MEE'AD LABARIN SOYAYYA MAI RIKITARWA:FITA TA ASHIRIN DA DAYA

MEE'AD LABARIN SOYAYYA MAI RIKITARWA:FITA TA ASHIRIN DA DAYA
          MEE'AD
                   
             
                
 
     
 
           ***CONTINUE***
 
 
 
*BY*
 
*_HAUWA IBRAHIM MISAU_*
 
Follow me on wattpad
@hauwancyy44
 
  
 
 
  
 
 
Ina kuke masu son DATA ? ku taho da hazanri ku saya dan kuma nazo muku da Data a sassaukan rahusa idan kuna bukata
 
    *MTN*
 
*50MB*   *#50*
*150MB*  *#100*
*250MB *  *#110*
*500MB*  *#150* 
*1GB*      *#250* 
*1.5GB*    *#400* 
*2GB*        *#500* 
*2.5GB*     *#650* 
*3GB*         *#750* 
*3.5GB*      *#900* 
*4GB*       *#1000* 
*5GB*         #1250* 
*6GB*         #1500* 
*10GB.*     #2500*
*15GB.*     #3800* 
*20GB.*     #5000*
 
Mai bukata ya tura ta wannan account number
 
3142669195 Hauwa Ibrahim First Bank .
 
Idan ka tura saika tuntubeni ta wannan number
09039285813.
 
Ga masu bukata akwai Glo da Airtel da kuma 9mobile.
 
Masu bukata suyimin maza kuzo ga dama tazo muku har gida.
 
 
45 ~ 46
 
Shiga falon Mommy tayi ba tare da tayi sallama ba, sai wani shan kamshi take cike da izza ta nuna Mommy dake zaune bisa kujera hannunta rike da zani tana ninkewa," ta ce ke! mara mutunci yau nazo gareki domin na gargad'eki keda waccar kod'ad'd'iyar aljanar y'ar taki daku fitar min daga hanci konasha iska, ku fita 'a hanyar y'ata d'aya tilo da kuma Mijin da zata 'aura idan kuma kun'ki to dukkan abinda ya biyo baya ku kuka saya da kud'inku.
 
Tana gama fad'in haka ta wuce fuuu! sai kumbure ~ kumbure take.
 
Binta da kallo Mommy tayi kafin daga bisani ta girgiza kai ta ce Allah ya shiryeki Hajiya Suwaiba ke dai kullum bakiso kiga 'an zauna lafiya, hmm Allah shi kyauta.
 
Da sallama ta shiga falon Hajiya ta tarar zaune ta rabka uban tagumi," karasawakusa da ita tayi ta dafa kafadarta Hajiya kiyi hakuri ki manta da dukkan abinda ya faru baniso naga kina yawan tinanin nan Allah," 
 
Murmushi Hajiya tayi hmm Mee'ad kenan! aike har yanzu yariyace na kuma san bazaki ta'ba fahimtar dalilin yin tinanina ba 'amma komai ya wuce tashi kije ki kwanta nasan jikinki a gajiye yake.
 
"Murmushi tayi kafin ta nufi daki dan samun nitsuwa.
 
Majeed ne kwance bisa gado fuskarsa na kallon sama da 'alamun tinani yake, gyara kwanciya yayi sannan ya dauko wayarsa yai dealing number Amal bugu daya ta dauka " barka da war haka Yayana, bai amsa mata ba sai cewa yayi ke! ki sameni a part dina inaso muyi magana, cike da hanzari ta amsa da ina zuwa yanzu.
 
" Tana kashe wayar juyowa tayi ta kalli Amrah ke Yayane wai yace naje part dinsa zamuyi magana, kai haba dai! anzo dai ~ dai wajenda nakeson azo kinsan shawarar da zan baki ? jijjiga kai tayi da 'alamar bata sani ba, yanzu dai tashi ki shiga wanka kafin Umma ta dawo muji yadda ta kasance tsakanin su" murmushi tayi ina 'kaunar ki 'kawata kinga bari nayi wanka nazo, bathroom ta nufa fuskarta dauke da murmushi.
 
" Binta da kallo Amrah tayi hmm yariya kenan! zaki san dawa kike tare, sai kinyi nadamar had'a abota dani, kuma bazaki ta'ba 'auren salihin Miji kamar Majeed ni kuma ki barni a titi ba.
 
%%%%%
 
Umma ce ta shigo cikin dakin tana fada harta zauna bata daina ba," Amrah ta kalleta a hasale Umma wai fad'anmi kk yine haka ? 
 
Au bakima san akan wani dalili nake fad'aba kenan ? to naje na sami waccer matar nayi mata gargad'i akan abinda takeyi kuma na ca ta fita ' a sha'anina baki d'aya.
 
"Wow Amma kin burgeni Umma da 'ace haka kike mata da tuni taji tsoron koda had'a hanya dake.
 
Murmushi tayi yauwa y'ata nasan dama kina son mu kuma kici gaba da bama y'ar uwarki shawara dan kin fita hankali, kuma kiyi duk yadda zakiyi ki rabasu da Mee'ad kinji d'iyar arzi'ki ?
 
Ta ce naji Umma kuma insha Allahu bazan ta'ba baki kunya ba.
 
Murmushi Umma tayi kinga bari na shiga kitchen na girka muku abin ta'bawa.
 
Umma indomie kawai nake son ci amma ' a had'a da kwai ko kifi," murmushi Umma tayi karki damu d'iyata yanzu zan girka miki, tashi tayi ta nufi kitchen.
 
"Bayan Amal ta fito daga wanka shiryawa tayi ta feshe jikinta da turare mai kamshi, juyowa tayi ta dubi Amrah dake zaune ta ce ya kikaga nayi kyau kuwa ?
 
Amrah tace kinga yadda kikayi kyau kuma, kinaso ki rud'a Majeed kenan ?.
 
Daria Amal tayi kin mata da shawarar ki tana aiki sosai ne ? ai naji dadin shawaran da kika bani a yau d'in nan kuma zanyi iya bakin kokarina naga na kwatanta 'abinda kika bani shawara 'akai.
 
Shewa Amrah tayi shiyasa kike burgeni 'kawata, yanzu dai kiyi sauri kije ki samu Mijinki tin kafin ya gaji da jira.
 
Ta ce ya gaji da jira kuma ai bai isa ya gaji da jirana ba sbd ni d'ayace a cikin baki d'ayan zuciyarsa.
 
Daria Amrah tayi kice kinfi ko wacce y'a mace a wajen Majeed kenan to nidai ina kara baki shawaran daki taka 'a sannu sbd maza basuda tabbas.
 
A'ah daina fad'in haka y'ar uwa koda maza basuda tabbas nidai nawa na musamman ne kuma yana da tabbas fiye da tsammanin mai tsammani.
 
Shewa Amrah ta kuma yi kinsan mi nake tinani kuwa 'kawata ? ina tina ranar da zatazo Amal ta juyama Majeed mai tabbas baya sbd ta samu guy d'in daya fishi kyau da cikakken nasaba.
 
Murmushi tayi hmm kinga zancen mu bazai kareba, sai anjima ko kuma nace sai munyi waya, nasan ba lallai ki jirana dawo ba zaki iya wucewa tinda da akwai abin hawa ' hannunki.
 
Laaah! ba matsala jeki wajen Yayanki kawai, nima indomie nake jira, kuma idan naci zan wuce gidane kawai.
 
Ok no problem, bari na wuce part din nasa bye.
 
Daga mata hannu Amrah tayi sannan ta d'auko wayarta ta fara lallatsawa.
 
Kai tsaye part din Majeed ta nufa tana rangwada da karairaya kamar wata sabuwar ta'ba'b'biya.
 
Da sallama ta shiga falon zaune ta tarar dashi bisa kafet hannunsa ri'ke da text book yana karantawa da 'alamun bincike yake. 
 
Sai da ya dauki lokaci mai tsayi kafin ya 'amsa sallaman da tayi, ya ce bismillah ga wajen zama" jiki a sanyaye ta zauna kusa dashi.
 
Tayi 'kasa da murya cike da kirsa Mijina dafatan ka wuni lafiya, dazu nasan nayi maka laifi kuma ban kyauta ba dan Allah kayi ha'kuri banyi haka dan ranka ya 'baci ko maka mancin haka ba. Allah sharrin shaidan ne Yaya na tuba bazan 'kara 'aikata irin wannan haka ba.
 
Yaja dogon ajiyar zuciya ya ajiye littafin dake hannunsa sannan ya ce tabbas raina ya 'baci sosai but now komai ya wuce sai dai ki kiyaye gaba, dama na kiraki sbd nayi miki fad'a 'akan abinda kika 'aikata. Kuma ya dole kije ki bayarma Hajiya hakuri idan Allah ya kaimu gobe.
 
Laaah! Yaya tarema zamuje dan na bata hakurin idan har hakan zai faranta maka rai.
 
Murmushi yayi ya ce ya wuce dai yanzu kam Allah ya kaimu goben.
 
Ameeen ta ce tana murmushin mugunta shawarar da Amrah ta batane ya fara dawo mata sabo, murmushi ta kumayi kafin tace"
 
"Yaya kasan wani abu kuwa tin lokacin daka dawo kasar nan bamu ta'ba samun kwanciyar hankali da nitsuwa irin na yau ba. Dan haka ya kamata ka sake jiki musha hiranmu irinta cikakkun masoya. magana take cike da kirsa tana matsawa jikinsa.
 
Ri'ko hannunsa tayi tana cewa Yaya nasan kai cikakken namijine bazaka ta'ba ganin mace kamata zaune kusa dakai ka kyale ba, hannunsa ta daura bisa wuyanta ta shagwa'be murya wash Allah da gaske ina 'kaunarka sosai, shiyasa yau nazo da shirina dan na tabbatar da irin son da kake mini.
 
"Biye mata ya farayi sbd baki daya ta tafi da hankalinsa," 
 
"Tina mi yake shirin faruwa tsakaninsu yayi. cike da zafin nama ya hankad'ata gefe ya kwad'a mata mari nan take zuciyarsa ta fara tafasa sai huci yake kamar mayunwacin zakin daya kwana ya yini bai sami kalace ba...
 
 
 
pls 
 
Follow 
 
Share
 
Vote
 
Comment
 
Fisabilillah.