MAMAYA: Labarin Soyayyar Mutum da Aljani, Fita ta 41

MAMAYA: Labarin Soyayyar Mutum da Aljani, Fita ta 41

Page 41......

 

 

 

Tunda Nasir yabar gun walimar Sai yaji baki ɗaya ransa ya ɓaci, domin ya lura Malamin nan san Bilkisun yake, ita kuma ga alama bata iya korarsa ko tayi masa kashedi.

 

Duk yabi ya ɗauki damuwa ya liƙama kanshi, daya rufe ido sai ya hango sanda yake baya kyauta yana gaya mata kalaman soyayya, ya sani sarai kawaicin Ibnah daman sai ya dinga cutarsa, jin daɗin sa guda da yasan tana sonsa dan haka da wuya wani yasa ta juya masa baya kan son da take masa.

 

Haka yayi ta saƙa da kwancewa har barci ya ɗauke sa.

 

Cikin barcin yaga wani mutum dogo mai tsayin gaske, yana ta kallonsa fuskarsa babu alamar rahama ko rangwame, ya dubi Nasir da wasu ƙwalaƙwalan idanuwa jawur yace,      "Na zo ne nayi maka kashedi kan wadda nake so, tun muna cikin fagen rahama ka gaggauta fita harkar ta, idan ba haka ba, sai na ɓadda kai daga dogon duniyarku zuwa tamu duniyar."

 

Cike da mamaki Nasir ke kallon aljanin domin yanzu ya fahimci ba mutum ke masa magana ba.

 

Wata uwar tsawa aljanin ya dakama Nasir ɗin ganin yayi biris da kashedin da yake masa, ga alama ko gezau bai yi ba balle yasa ran kashedinsa ya ratsa kunnen yaron.

 

Hakan yasa siffar aljanin ta fara sauyawa zuwa siffa mai ban tsoro da firgitarwa, hakan yasa Nasir ɗin ƙoƙarin fara karanto addu'ar neman tsari daga abin tsoro.

 

Sannu a hankali siffar aljanin ta koma wani mummunan dodo mai manyan idanuwa farin ruwa na kwaranya daga cikinsu, ya ɗaga kafta-kaftan hannuwansa sama, sai ga wasu manyan kawuna masu fissar kan Hawainiya na fitowa daga cikin kowane hannu nasa, hancinsa yayi tsini sama kamar an miƙa sanda sama, hancinsa yayi bake-bake sai a jefa jariri cikinsa ya shige kai tsaye.

 

Wani irin ihu yake yana tada tsuntsayen dake dajin dan firgita.

 

Wuta ta kama jikinsa tana ci bal-bal ba kyan gani.

 

Duk abin nan Nasir bai motsaba sai kawai bakinsa dake motsawa yana karanto addu'a.

 

Zuwa yanzu wutar ta fara rarraba jikin aljanin sai dai kuma dukbtsokar da ta fita sai ta koma siffar jikinsu aljanin ta kama ihu da hargogowa.

 

Wata uwar walƙiya ta bayyana sai ga wata mace cikin shirin kayan mayaƙa ta bayyana da wata doguwar sarƙar wuta tana ci a hannunta.

 

Bayyanarta gun kenan ta buga sarƙar a cikin tsakiyar aljanun, ai kuwa sai wutar ta ɗauke sai gasu sunyi cirko-cirko cikin mummunar shiga ba kyan gani, suna ganin matar duk sai suka razana suka nemi tserewa inka cire babbansu dake tsaye cikin fusata da baƙin rai .

 

Cike da tsawa tace, "Na rantse da abin bauta ta duk wanda ya kuskura ya taɓa Nasir anan zan masa keji na rufesa na tsawon rayuwarsa."

 

"Ƙarya kike muddun ina shaƙar numfashi sai naga bayan Nasir tunda ya shiga cikin soyayya ta.

 

Wata mahaukaciyar dariya ta bushe da ita kafin ta nuna shi da yatsa tace, "Kai ne kake ambatar soyayyar wata halitta bayan masoyiyarka Bintu bin Safar ? Lallai ka ranka kuskure mai girma domin kafin kowa sanin wa ce ce Bintu bin Safar , ta kashe ƴan matan Aljanu fiye da dubu goma sha tara saboda kai, ta shiga  wahalhalu masu yawa saboda kai, shine yanzu zaka bikironda soyayyar wata bil'adama dan kawai ta tafi duniyar gabas jinyar mugun raunin da saboda kai ne ta same shi?

 

 

 

Dariya ta bushe da ita tace ba dan ni ce mai kare lafiyar Nasir da abin da ya shafesa ba da ni ce ta farko da zan fara aika mata da saƙon soyayyarka .

 

Tana zuwa nan ta ɓace ita da Nasir ɗin suka bar Yah Malam cikin fuskar tashin hankali da ruɗani.

 

 

 

Inna Huraira na kwance jiki yaƙi lafiya zuwa yanzu bata ko magana sai ɗaga kai kawai take iyawa.

 

Jikinta yayi baƙi ba kyan gani tamkar an shafa mata gawayi , magani ake mata amma ba wani cigaba juya iyau dai ake .

 

Hankalin Bilkisu sosai ya tashi da ciwon Innar tasu musamman wani lokacin da take yawan jin zuciyarta na raya mata Innar kamar ba ita bace ba, tasha jin kamar Aljana ce kawai ke dawainiya a cikin siffar Innar tasu, amma wa zata gayamawa ya aminta ?

 

Kamar yau da tana zaune gabanta tana shafa powder Kawai Sai madubin ya hasko fuskar Innar tasu kawai ganin wata ɓakar mace tayi tana ta barci madadin fuskar Innar da take gani a fili, ɗaya kalli Innar a fili sai ta kalleta a cikin madubin sai ta ganta daban ba kyan gani.

 

To fa mike faruwa da Inna Huraira ne ?

 

 

Taku Haupha