ANA BARIN HALAL....:Fita Ta 39
ANA BARIN HALAL....:
*Page 39*
*INA UWARGIDAYEN SUKE? NACE INA UWARGIDAYE MASU CAPACITY SUKE, IDAN BAKI YI MATSA GA MASU* *AUTHOURITY, NACE TSAYA IDAN BAKIYI GA AMARE MASU AUTHOURITY,* *IDAN KIN SHIRYAH GWANGWAJE SHINFIƊAR MAIGIDA,* *TOU KI ƘYALE ƳAN LOCALLITY KI MATSO KI SAYI NAKI,* *BEDSHEETS ƳAN GASKE, KU MATSO KU YAƘI PORVERTY DAGA TASKAR HALIMA YISUF GWARZO, INA MAI TABBATAR MIKI IDAN KIN SHIMFIƊA ZAKI ZAMA MAI CAPACITY MAI AUTHOURITY,* *DOMIN KI WANKE ZUCIYAR MAIGIDA YA HASKAKA,*
*MUNA AIKAWA DA SHI KO'INA A FAƊIN ƘASAR NAN.*
*DOMIN SAYEN ƊAYA KO SARI, KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAMBAR*
08064586559
**********
Tun ɗazu da Aliyu ya ƙira wayana, wai yaji lafiyan sabeer nakejin zuciyata babu daɗi, ni ban san ma na tsane shi ba sai yanzu, da baya burgeni ne kawai, yanzu kuma daya wahalar da habiba sai naji haushin shi nakeji, gashi yau ana magrib mamie ta aiko mai mata aikin side ɗinta ta karɓi Sabeer, sai naji haushin sun mun yawa, don na lura kwana biyu idan naje ɗaukan shi ta ringa mun wasu kwane -kwane, ko tace ya tashi da mura ko tace yana bacci, ni dai naƙi yin zuciya saboda ina ji a raina ɗana ne habiba ta haifa mun, anzo an ɗauke shi babu daɗewa Aliyu kuma ya ƙirani, gaya mishi nayi ya ƙira mamie Sabeer yana chan, haka dai ya ɗan taɓa kame -kamen shi ya barni, don ina jin shi har da cewa tsaraban me nake so idan zai dawo, darajan jammy yaci da na kashe wayana a lokacin, amma na daure mukayi sallama.
Ɗaukan ƙiran A.G nayi duk babu wani walwala a tare da ni, jin muryana wani iri sai yayi ƙasa da muryan shi yana tambayana, "waya taɓa beauty ne"?
Turo baki nayi kaman yana gani na nace, "mijin habiba ne ya ɓata mun rai", "lallai ya maida hankalin shi, don darajan habiba ne da yaron mu zai saka na ɗaga mishi ƙafa, sbd haka kada ya sake", dariya maganan shin ya bani, haka dai baya son yawan maganan amma yaja ni da hira, har 11:00 muka kai muna hira, yawanci ma nike bashi labarin, rayuwar mu na ƙuruciya da habiba yawanci nake bashi, wani yayi dariya wani ya tayani alhinin mutuwan Ayshaa, da ƙyar dai yayi sallama dani, don sai da yaji na fara jera hammah tukun ya barni.
Washe gari kuwa ana idar da sallan ishaa suka zo tare da M.G, bayan sun gaida ummie parlon hajiya ummah suka wuce, nima achan naje na same su, gaba ɗaya sai na samu kaina da jin kunyan A.G, gashi tun da na shigo idon shi suke zube akaina, ko kunyan M.G da keta zolayan shi baya ji, nidai sai sunne kai nakeyi kamar wata munafuka, abun mamaki M.G kaman bai taɓa sona ba haka yayi ta acting, irin dai kawai ni wanda amininshi ɗan'uwan shi zai aura ne, nima ganin yadda yayi kawai sai fuske, muna zaune kuwa sai ga wayan Aliyu ya shigo, ido na zubawa wayan har ta gama ringing ina kallo ban ɗaga ba, a karo ta biyu da ta sake shigowa sai A.G ya ƙura mun ido, ganin haka sai M.G yace, "ki ɗauki wayan mana, ko ba important call bane"? Ɗaga kai nayi alaman hakan ne, shidai A.G ido kawai ya ƙura mun, jin kusan 5mnt ba a sake ƙira ba sai hankali na ya kwanta, amma da yake Aliyu jarababbe ne sai ya sake ƙira, haɗa ido mukayi da A.G, bai buɗe baki ba yayi mun alaman na ɗaga wayan, ganin fuskanshi ya ɗan chanja sai na ɗaga wayan, sallama mukayi daga nan muka gaisa, tambaya na yayi Sabeer, gaba ɗaya naji haushi yakamani, har ban san lokacin da nace, "bayan magrib nae maida shi wurin mamie, ka dinga ƙiranta kana jin yayah yake mana", murmushi yayi yace, "haba ayshaa ae tunda ba nono yake sha ba kidinga barinshi a wurinki mana, ae inaga kwana ma zai iya a wurinki, ni ina so ya buɗi ido baisan kowa ba a matsayin uwa sai ke",..... ban jira ya ƙarasa shirmen shi ba nace, "sai da safe ina tare da baƙi", kashe wayan nayi na ajiye, ina ajiyewa muka haɗa ido da A.G, ƙura mun ido yayi kawai, duk sai naji babu daɗi, a ɗan ruɗe nace, "mijin habiba ne, yana so yaji yayah sabeer yake"? "ok shirmemen mutumin da Barrister ya bani labari wai don shirme ya turo mamyan shi wai a bashi ke madadin habiba ko? Tou ya manta irin uƙuban da ya bawa habiba ne? Baida hankali ae".
Da sauri A.G ya maida kallon shi kan M.G, har muryan shi na ɗan shaƙewa yace, "yaushe haka ya faru"? Tsaki M.G yayi yace, "ae inaga maganan nan bai wuce 2weeks ba, yafa saki habiba kafin ta haihu, amma don rashin hankali wai a bashi Aysha, sai da Abba ya fito musu a mutum tukun suka haƙura", M.G yace.
Idon shi ya dawo dashi kaina, batare da ya kalli M.G ba yace, "bai haƙura ba",
Kallon shi M.G yayi sannan yace, "kaman yayah? Kaji sun sake dawowa ne"?
Fuskan shi a matuƙar murtuke yace, "dama ae wancan ɗinma daga kai har ita babu wanda ya sanar dani, ballanyana har naji a wani wurin, salo ya chanja, meyasa zai ƙira wayanta? Yaron ya isa magana ne"? Ajiyan zuciya na sauƙe na maida kallona kanshi, harara ya aiko mun da shi, hakan ya saka na buɗe bakina da sauri nace, "tou ae Abba ya dakatar dasu",
"duk da haka kin gaya mun"? Naji A.G yana faɗa, ganin haka yasa M.G ya miƙe tsaye yace, "bari na ɗan miƙe ƙafana kafin ka fito", shima A.G miƙewa yayi tsaye yace, "muje kawai, nima zan leƙa gidan Daddah", murmishi M.G yayi mun sannan yayi sallama ya fita, nidai ban tashi ba kuma kaina yana sunkuye, ɗaure fuskana nayi naƙi kallon inda yake, ganin haka yasaka ya kasa fita, dukka hannayen shi ya zuba cikin aljihun wandon shi, ido ya ƙura mun har na zuwa wani Lokaci, ko ya fahimci raina a ɓace ne yasaka ya ƙaraso gaba na ya tsaya, shiru naji yayi hakan ya saka na ɗan ɗago kaina na dube shi, ganin kallona yake yasa na murguɗa bakina na maida kaina ƙasa.
Tsugunawa yayi dai-dai saitin fuskana, sannan naji yace, "tou meye ne kuma Eeshaa"? Murguɗa baki na sakeyi na ƙara hararan shi, kawar da kaina gefe kaɗan nayi, wani ƙamshine mai nutsuwa yake tashi daga jikin shi, hakan ya saka naji na sake kallon shi, kallo shi kuma na sakeyi, ya wani marairece fuska kaman zaiyi ihu, "tou ni meyasa zan gaya maka maganan da baida wani muhimmaci a gare mu, kana Exams fah lokacin", na faɗa ina maida ido na cikin nashi, idon nan a lumshe an zuba mun su kaman zai lashe ni, "bana son ƙiran da yakeyi Eeshaa, please ki daina ɗauka, idan yana so yazo gidan yaga ɗanshi, shima bake zaki kai ba, yaje wurin kakar yaron please".
Ɗaga mishi kai nayi alaman naji, "tou ki sake fuskan ki bar fushin", ya faɗa still yana tsugune a gabana, kallon shi nayi nace, "tou meyasa zaka tafi yanzu"? Tashi yayi ya zauna a kujeran da yake gefe na yace, "an ma fasa tafiyan nan, dama M.G nake yiwa wayo ya fita".
Dariya ne ya kubce mun babu shiri, "ka dai chanja ne, ae ɗazu fushi kayi", shima dariyan yake yace, "ae danaga naki fushin yafi nawa tunin na daina, shi kuma M.G abun ya hanani tafiya wai sai yayi gaba irin na biyo shin nan, tou anƙi wayon, so yake mu kuma yaje yaga wannan mummunar budurwar wanshi, ni kuma yasaka nayita kallon bango".
Dariya sosai A.G ya sakani, wato idan ya samu wuri shima bakin shi buɗewa yakeyi ko? Wato har zolaya ya iya?
Ido ya zuba mun yana murmushi, gaba ɗaya yayi kyau sosai, har wani rausayar da kanshi gefe kaɗan yayi yana kallo na, a hankali na dakata da dariyan na kalle shi, "waya gaya maka Heedayah mummuna ce? ae da kai take kama fah, kuma ta fika ma kyau don ita mace ce", na faɗa ina kallon shi da murmushi a fuskana, kwaikwayon yadda nake tura baki yayi, "waya gaya miki mace tafi namiji kyau? Kema ae baki fini kyau ba ballantana heedayah, ku daina saka kwalli, da shafa powder da jan baki kuga idan ba ace munana bane ku, ke kinyi sa'a fah", ya faɗa yana shafa fuskan shi.
Hararan shi nayi cikin wasa nace, "yanzu kai kana ganin kafini kyau ne"? Ɗaga kai yayi yana kallon cikin idona, jijjiga kai nayi na kawar da ido na.
"kijira muyi aure, wanzami zan saka ya miki aski tal kwabo, ranan zaki banbance nida ke wayafi kyau, nima zanyi askin".
Ya faɗa yana kashe mun idon shi.
Aeko bansan wani irin dariya bane yazo mun, amma na saka hannu na rufe bakina, dariyan yayi yace "kin yadda nafiki kyau?"
Kai na girgiza alaman a'a, "tou sai mun haihu, me kama dani da me kama da ke, zakiji ance kai mai kama da Aminun yafi kyau" ya faɗa yana ɗaga mun dukkan giran shi.
Tura baki nayi dukka gaba nace, "ni duk masu kama dani zan haifa".
"Haba? Dayawa zaki haifa mun"? Ya faɗa yana sunkuyo da kanshi dab da fuskana, rufe fuskana nayi ban ce uffan ba, chan da na gajji da zolayan shi sai nace, "suɓutan baki ne fah", dariya ya fara yana miƙewa tsaye yace, "aeko ni A.G na dinga saka ki suɓutan baki, da ido a sai kin mun suɓutan zance, ƴan mata tashi kimun rakiya kada M.G ya zaune miki ni yau,"
A mota muka samu M.G ya kwantar da sit yana ta waya, harara yabi A.G da shi, shi kuma A.G ya wani ɗaure fuska kaman bashi bane yanzu yake ta ɓarin zance, ni dai murmushi kawai nakeyi ina kallon su, har sai da suka shige tukun A.G ya kallo ni, "gobe insha Allahu da yammah zan shigo, zanzo naga yarona ko"?
"gara da kache kai, don gobe saloon zan kai Giwata, ba zanyi wani rakiya ba azo ana fito da ni waje da wayo", murmushi nayi nace, "tou yayah M.G a gaida giwar", sannan na juya da sauri nayi cikin gida.
Ina shiga na wuce direct ɗakin Ummie, anan na sameta ita kaɗai, tambayanta nayi hafsy, "tana ɗakin ku tana jaraban wayan kun nan", nidai murmushi nayi na zauna a gefen gado kusa da ita, zayyene mata yadda Aliyu yake damuna da ƙira nayi, da kuma yadda yau mukayi har ran A.G yaso ɓaci, ido ta ƙura mun tayi tagumi tana saurara na, har sai da nagama tukun ta sauƙe ajiyar zuciya, "kada ki ƙara ɗauka, insha Allahu da safe zamuyi magana da yayinki, abunda muka tsayar kuma zamu gayawa Abban ku, amma in banda neman fitina an ce musu da maganan aure akan ki, shi kuma zai dinga damunki da ƙira? Gaskiyan Aminun ne ae, yazo har gidan yaga ɗan na shi mana, ae Abban ku bai hana su ba, ko kuma ya ƙira mamin ta ku yaji yayah yake mana? Shirmen banza dama ya damu da abunda ke cikin ne ya wofintar da uwar yaron"?
Muna maganan sai ga hafsy ta fito, zama tayi tana ta zabga masifah nidai ido na ƙura mata nayi tagumi ina kallon bakin masifan nan, sai da tayi iya yinta sannan ta dube ni tana wani murmushin shaƙiyanci, "Adda nace yayah A.G bai kawo mana wani tsaraba bane? Ina sauri ae naje muyi gaisuwa na musamman sai aka ƙirani a waya, dama turare nake sha'awa wallahi, idan bai sayo ba kuma sai ya ɗan zaga damu gari su ganmu muma mu gansu, don naga wata sabuwar mota sukazo da ita, nace harka taci uban tada kenan"?
Hararanta ummie tayi tace, "wallahi naga kinje kin tambayi wani tsaraba kiga yadda zanyi gutsi-gutsi da naman bakinki, ke ni hafsy meyasa kunya ya miki ƙaranci ne kam"?
Tana Dariyan ummie tace, "haba mumsy bawai kai tsaye za'a fito ba ae, kwane -kwane akeyi ae, bayan gaisuwa sai a sauƙe dabaru, kin san kuɗin nan fah kaman na banza suke da shi, ba wai daɗin shima suka sani ba", ta faɗa tana dariya.
Dariyan nayi nace "kin ɗauka ranan bai fahimce manufanku bane keda ummie ko? Tou bayan kun fita dariyan ku yayi tayi, har ya ƙara mun haske akan halin ku".
Baki hafsy tariƙe tana dariya, "kin fasan barristocin nan Allah ya musu ɗam banzan wayo, bakiga yayah Ahmad bane, duk shirun shi wayon tsiya yake da shi kina shirin cutar shi yake ganoki, kuma sai yabi diddigi kafin ya baki abu, shiko yayah muhammad bawan Allah yayanmu madadin ubanmu, kana faɗa zakaji tarararat a account ɗinka, baya ma bin ta kanka wallahi, tou inaga da M.G ne buris zaiyi damu yayi ta labta mana abun duniya, shi ko A.G nan daga ganin idon shi wayone da shi, idan bakiyi da gaske bama Adda sai yaci naki", ta faɗa tana wani ya mutsa fuska, ita dai ummie kallon bakin ta kawai take tana mamakin halin hafsy, nima dariyan ta nakeyi, "aiko zan gayawa Yayah Ahmad abunda kiƙa faɗa, tou na hannun damanki fah"? Na faɗa ina dariya, don nasan sharrin da zata zabgawa yayah umar.
Aiko baki ta riƙe da hannunta, "dila kike ji, ae ba banza ba hajiya umma take ce mishi diƙa sarkin wayo, ae yayah umar sai da yaci naka, don ni har yanzu yana ƙwaƙile mun account ɗina, kullum alƙawari yake mun idan yayi kuɗi ni zan fi kowa morewa a gidan nan, a wayon shi wai ko ummie bazata ci kuɗin shi ba irina".
Aiko daga ni har ummi dariya muka kwashe da shi, ummie tace, "amma duk da kinsan wayo yake miki ae ko kullum ƙusƙus ɗinku tare ne,"
Dariya hafsy tayi tace, "tou ummie yayah na iya da saurayin kakata ummah? ni bana so mu rabu ne saboda duk gidan nan nafi jin taisayin shi, saboda baiyi dace da mace ba, don wallahi ummitah ɗan banzan wayone da ita ga son abun duniya, kedai kawai ummie godiyarki ga Allah da kika haifi su yayah Ahmad masu tausayinki, sai kuma da Allah ya baki ni, don ido na akan ummitah yake, tana samfe yayah umar zan samfe yayah ishaq, kema ki dongwali arzikin ƴaƴa, tou ina zan saka ido ana zuƙe miki ɗa acan side ɗin nima nakasa zuƙe na wasu ɗan", ta faɗa tana wani tura baki gaba.
Dariya kaman zan faɗo a kan gado, ummie na kallon drammer hafsy tace, "nidai tashi kije kiyi alwala kizo kiyi shirin bacci, ae Allah yaga halin ku ɗaya ne ya haɗaku ƙawance, mazajen ma ya baku daidai da ku, halinku ɗaya da umaru a wayo, shiyasa kuke son junaku, kinga Ayshaa ae da yake halinsu ɗaya su uku sai naso yazo ɗaya, shiyasa ma mijinta bai da fitina irin halinta Allah ya bata".
"yanzu ummie kina nufin yayah ishaq baida halin ƙwarai kenan"? Hafsy ta faɗa tana wani zaro ido waje.
"nikan ki rufa mun asiri hafsy, bance kije ki gayawa ishaq nace wani abuba, ae ishaq inda hali ake bi ae bazaku haɗuba, shima masha Allah, kedai tashi ayi shirin kwanciya", haka mukayi sallama cike da farin cike a zuciyar kowa, har bakin ƙofan parlor ummie ta rakani, tana tsaye har na ƙarasa ƙofan parlon hajiya ummah, hannu na ɗagawa ummie itama ta ɗaga mun, ina shiga na samu hajiya ummah zaune a parlor, harara take bina da shi, dariya nayi nace, "ke kuma matar umaru hararan na meye"?
Tsaki tayi tace, "kin tattare kinje wurin mahaifiyarku, babu kunya ta zauna tana ta hira da ƴaƴan cikinta, ae da kuka gama hiran da A.G ɗin sai kizo muyi shawar -wari, amma bawai kawai ki wuce wurin uwarkiba, itaga ga mai ƴaƴa ta wani riƙe ki a chan",
Dariya nayi nace, "ke idan Abba ko Aunty Rakiya sukazo kada ki kula su, ki dinga sharesu su zauna su gajji su tafi, ni kuma muna tare ne da hafsy bawai ummie ba", na faɗa ina ɗaukan ruwa nasha.
"Wato ƴaƴan nawa kike so nabarwa duniya su? Tou baki isa ba, kinci uwar ƙarya kuwa, ita kuma hafsy take kowa? Munafuka baka ganin ƙafan ta anan sai isiyaku yazo tukun zata ishe ni da iyayi, ta dinga jele kenam kaman wutsiya", tana faɗa kuwa na kwashe da dariya.
Waya nane ya fara ringing, ganin A.G ne ya saka na tashi nayi hanyar ɗaki ban kula ta kanta ba.
*AUNTY NICE*
managarciya