Wike Ya Gayyaci Jigon APC Sanata  Wamakko, Don  Kaddamar Da Ayyuka A Rivers 

Wike Ya Gayyaci Jigon APC Sanata  Wamakko, Don  Kaddamar Da Ayyuka A Rivers 
 

Gwamna Nyesom Wike ya gayyaci jagoran jam'iyyar APC a Jihar Sakkwato, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya zo ya kaddamar da ayyuka a Jihar Rivers a ranar 9 ga watan Agusta.


Takardar gayyatar na dauke da kwanan watan 2 ga watan Agusta kuma tana dauke da sa hannun gwamnan a hukumance.
 
A cikin wasikar, Wike ya gayyaci tsohon gwamnan Jihar Sokoton, wanda shi ne shugaban kwamitin tsaro na Majalisar dattijai, don kaddamar da tagwayen titin Ogbumnmu-abali a Port Harcourt.
 
Wike jigo ne a babban jam'iyyar hamayya, ta  PDP a kwana nan ya yi musayar maganganu da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar  a yayin da shugabannin jam'iyyar ke kokarin sulhunta su. 
Wasikar ta ce: "Gwamnatin Jihar Rivers ta kammala ginin tawagwayen hanya na Ogbumnu-abali a birnin Port Harcourt a wani bangare na shirin sabunta birni da cigaban jihar. 
"Za a kaddamar da titin a hukumance a ranar 9 ga watan Agustan 2022 misalin karfe 11 na safe. 
"Don haka ina gayyatar ku domin zuwa kaddamar da titunan, kamar yadda aka tsara, da izinin Allah da kuma amfanin mutanen Jihar Rivers.