DUHU DA HASKE: Fita Ta 30

DUHU DA HASKE: Fita Ta 30

DUHU DA HASKE


     Na
*Jiddah S mapi*


*Chapter 30*


                 ~A compound yayi parking lokacin Ameesha ta gama yin parking itama fitowa tayi tana rufe marfin motan, abdool ya zuba mata ido tayi kyau cikin material na dogon riga pink, hanunta ɗaya rike da uniform nata ɗayan kuma ta rike jaka da waya, tafiya take cikin gajiya ganin motar yazeed ya tsaya taje tana jira ya fito su shiga tare, tinted glass ne shiyasa ba zakaga na ciki ba saide na ciki ya ganka, ganin bai buɗe bata fara knocking yazeed yana kallonta yayi murmushi ya buɗe marfin yace "meesha"
cikin shagwaɓa tace "yaya na gaji"
ya rufe marfin motan taga yana zagayawa yace "sorry"
buɗe motan yayi abdool ya fito, da sauri ta ɗauke kai, zata wuce yazeed yace "meesha"
tsayawa tayi, yazo ya rike hanunta yace "bakiga abdool bane?"
tace "na ganshi"
"ki gaisheshi"
tace "ina wuni"
zai kara magana ta wuce, shiru sukayi su duka harda abdool wanda jikinshi yake a sanyaye, shiga ciki tayi ta wurgar da jakan da uniform ɗin a tsakar falo sannan ta wuce wajen momy wacce tayi tagumi tana tunani, kwanciya tayi akan sofa ta kwantar da kanta a cinyar momy tace "wash na gaji"
momy tayi innocent murmushi tace "sannu ameesha ta"
shigowa sukayi su biyu abdool a takaice ya gaida momy ya ɗauke kai, a duk lokacin da yaga fuskanta manal yake gani, hakan yasa idan tana falo ma ko fitowa baison yi, zai wuce ammi tace "man"
tsayawa yayi, tace "zo nan"
zuwa yayi ya durkusa kusa da ita, gefenta ta nuna mishi tace "zauna kamar bakada lafiya meke damunka?"
yace "ba komai"
kafanta ta nuna mishi tace "kwanta"
a hankali ya kwanta akan kujeran ya kwantar da kanshi a kafarta yayi shiru yana facing ameesha dake kwance a jikin momy, juya baya tayi ganin yana kallonta, yazeed yana tsaye a jikin kofa ya harɗe hannu a kirji yana kallonsu, Abba ya shigo da sallama duk suka amsa, yace "man bakada lafiya ne kuma?"
yace "lafiya ƙalau Abba"
yace "Masha Allah yazeed ya faɗa maka sako?"
yace "eh abba na gode sosai"
Abba yace "babu komai saimu shirya daga ranan da aka yanke hukunci a kotu shikenan zamu tattara mu koma abuja babu kuma abinda zamu kara yi anan garin, gida me part biyu ne a Abuja ɗaya nawa, ɗaya kuma na babanku, ya dawo daga yola jiya ya bani makudan kudaɗe zamuyi amfani dashi wajen kara bunƙasa kasuwanci, ina fatan kowa zai maida hankali jiki, sannan Imran da fahad zasu koma school, Imran zai shiga university shi kuma fahad zai karasa secondary, yanzu dai kawai rana muke jira a yanke hukunci"
duk suka amsa da "to"

Ammi ce tayi musu girkin dare kowa ya hallara harda baba, kowa yayi shiru yana cin abinci banda man wanda yake aikin kallon ameesha amma sam taki yadda su haɗa ido, tayi kyau cikin black hijab tana kallon yazeed tace "ya yazeed yaushe zaka maidani wajen shopping ɗin can?"
yace "duk ran da kika shirya"
tace "tom ko yanzu?"
yace "no saide gobe"
hanan tace "harda ni yaya?"
girgiza kai yayi, ta turo baki bata kara magana ba, ammi tace "karki damu zan kaiki"
cikin jin daɗi tace "thank you ammi"
ameesha ta kalli momy dake jujjuya spoon a abinci da alama akwai abinda yake damunta, ta riko hanunta, a hankali ta kalleta murmushi tayi mata alaman taci abincin, ci ta ta fara, ameesha ta tashi zata tafi Ammi tabi man da ido yadda yake kallon ameesha kamar zai haɗeta, ammi tace "ameesha"
a hankali tace "na'am"

"dawo ki zauna"
a hankali ta dawo ta zauna kamar bata da lafiya yadda ta zama, ammi ta kalleta sannan ta kalli man tace "wannan waye?"
a hankali tace "man"
tace "ba sunanshi na tambaya ba, ina nufin shi waye ne a wajenki?"
shiru tayi, ammi tace "shi waye? ko dai ba zaki bani amsa ba?"
a hankali ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsanta, ammi tace "shikenan tunda ba zaki bani amsa ba, watakila dan ba nice na haifeki ba..."
da sauri tace "a,a ammi wallahi ba haka bane, dan Allah ammi karki kara faɗan haka, zan baki amsa"
kallon man tayi tace "shine Abokina tun na yaranta"
ammi tace "to ameesha meyasa kike fushi dashi? da wanne zaiji? ko sau ɗaya bai taɓa jin daɗin rayuwa ba tunda ya auri manal cikin bakin ciki yake, duk da kinsan dalilin da yasa yayi hakan meyasa kike fushi dashi?"

A hankali tace "ammi yadda nake da man har akwai abinda zai ɓoyemin? tun farko meyasa bai gayamin dalilin da yasa zaiyi hakan ba? daya faɗamin ai ba zan hanashi aurenta ba, saide ma na bashi goyon baya amma shine zai ɓoyemin harma ya rinƙa wulaƙantani, shiyasa nake fushi dashi ammi"
durkusawa kasa yayi a gabanta ya haɗa hannu biyu yace "dan girman Allah ki yafemin"
ware hanunshi tayi tace "ba komai ya wuce"
ganin yana kuka tace "ka daina kuka haka ya isa"
rungumeshi tayi, Imran ne ya fara murmushi ranshi yaji wani irin sanyi ganin abotan da aka gina da jimawa ya dawo yau, yazeed dake zaune yayi gyaran murya ganin yadda suke kankame juna da alama sunyi kewan junansu sosai, a hankali ta zameshi daga jikinta, yazeed ya mika mata hanu yace "let's go yau zan kaiki shopping ɗin"
tashi tayi tana murna tace "yeee thank you"
tare suka fita man ya bisu da kallo, Imran da Fahad basuji daɗin tafiyan ameesha a yanzu ba, momy ta tashi tace "Alhmdllh"
hanan ma tace "masha Allah na koshi"
tafiya tayi, ammi ta kalli man tace "karka damu kaji?"
yace "to ammi"

bacci manal take jikinta duk ciwo ta gaji sosai bata samun hutu, ruwan sanyi taji saukanshi a jikinta a firgice ta buɗe ido tana kallon matar dake tsaye rike da bokiti tace "bacci aka kawoki kiyi? tashi kije kiyi girki"
a hankali ta tashi tana goge jikinta sanyi sosai take ji, jikinta ya lalace ta zama kamar wata me cutan kanjamau ta rame tayi baƙa gashinta ya cinye duka, tayi datti sosai kamar ba manal ba, yunwa bata iya cin abincin da suke bata yadda suka aje haka suke zuwa su ɗauka"
fita sukayi tare taje wajen girki, itace yanata hayaki akace ta fara girki a wani katon tukunya, gyara riganta tayi ta ɗaure bayan sannan ta fara girkin itacen yanata sata hawaye sai sharewa take tana cigaba da girki, da kyar ta gama ta zuba a tulin kwanunkan waje sannan ta koma ɗaki ta kwanta cikin warin hayaƙin.

*Ranan Talata*

yau ne za'a yanke hukunci a kotu, kowa ya hallara ameesha tayi matukar kyau cikin farin abaya da farin mayafi karami sai bakin glass data rufe idonta dashi, man da yazeed suna zaune kusa da ita sun sata a tsakiya, ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya tana kallon cikin kotun, momy da ammi da baba da kuma Abba suna layin bayansu ameesha, Imran da fahad da hanan sunsa hanan da tayi kyau cikin abaya red tasa bakin glass itama, duk sunyi kyau sosai kamar ka sacesu ka gudu, man sanye yake da shadda me matukar kyau fari sal sunyi anko da ameesha, sai kamshi yake sosai yayi kyau sabida raman da yayi ya ɓata, yazeed kuma yayi kyau shima cikin shadda coffee yasa farin hula ya harɗe hanu a kirji lips nashi na kasa cikin bakinshi yana tsotsa a hankali, alkali yana zaune ana jira a shigo da manal, mintuna kaɗan sai gata sanye da baƙin kaya ansa ankwa a hanunta ga kuma police maza da mata a bayanta tana gaba, a gaban kotu akasa ta tsaya, Alkali ya fara karanto laifukanta duk wanda tayi saida aka faɗa tareda shaida, murmushi tayi tace "na amsa laifina"
yace "zakiyi alwala kizo kiyi salla raka'a biyu"
fita da ita akayi taje tayi alwala tazo, cire mata ankwa akayi sannan aka shimfiɗa mata sallaya tayi salla raka'a biyu, daga nan ta koma ta tsaya a gaban kotu, alkali yace "akwai sakon da kikeson isarwa kafin kibar duniya?"
tace "eh"
alkali yace "menene?"
kallon Abdool tayi wanda ya janyo hanun Ameesha yana matsawa, tace "sakona an halicci abdool ne sabida manal kaɗai"
daga nan tayi shiru bata kara cewa komai ba, alkali yace "to yanzu za'a gudanar da hukunci"
rufe mata fuska akayi da baƙin kyalle ta yadda ba zataga komai ba, ɗakin dake da duhu aka shiga da ita, gabanta yana faɗuwa sosai tana jin tsinkewan zuciya, a babban tv aka buɗewa waɗanda suke wajen kowa yana kallo har aka shiga da ita, wajene me matukar ban tsoro ga abin hanging a wajen, momy tana gani jikinta ya fara rawa, ameesha ta sunkuyar da kai lokacin da aka aiwatar da hanging wa manal, saida ta daina motsi duk suka tabbatar bata raye, shiru akayi kowa jikinshi a mace, fito da gawanta akayi akace momy tazo tayi mata addu'a, momy taki zuwa, sutura akayi mata sannan aka taru gaba ɗaya maza da mata domin tabbatar da an binneta akaje aka sata a makabarta, duk saida sukayi hawaye banda man da idanunshi ko canja kala basu ba, jikinshi a mace suka koma gida, Abba ma jikinshi a mace ganin yaran nashi duka babu wanda yake cikin walwala, ga ammi da take kukan sabo da manal, momy kam har zazzaɓi take ji, a hankali yace "jirginmu ya kusa tashi yau zamu tafi Abuja"
duk suka amsa da "to"
hanan ce ta shirya musu kayansu sabida itace me ɗan karfi, Imran kuma cikin farin ciki shida fahad suka shirya kayansu dana ya man, yazeed da kanshi ya shirya nashi, ammi ta shirya nata dana baba, sai momy da Abba ya shirya musu sabida yaga bata ma magana yau yanayinta na daban ne, yasan dole hakan zai faru ƴa ba wasa ba.

jirgin yamma sukabi sun isa Abuja babu jimawa, gidane guda biyu amma a haɗe nasu abba dasu momy dasu yazeed da hanan da ameesha daban sai na baba dasu man dasu Imran suma daban, tsararren gida ne me matukar kyau tsayawa faɗan irin kyaun gidan ɓata lokaci ne, saide muce an kashe dukiya me yawa a cikin wannan tsararren ƙerarren gidan, man a ɗakinshi su Imran suke shirya mishi kaya ya zauna yayi shiru akan makeken gadon da yake mallakinshi ne, Imran ganin yana cikin damuwa yace "ya man me kuma yake damunka yanzu? ba komai ya wuce ba?"
ya kalli Imran yana tsoron faɗa mishi abinda yake tunani, kawai sai yace "ba komai"
ameesha tana zaune a bakin gado itama tasa riga da wandon shan iska ta harɗe hanu a kirji, hanan dake shirya musu kayansu cikin wardrobe tace "wow meesha kalli yadda gidanmu yayi wani irin kyau? kalli ɗakinmu kamar a kasar london wallahi ɗakinnan yamin kyau"
faɗawa tayi kan gadon tace "wayyo Allah yau ji nake kamar an sauya min rayuwa"
ganin ameesha tayi shiru tace "wai mene? ba komai ya wuce ba?"
tana tsoron faɗan abinda yake ranta kawai tace "eh haka ne kawai ina tausayawa momy ne"
tace "ai momy ta gama danuwanta yanzu haka tana can kitchen tana shirya mana abinci me daɗi"
murmushi tayi tace "Allah?"
gyaɗa kai tayi, da sauri ameesha ta tashi ta fita zuwa kitchen ɗin, da Abba suka haɗu ta durkusa kasa tace "sannu Abba"
yace "yawwa ameesha ya kikaga gidan? ya muku kyau ba?"
tace "gaskiya Abba yayi kyau sosai"
yace "masha Allah ku kwantar da hankali sosai yanzu babu wani abinda zai kara faruwa kunji?"
tace "to Abba mun gode"
kitchen ta shiga taga momy tana yanka albasa da sauri tazo tace "momy kawo na yanka miki"
momy tace "da kin bari ameesha yanzu zan gama kar kiyi warin albasa kuma kinga akwai gajiya kije ki huta"
kallon innocent face na momy tayi tace "momy ina sanki sosai"
ji tayi har cikin ranta tana son ameesha tace "nima ina sanki meesha"
cikin shagwaɓa tace "to idan kina sona kawo nayi girkin"
mika mata wuƙan tayi tace "to gashi"
karɓa tayi momy tana tsaye tana kallonta, yazeed da baisan momy na kitchen ɗin ba yaga shigowanta cikin sanɗa ya shigo yasa hanu ya rufe idonta wai shi ala dole zai bata tsoro, dariya tayi tace "sakeni nikam nayi aiki kamshin turarenka ai babu me faɗamin shi"
sakinta yayi yace "shine zaki ganeni?"
tace "eh"
tayi maganan tana kwaikwayon muryanshi, yaja karan hancinta yace "kinada kyau sosai fa"
momy ganin yana maganan kamar raɗa taja kafa ba tareda ya ganta ba ta fice daga kitchen ɗin, ameesha tace "kaima haka"
girkin ya fara taya ta, man ya shigo yana dube dube ko zaiga ameesha bai ganta ba sai yaga hanan tana fitowa tana gyara farin glass nata yace "sit"
murmushi tayi mishi tace "ya man ya akayi?"
yace "ina meesha?"
kitchen ta nuna mishi da sauri ya nufi hanyan kitchen ɗin yana murmushi ya shiga, daidai lokacin attaruhu ya shiga idon ameesha ihu ta fara yazeed ya riketa yana duba mata idon, tsaban zafi batasan time ɗin data rirrikeshi ba, man yana shiga ya gansu a haka da sauri ya juya ba tareda yayi magana ba zai fita yazeed yace "ji mana"
tsayawa yayi, yazeed ya saketa yaje yaja hanun man ya shigo dashi ciki, yace "duba mata idonta ana kirana"
fita yayi ya barsu, yana shiga ɗaki yace "banyi adalci ba idan na shiga tsakaninsu, nasan Ameesha zata zaɓeni sabida kawaici amma ya zama dole na taimaki man, dukkansu suna taimakon mutane shi man ya taimaki manal ne har ya aureta, ita kuma ameesha kullum cikin taimako take, hakika marayu ne tun suna kanana suka taso da tausayi a ransu.

Jiddah CE....