Tambuwal Ya Aiyana Litinin Ta Zama Ranar Hutun  Shekarar Musulunci

Tambuwal Ya Aiyana Litinin Ta Zama Ranar Hutun  Shekarar Musulunci

Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya aiyana ranar Litinin ta zama ranar hutu domin shigowar sabuwar shekarar musulunci.
Gwamna Tambuwal ya ce bayan tattaunawa da Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar kan shigowar sabuwar shekarar musulunci a wannan Jumu'ar "na aiyana Litinin 1 ga watan Agusta 2022 ta zama ranar hutu ga ma'aikatan gwamnati a fadin jihar Sakkwato baki daya".
Tambuwal ya roki mutane su yi amfani da lokacin ga aikata kyawawan dabi'un yin sadaka da yin addu'o'in zaman lafiya da samun gwamnati mai kyau.
"mu ci gaba da kulawar  karantarwar addini a wannan watan ganin yana cikin watanni hudu dake da daraja, da aka haramta zubar da jini da wasu manyan laifuka.
"Allah ya sa da mu da rahamarsa da gafara, ina fatar samun dacewa a shekarar musulunci," a cewar Tambuwal.