HAƊIN ALLAH:Labarin Soyayya Da Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta Sha Ɗaya

HAƊIN ALLAH:Labarin Soyayya Da Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta Sha Ɗaya

   Labari da rubutawa
       
   *Hauwa'u Salisu (Haupha)* 

        Page 11


Ina zaune ina saƙawa da kwancewa Deeni ya fito daga ɗaki, shi dama bai wanka sai dai idan ya gaji da kayan jikinsa ya dawo ya cire su ya saka wasu, duk da lokuta da dama zai ta tashin wari irin na mutum ya sha rana amma ko a jikinsa, ga sumar da yake bari cike da hammata na ƙara taimakawa gun fitar wari a jikinsa, amma ruwansa shi, ko a jikinsa. Ni kuma ina bala'in son namiji mai tsabta wayayye, wanda ko da yaushe zamu kasance cikin farin ciki da walwala, muna wasa da tsokanar juna, amma ban da Deeni, kawai shi idan ba dole akwai maganar da zai mun ba, bai min magana sam. Idan ya shigo gidan duk da bai sallama nakan basar na amsa ma shi sallama nayi kamar naji ya yi sallamar. Duk da yadda yake gwasaleni hakan bai hana ni ƙoƙarin dinga jan sa da wasa ba, amma sai ya buga tsaki ya fice bai nuna ya jini sai ta silar tsakinsa zan fahimci ya ji ni sarai lokacina ne bai da shi kawai.

Ina cikin tunanin zaman gidan aurena Deeni ya fito ya sauya kayan jikinsa, har ya wuce ya dawo ya sunkuya ya ɗauki abincin da aka aiko min da shi. Gudun kar ya cinye kuma ina buƙata yasa nace a sanyaye "Don Allah ka rage min ban ci ba, kuma yunwa nake ji." Wani banzan kallo ya bini da shi ya taɓe bakinsa kamar zai aje robar abincin sai kuma ya ɗauka yace, "Mutum sai shegiyar rowar tsiya ta gadon gidansu. Ki ma gode wa Allah da har kike aje abu ina ɗauka, ba don ban da shi ba ne sai don na taimaka maki wani lokacin kuma naga yadda za ki yi kamar dai yanzu da zan ɗauke abincin, ba daga gidan rasuwa aka kawo min sadaka ba har gida? Ko gidan ke kaɗai ce mai iko da shi? Ina ga nan gaba cewa za ki dinga yi gidanma naki ne ko? Ban da munafukar rowa da son banzar tsiya ma irin taki ni da gidana ace ban cin abin da ke cikinsa? Ke kam anyi marowaciyar gaske Dilla." Ya ɗauke abincin ya koma gefe na ya zauna yana ci, sai kawai raina ya ban na je na saka hannu mu ci abincin tare muna ƴar fira ba mamaki daga nan hakan ya ɗore da nafi kowa murna da farin ciki gaskiya, ina matuwar son naga ina abubuwan birgewa da mijina amma ina shi ba ruwansa ko kallonsa nayi nai murmushi sai yace "Rainin ne ya motsa ko?" Idan kuwa yana zaune na je na zauna gab da shi sai ya haɗe rai ya tambaye ni "Lafiya ki zo kika tasani gaba kamar wani marar lafiya kin mun zuru da waɗannan idanun naki?"  Ni kuma sai na kasa magana sai kawai na miƙe na bar gun amma har a zuciyata so nake mu yi rayuwa tamkar yadda musulunci yace, "Rabin jin daɗin rayuwar duniya samun mace ta gari." To ni ya zan na zama ta garin ga Deeni? Ko da yaushe tambayar da nake ma kaina kenan. Yaushe Deeni zai dinga sakin fuska yana min dariya muna wasa da dariya? Yaushe ne zan ga Deeni na mun magana babu ƙunci a kan fuskarsa? Na rasa me yasa burina ya ƙi cika na zaman aurena, tun ina Lagos nake mafarkin gani gidan aurena da wani dogo mun rungume juna duk lokacin daya dawo daga waje, haka ina ganin muna abubuwa masu kyau na soyayya da saka farin ciki, sai dai ban taɓa ganin fuskarsa ba, ko da yaushe jikinsa kawai nake gani kansa na cikin jikina ko dai yana sunsunar wuyana ko kuma ya rumgume ni yadda ba zan ga fuskarsa ba. Babu ranar da ban mafarkin nan har aurena ina yi, kawai tsorata nayi don naji ance aljani na auren mace don haka nake ƙin barin mafarkin ya yi tasiri a zuciyata ko da safe idan na farka. Na yi tunanin idan nayi aure ba zan sake irin mafarkin ba amma sai naga ban daina ba, kullum sai nayi mafarkin ga shi wanda nake gani dogo ne amma ban taɓa ganin fuskarsa ko na gane fari ne ko baƙi ba, kawai ina mafarkin namiji ne ko muna rungume da juna ko yana min kiss ko kuma nayi lamo a jikinsa tamkar wata mage. Hakan yasa nake son tabbatar da mafarkina akan mijina amma ina shi ba haka ne a gabansa ba, gwarama da kafin na kama shi da ƙawata Safiya yana ɗan murmushi ya taɓe baki idan nayi mai shagwaɓa ko ya shigo gida nace "oyoyo Lovely " To yanzu duk wannan ta kau tsakanina da shi muguwar harara da uban tsaki ne, sai kuwa idan yaga abu ya ɗauke duk da yasan ba shi ne ya kawo abin ba.
Kamar wasa Deeni ya zauna ya cinye abincin ya dube ni fuska ba walwala yace, "Tsabar iskanci ruwan shan ma Yau sai na ce aban?" Girgiza kaina nayi na miƙe da ƙyar, na fita don kawo mai ruwan, wanda nasan ya fini gaskiya ya kamata ace yana fara cin abincin na kawo mai ruwan kamar yadda na saba yi mai ko da yaushe. Ina jin shi yana cewa, "Yarinya ba zan ɗauki rainin hankali ba ni da kuɗina, dama kin natsu kafin na natsar da ke a banza. Ina ma amfanin auren yarinya ƙarama? Ni ban san makancewar data sa na kai kaina ba nace ina sonki ba ma, ko da yake wannan shegen farin ne ya ja ni ya kaini ya baro."  Ni dai ban ce ƙala ba ko a zuciyata domin dai nasan ban da gaskiya, taya miji na cin abinci ba ruwa a gabansa? Ba haka naga Mamata nayi ba, ko da yaushe tanadar komi take na mijinta, idan yana cin abincin ma tana gefensa suna labarin duniya, dana jama'ar gari. Lokacin dana kawo mai ruwan har ya cinye abincin tas yana latsa wayarsa, idona ya kaimun kan sunan Safiya dake cikin wayar alamar ita yake son kira. Gabana ya faɗi sosai har kaina ya amsa naji juwa na neman kadani na zubar da ruwan a jikinsa na shiga tara kuma ba uku ba, na samu na daidaita natsuwata na aje mai ruwan cikin muryar da kaɗan ya rage na fashe da kuka nace "Ga ruwan na kawo." Har ya kanga wayar a kunne ya janye yace min, "Munafurci dodo ne, mai shi yakan ci." Ban ce komai ba na wuce na koma inda na tashi na zauna zuciyata na suya da tafasa, ji nake tamkar na haɗiye zuciya na mutu,tsabar yadda zuciyata ke luguden tara-tara.  Kamar daga sama naji yana cewa, "Ya kina gidan ne ko kuwa? Ni fa daɗina dake kenan banzan tsoro wallahi miye naki a ciki aini zatai mawa idan ta isa ko? Sai kuma ya yi murmushi yace to ina zuwa yanzu mu yi bankwana ki ɗan jira ni kaɗan."  Kasa riƙe kaina nayi sai da na ɗago na dube shi har ya miƙe tsaye nace, "Yanzu don Allah baka rabu da Safiya ba, har yanzu kuna tare? Baka gudun mijinta ya kamaku kamar yadda na kamaku?" Ya wani zaburo kamar zai kai min mari yace, "Dama jiranki nake, uban miye naki a ciki to? Kika kama mu satar me mu kai maki? Wallahi ki fita idona na rufe kafin na sauke maki kwandon  mutunci. Ko gidanki ne nace? Nace gidan naki ne na kawo ta ciki da za ki min munafurcin banza? Idan  gidan iyayenki na kaita ba sai ki sa a koro mu ba." Har ya fice waje yana masifa, ni dai kwanciya nai mina-mina ina kuka mai matuƙar ciwo, ji nake tamkar ba ni ba, ji nake ban da kowa a duniyar nafi kowa matsala haka nafi kowa damuwa. 
Kamar wasa haka na wuni cikin gida ba wanda ya leƙo ni har la'asar sannan Binta maƙwabciyata ta shigo tana min gaisuwar mijin Mamata. Na amsa mata har nayi mata godiya, ta dubeni sosai tace, "Jiddah bari na kawo maki kunun kanwa ki samu ki sha yanzu naji ina marmarinsa na dama shi, to nasanki da son shi, dama zuwa nayi naga ko kina nan na kawo maki."  Allah Sarki! Daɗi naji sosai amma don kar ta gano gazawata ko ta fahimci yunwa gareni sai nace cikin ɗan yaƙe, "Lah ai da ma kin bar shi wallahi na gode Binta." Tana kallona kamar bata sanni ba ko ta jima bata ganni ba tace, "Amma Jiddah kin saka abin nan har yanzu a ranki ko? Kin ga yadda kika koma kuwa? Baki ɗaya kin fita hayyacinki da anganki ko baki faɗa ba ansan kina cikin damuwa. Don Allah ki manta da komai kinga ko asibiti ana yawan yi mana faɗa kan damuwa ance har hana haihuwa take yi." Murmushin yaƙe nayi nace a sanyaye "Ban lafiya ne Binta don haka ko gidan gaisuwar ban je ba, ba abin da ke damuna ni." Cikin shakku tace, "Bari na miƙo maki kunun ki daure ki sha, amma ban daina gaya maki ki cire damuwar namiji a ranki don anyi babu ke wallahi indai ɗa namiji ne duk yadda kike kau da kai kike haƙuri da shi idan ba ki dace ba, sai ranki ya dinga ɓaci a banza." Ta fice na bita da kallo kawai raina na gasgata maganarta, amma kuma me yasa Deeni zai mun hakan? Bayan yasan ba sonsa nake ba lokacin da akai aurenmu ban san shi ba, nayi biyayya ne kawai na aure shi saboda ban da gatan da zan ja da aurensa. Haka kuma ban san kowa ba a zuciyata amma dai nasan wanda nake so nayi rayuwar aure da shi a cikin raina shi ne irin wanda nake gani a cikin idanuna da mafarkina idan nayi barci, shi ne wanda nake hango muna rayuwar aminci mai cike da walwala da mutunta juna. Amma ban san me yasa zuciya ke son irin rayuwar ba duk da bata dace da  irin shi ba a zamantakewar aure. Ina nan Binta ta kawo kunun yana ta ƙamshi, taban ta fice tana ƙara ban shawarar na yakice damuwa na samu zaman lafiya inba haka ba ni zan jawa kaina ciwo babu mai jinyata da ɗawainiya da Ni sai dolena, nace a raina tana nufin Mamana kenan.

Tabbas kunun ya yi mun daɗi sosai na shanye duka duk da yana da yawa, na tashi haka nan ta kama sharar gidan duk da mugun ciwon kan dake addabar rayuwata, ina son na manta da komai ne don haka nake tsirar aikin da zai sa ma manta yadda nake cikin damuwa, sai dai sharar nake amma hawaye sai zuba suke a idanuna, a bayyane nake furta, "Yaushe ne zan ji daɗin rayuwata? Yaushe ne zan cika burina? Tabbas ina son na koma karatu ko dan na samu sauƙin baƙin cikin cikin gidana, amma Deeni zai barni na koma karatuna? Ina son naga Mamana a farin ciki yaushe ne zan saka ta cikinsa? Ina son rayuwar gidana ta daidaita yaushe ne zan daidaita ta?"
Ina cikin sharar naji sallamar wadda har in mutu ba zan manta sharri da alkhairinta gare Ni ba, wadda ta zaɓi zamana a cikin baƙin ciki madadin farin cikin da Ni na zaɓar mata zama.
Shin kun san Wacece wannan?


Ku biyo Haupha dan jin wacece wannan matar tai ma Jiddah sallama a wannan lokacin da take tsaka da neman makullin zaman lafiyar rayuwarta.

Taku a kullum Haupha!!!