Hare-haren 'Yan Bindiga Mazauna Ƙauyuka Sun Gudu Birni Neman Mafaka A Jihar Kebbi

Hare-haren 'Yan Bindiga Mazauna Ƙauyuka Sun Gudu Birni Neman Mafaka A Jihar Kebbi
Daga Abbakar Aleeyu Anache,
Yan bindiga sun kai wani hari a wasu kauyuka a arewacin Najeriya sun kashe mutane 10 a farkon wannan mako a wasu hare-haren da yan bindiga suka kaddamar a kan wasu kauyuka a yankin Zuru,
An kashe mutane da dama acikin wasu yankunan da ke karkashin karamar hukumar Zuru sakamakon hare-haren da yan bindiga suka kai
Jihar Kebbi na daya daga cikin jihohin da suka fi fama da hare-haren yan bindiga a Najeriya al'amarin dai ya tilastawa mata da yara kimanin dubu goma kaura cewa gidajensu a yankin Zuru, 
A cewar wani rahotanni wasu yan bindiga dauki da mungan makamai sun afkawa wasu kauyuka a karamar hukumar Zuru a jihar Kebbi, inda suka kashe mutane da dama acikin garuruwan, 
Wasu mazauna kauyukan Tadurga da kyabu da kuma wasu yankunan Zuru sun ce yan bindigar sun mamaye al'ummarsu sun kashe mazaje tare da lalata dukiyoyi, 
Yan bindigar sun sace mutane tare da kashe wasu acikin kauyukan inda suka tare hanya tare da mungan makamai suka ci karensu babu banbaka ba tare da an kai masu dauki ba in ji sanarwar, 
Wani mazaunin garin ya bayyana cewa yan bindigar sun yi garkuwa da mata a Tadurga sun kuma shiga wani kauye mai suna kyabu suka yi garkuwa da mutane kafin su wuce Maga suka yi garkuwa da mutane da dama, wadannan sun faru ne da safiyar ranar Larabar da tagabata, 
Rahotanni ya kara da cewa kauyuka da dama sun zama ba kowa yayin da mazauna kauyukan ke tashi da gudu zuwa Ribah da Zuru,