHOURITY, NACE TSAYA IDAN BAKIYI GA AMARE MASU AUTHOURITY,* *IDAN KIN SHIRYAH GWANGWAJE SHINFIƊAR MAIGIDA,* *TOU KI ƘYALE  ƳAN LOCALLITY KI MATSO KI SAYI NAKI,* *BEDSHEETS ƳAN GASKE, KU MATSO KU YAƘI PORVERTY DAGA TASKAR HALIMA YISUF GWARZO, INA MAI TABBATAR MIKI IDAN KIN SHIMFIƊA ZAKI ZAMA MAI CAPACITY MAI AUTHOURITY,* *DOMIN KI WANKE ZUCIYAR MAIGIDA YA HASKAKA,*
*MUNA AIKAWA DA SHI KO'INA A FAƊIN ƘASAR NAN.*
*DOMIN SAYEN ƊAYA KO SARI, KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAMBAR*
08064586559


*PAGE*  32


**********
Da ƙyar M.G ya shawo kaina muka fara gaisawa da shi ta waya, don sai da yace mun,   "Aysha kada kiji haushi na don Allah, son da nake yiwa A.G zan iya mishi komai, kuma abunda na fahimta son da yake miki yafi ƙarfin wanda ni nake miki, don Allah kiyi haƙuri ki bashi dama". 
Nidai ban ce mishi komai ba, shiru kawai nayi, shima jin baxan ce komai ba ya cigaba da maganan shi.

Rayuwa da lokaci abun tsoro ne, duba da yadda suke guduwa, a haka har bikin Fatima yazo, lokacin muke ta shirye - shiryen tafiya maiduguri, Aunty B takai 1week da wucewa,mu kuma sai week ɗin muke shirin tafiya, Mamah da ni da su maryam, zainab, hadiza, sai Aunty J, mota biyu muka tafi da shi, ranan da zamu tafi da asubah na buɗe data na, whatsapp na hau zan tura message wa jammy, sai naga baƙon number an mun magana, gaisuwa ne da tambayana yayah shirin tafiya maiduguri, sannan ake jaddada mun na kula da kaina, nidai ban damu da na bi takan message ɗin ba nayi abun da yake gabana na sauƙa,
Mun shiga maiduguri wuraren la'asaar, sauƙi aka kaimu chan gidan yayan su Fatima, mu dai bamu wani daɗe ba muka wuce wurin Fatima da ƙawayen ta, 
Bamu dawo bauchi ba sai ranan sunday, gaskiya bikin su yayi kyau sosai, mun sha ƙamshi kam, kuma munyi tsaraban ƙamshi, muna dawowa da 1month aka fara shirin auren maryam, nidai gaba ɗaya na zama busy a lokacin,  satin bikin maryam A.G yazo ƙasan, da safe ranan thursday muna shirin shiga gidan su maryam wurin lalle sai ga habiba ta shigo wujiga - wujiga da ita, duk fuskanta a kumbure, a compound ɗin gidan mu muka haɗu da ita, gaba nane naji ya faɗi, dole naja na tsaya ina kallon ta yadda take tafiya take wani irin kuka, duk jikina yayi sanyi da yanayin da ta ke ciki, hafsy ce ta jawo hannu na tace,  "don Allah Adda mu tafi, yanzu tsayuwar nan sai mamie ta ƙala mana wani sharrin, ko tace gulma ne ya tsayar da mu, jiki a sanyaye na bi bayan hafsy muka wuce, tunda muka shige naji ni babu walwala, haka akai ta sha'anin lalle har yamma muka dawo gida, washe gari friday za'ayi liyafan da mamanta ta haɗa mata, a haraban gidan su za'ayi, saboda suma filin gidan su yana da girma duk da bai kai namu ba, a ranan kuma da safe haɗiza ta shigo bauchi, wurin azahar kuma zainab ta shigo unguwar mu, tunda suka zainab ta iso muke ta shirin shiga gidan su maryam, anan hafsy suka shigo ita da ummitah, kallon su muka tsaya yi ganin irin ɗan banzan dariyan da sukeyi, don har ƙasa hafsy ke sunkuyawa, ganin haka hadiza ta tsaya da jan zip da take niyyan yi mun, baki buɗe tace,   "da alama dai kun hangi wawan zama ne ko?"   dariya suka sake ɓallewa da yi, " Adda wallahi abun dariya da tausayi ne ya faru a gidan nan, ashe jiya da muka ga shigowan Adda habiba, ashe Aliyu ya ƙara lafta mata na jaki ne, natan tausayi abun ya bani, don ance tana da ciki ƙarami, kunga ae bai kyauta ba, duk da dai ya kai 4month, ita kuma marar kunyar ƙanwar nata yau sai ta bishi har gida, ita da ƙanwar wanda zata aura, yanzu haka dai maganan da nake miki an kaita wurin mai ɗauri, don ko ya ɓalla hannun marar kunya, wai ta zare key ɗin motan shi, tana mishi magana yaƙi sauraran su ya fice wurin motan shi zai bar gidan, ita kuma sakaryar sai ta nuna mishi ita jinin mamie ce, ta saka hannu ta chafko key ɗin motan wai sai ya tsaya ya mata bayanin me yake gadara da shi da zai daki ƴar'uwarta don zaiyi aure? Bai jira komai ba yayah nah Ali gadanga kam, ya murɗe hannu sai da ya targaɗa ya karɓi key, kuma ya ingizita ta zube a wurin ya fice, bayan ya umurci mai gadi yayi waje da su,  yanzu mun shiga parlon hajiya ummah muka samu Abba yana mata bayani, shi bazai ɗauki matakin komai akan abunda yayiwa raliya ba, don ita ta jawo ita taje har gidan shi, kuma tayi mishi rashin kunya, amma akan adda habiba kam zai ɗauki mataki, don auren kawai yace zai raba, kuma itama hajiya ummah ta goyi bayan hakan, har take cewa ae rabawan shi yafi dai-dai, don babu laifim Aliyu ba son habiba yake yiba dole aka mishi da asiri, wallahi ran Abba a ɓace ya fita, ita dai raliya yau ta gamu da gamonta",    ta ƙarisa suna ƙyalƙyala dariya, suma su hadiza da zainab dariyan suke har suka ban mamaki,  ina jin jadiza tana cewa, ae kuwa Allah ne ya kama raliya da shegen ƙaton hancin ta irin na mamin ta, lokacin da na shiga gaida mamin na samu zasu fita ita da figaggiyar ƙawar nata, har tana wani mun banzan kallo ita marar kunya, nidai ban kula ta nata ba na shige parlon su, ina hango habiban tayi sauri ta shige ɗakin mamie, nidai ban bi ta kansu ba na gayar da mamin tana amsa mun rai duk a ɓace, ashe zata haɗu da gamunta ne marar kunya",   zainab ce ta ɗan ya mutsa fuska tace,   "Abba ya mun dai-dai gara ya raba wannan gantalallen auren kowa ma ya huta, ita kuma habiba idan tayi hankali da rayuwar cin amana tou tayi karatun ta nutsu, idan kuma batayi ba sai ta zo ta gama iddah idan sakarcinki ya kai ki kin sake samu mijin aure ki tallata mata ta sake amshewa, don naga ke ba kan gado bane da ke,  ita kuma raliya kaɗan ta gani, ajuri zuwa rafi",   baki na buɗe ina kallon zainab da magana ma baƙin halinta baya barinta tayi, "zainab nice mai laifi kike gani"?  Na tambayeta, dariya ta ɗanyi kaɗan tace, "wallahi Ayshaa ke nake jin haushi ba habiba, kawai dai ban nuna miki bane saboda naga baki son gaskiya, tun farko ma mai ya kai ki bayyana mata manemin ki? Kinsan halin mahaifiyarta da mugun fatan da take muku, amma idan anyi magana sai kuce mutum ya cika mugun hali, yanzu rayuwa ba komai ake bayyana shi ba ko ciki ɗaya kuka fito da mutum, amma ke har hira kike barin su sunayi,"?  Ta ya mutsa baki alaman haushi na takeji, kallon ta nayi baki a buɗe,  "yanzu dai komai ya wuce ku fito mu wuce wurin maryam sai ƙiran wayata ta ke tayi.

Muna zaune wurin liyafa naji wayata tana vibration, ɗaukowa nayi na buɗe sai naga M.G ne, katse ƙiraɓ nayi na tura mishi message muna wurin liyafah, babu daɗewa yayi replying ɗina da A.G ya shigo, insha Allahu bayan sallan ishaa zasu shigo, duk sai naji na ɗan burkice, da ƙyar na mishi reply da "is ok".


Ana idar da sallan isha kuwa babu daɗewa sai ga wayan M.G wai sun iso, da ƙyar na bashi amsa da muna gidan su maryam, dariya yayi kaɗan jin yadda na ɗan burkice, "mu ƙaraso gidan ne ko kece zaki ƙaraso gida"  ya tambaye ni,  "ehh ku shiga wurin hajiya ummah yanzu zan taho",  na bashi amsa,  "ok bari mu shiga mugaida ummie tukun",  yana faɗa ya kashe wayan, nidai duk sai naji nutsuwata tayi ƙaranci, ina ɗaga ido muka haɗa ido da zainab, alama ta mun da idon ta akan na fita basai nagayawa wani ba, haka ko akayi ban bari an hankalta ba na tashi na ficce.
Side ɗin ummah na shige, gaishe ta nayi sannan na wuce ɗaki, ina kallinta tana ta bina da harara, ni ko kula ta banyi ba, don nasan draman da suka sha ɗazu ne da hafsy da ummitah take jin haushi na, wai yara ƙannen bayana sun fini wayo kowa ta riƙe gwanin ta, su kuma suka gwasale ta, kacha- kacha sukayi har tace duk sai ta hana jikokin ta auren su, bari Allah ya dawo da su lafiya, da yake duk sun tafi Training na soja a NDA kaduna, da taga sun haɗe mata kai sai ta dawo kaina da yabo, ni kuma na ƙi kulata na fita, shine ban shigo ba sai yanzu, ban gama abunda nakeyi ba kuwa naji muryan sallaman M.G, ina ji suna gaisawa da hajiya Ummah, ita kuma kaman zata cinye su don murnah,  sai maimaitawa take da "Allah sarki jama'an Ahmadu na,  wato duk da Allah baisa Ahmadu yazo ba kunyi kara kunzo gaishe mu ko? Barka wallahi naji daɗin zuwan ku, Allah dai ya muku Albarka,"  sannan ta juyo tana ƙwala mun ƙira wai na fito na kawo musu ruws, amsawa nayi na fito, gaishe su nayi a jam'i, sannan hajiya ummah tace, "kuran baya sai ki buɗe fridge ki ɗauko ruwa da ɗan abun zaƙi wanda ɗana Usmanu yake sayowa donni da baƙina ki kawo, don dai badon kowa yake kashe kuɗin sa ba sai donni",  ina jin tafara musu bayanin faɗan mu na ɗazu suna ta dariya, na ƙarasa kitchen na haɗo abunda duk ta lissafa, bayan nakai musu ne na wuce ɗaki na basu wuri suyita shan labarin nata, bayan mintuna goma naji ta sake ƙwala mun ƙira haka nafito na dawo parlon na zauna, ina jin tana ta mitan tafiya na, har tana cewa M.G ae ban waye ba  a rashin wayewa na ƴar'uwata ta ƙwace mun mijin aure, yanzu dai kana ganin ta kaman mai hankali ko? Tou fosss take babu kan gado, idan ba rashin wayo ba ni kuma wani hira zan muku y kuji daɗin shi zamanin mu ba ɗaya ba? Ya wuce gaisuwa da ɗan wasan jika da kaka ae sai su, kodan farin fuskarta ae sai ku kai goma na dare baku ankara ba, nikan ae tun ɗazu nake ga mao shirun nan kaman ya daka tsalle ya fice don gajiya da hirana",   dariya M.G yayi yana kallona har na zauna a gefe ɗaya, bayan ta wuce ɗakinta M.G ya juyo yana kallona fuskan shi cike da fara'a yace,  "wato ke ƙwacen samari ake miki ko? Koda yake hakan na ya mana dai-dai don ke ba rabon su bace, rabonki gashi nan tafe akan lokacin da ya dace",  yana faɗa yana kallon A.G da dariya a fuskan shi, ɗago kaina nayi kawai sai idon mu ya haɗu da A.G daya ƙura mun ido, haushin shi naji ya kamani, gashi yayi wani irin fari yayi kyau, sai dai kuma kaman ya ɗan faɗa kaɗan, murguɗa mishi baki nayi na ɗan harare shi,  kaɗan kai yayi alaman dai nida shi.
Wato M.G da A.G dukkan su kyawawa ne kuma farare, banbancin M.G yafi fari kuma yafi kyau, sannan idon M.G a bayyane suke, shi kuma A.G idon shi a lumshe suke,  sai wani dalile ne yake saka shi buɗe su, idan ya buɗe kuma zakiga girman su da kyaunsu,  don shi Allah yayi mishi kyakkyawan ƙwayan ido, sai kuma tsayin su kusan ɗaya ne, M.G shi yana da ɗan jiki fiye da A.G, shiyasa an fi ganin tsayin A.G,  sannan A.G gashin kanshi mai laushi ne irin na fulani, hancin M.G yana da tsayi sosai, while A.G nashi dai-dai suke, amma suna da kyau sosai na tsarin zaman su akan fuskan shi, duk a wannan haɗa idon da mukayi da shi na ƙare mishi kallo, wanda ban taɓa tsayawa na ƙare mishi kallo ba, amma duk da haka banji yayi mun ba,  idona na mayar kan M.G da naji yace bari ya ɗauko abu a mota, bayan ya fita parlon ya ɗauki shiru na wani lokaci,  chan kaman an mishi dole na tsinkayo muryan shi yana cewa,   "ke baki iya gaisuwa ba ko?  bakijin magana ko?",
Hararan shi nayi ƙasa-ƙasa nace,  "kunnen ka dai bayaji, ae na gaisheku",  na faɗa ina ƙara tura bakina gaba,  ido ya ƙura mun wanda har naji kaifin idon na shi a jikina, hakan ya saka na sake ɗago idona na kalle shi, shiɗin ma kallo na yake babu ƙiftawa, da sauri na sauƙe idona ƙasa,  "kedai ɗago kanki ki kalli kyakkyawar fuskana ki ɗan samu peace of mine",  naji muryan shi ƙasa -ƙasa yana faɗa, murguɗa baki nayi nace  "ni har akwai wani kyaun fuskan ɗa namiji da zan gani har ya burgeni? Ni ban ma ga kyaun ba".
Wani sautin dariya naji kaɗan ya fito daga gareshi, wanda ya ban mamaki har na ɗago na dube shi, don ko murmushi ban taɓa tsammanin yana yi ba,  "zakiyi bayani wataran, duk ran da Allah ya baki ɗa ko ƴa, mai kyaun fuskan nan zakiyi bayani idan kina shayar da shi",  yana faɗa ya miƙe tsaye, dukka hannayen shi a zube cikin alhajihun wandon shi yace,  "gobe what time kike free"?   Kaman bazan amsa mishi ba kuma dai sai nima na miƙe na ce,  "gobe fah shine ranan bikin gaba ɗaya, ni bana free".
" saboda baki da wayo yadda kaka tace ko? Inaga a gidan amaryan zaki kwana, tunda ance gobe za'a ɗaura aure, wuni, kai amaryah, akwai wani abu bayan wannan"?
Harara na sake jifan shi da shi, "a gidan amaryan zamu kwana ae", na bashi amsa kai tsaye, juyowa yayi kaɗan ya kalle ni, bakin shi a ɗan mele ya wani ya mutsa fuska yace,     "kada ma ki fara, don ki sani naki ranan auren bana tunanin ma wata ƙawa zata miki rakiya, so gara ki daina wahalar da kanki a na wasu, angon ki da yammah zai zo ya ɗauki kayan shi,babu maganan rakiya ballantana maganan kwana",
 "chabɗi jam ae dai ba lalle kadan mijina ba ballantana ka bashi shawaran hakan",    na faɗa ina zaro idona, ɗan murmushi  kawai yayi yace,  "zoki rakani yarina, babu amsan da zan baki zakiyi bayani lokacin,"
Ba don naso ba na raka shi, a mota muka samu yayah M.G yana kwance yana waya, tasowa yayi hannun shi riƙe da wayan yana kallon mu cike da murmushi a fuskar shi ya miƙo mun wayan yana cewa,  "ku gaisa da GIWATA".
Zuciyata tace nai ta yanke Rasssss, har rawa  jikina ya fara, da ƙƴar na saka hannu na kari wayan, ɗan ƙaramin muryantq marar gurman amo ne ya daki kunne nah, "Aunty Beauty barka da dare, ae basu ce mun zasu zo wurinki ba da na bada saƙon gaisuwa na, don nasan wannan lion ɗin naki ban isa nace zan biyo suba, don sai ya ɓal mun ƴan yatsuna",  ta faɗa tana dariya, nima ɗan murmushi kaɗan nayi marar sauti nace mata,  "barka da dare",  da dariyan ta tace,  "sorry Aunty nine yakamata na gaisheki sai na tsaya suruti, Aunty beauty yayah kike?  Hope dai mun samu karɓuwa, don  Giwa na yace yau zai je rakiya, tou Allah ya sanya alkhairi,  Allah yasa ke rabon yayah nane, Ameen ya rabbi",  zuciya nane naji ya hautsine, wato dai daga dukkan alamu M.G ya fara neman Heedayah kenan?  miƙa mishi wayan nayi ba tare da na bata amsa ba, karɓa yayi batare da ya nuna alamun damuwa ba yace,  "Giwata bari nadawo zamuyi magana",  yana faɗi ya katse wayan, hararan shi A.G yayi yaja tsaki yace,  "ka cika shiririta wallahi, yarinya ƙarama kake wani cewa Giwata? Wallahi zata rainaka",  ya faɗa yana buɗe wurin zaman mai zaman banza ya zauna, shidai M.G dariya yakeyi ya ɗan rusuna kaɗan yace,   "da girman kujeran babban yayahmai bani aure da aurar da ni, ni na'isa nace wani abu? da ba don kada ka hanani Giwata ba ae danace, Allah kaɗai yasan me kace yanzu a ciki kafin ka fito, hala ma suƙawa kayi kayi sallama",  yana faɗa ya buɗe gaban motan ya shige yana dariya,  hararan shi A.G yayi baice komai ba sai dawo da idon shi kaina yayi,  "goodnyt sai munyi magana"  hararan su dukkansu nayi na juya na koma ciki,  a zuciyata nake cewa dama ban rako su ba, na fito ne don muyi sallama da M.G ashe rabon naji takaici ne kawai ya fito dani wajen, raina ranan a ɓace na kwanta, wanda dukkan su sun kasa gane kaima, haka suka haƙura da tambayana suka kwanta.


Washe gari aka ɗaura auren maryam lafiya, akayi wuni cike da farin ciki da nishaɗi, ana idar da sallan la'assar aka fara tafiya kai amaryah, saboda za'ayi buɗan kai a gidan su angon, kunsan ƴan bauchi da hawa da buɗan kai,  ina tsammanin ganin ƙiran M.G tun safe amma shiru, haka ɗai na sake a ka cigaba da hidiman bikin, muna gama shiri sai ga Hafsy ta shigo, ƙirana tayi tace mun na fito gasu Yayah M.G da Yayah A.G a waje suna mun magana, raina naji ya ɓaci, amma ban neme wulaƙantasu ba na fita inda suke, lokacin da na iso jikin motan still M.G waya yakeyi, ɗaga mun hannu kawai yayi ya cigaba da wayan shi,A.G ne ya ƙura mun ido,  hararan shi nayi na juyar da kaina gefe ban gaishe shi ba, shima shirun yayi kawai yana kallona, ganin haka yasaM.G ya juyo yace,  " Aysha kiyiwa zainab da hadiza magana mu wuce gidan amaryan ko".
Idona na mayar kanshi nace,  "akwai motocin da angwaye suka turo ae,su zamu bi",  ina faɗa naga M.G ya mayar da kallon shi kan A.G yana dariya ƙasa -ƙasa.
"Bana son musu zaki yiwa Ahmad musu ne? Ko dan kinga M.G yana wasa da ke? Wuce kije ku fito, ban amince ki shiga motan kowa ba",  ya faɗa fuskan shin nan babu alaman annuri, ba don naso ba na juya na shiga neman su Hadiza, don wannan masifaffen bazan iya da shi ba.


Kuyi haƙuri hala kuyita ganin error, ban yi editing ba, nagode.


*AUNTY NICE*